An buga:
Farawa a: Mayu 1, 2018
Yarjejeniyar Sabis na Microsoft
SirrinkaSirrinka1_YourPrivacy
Taƙaitawa

1. Sirrinka. Sirrinka yana da muhimmanci a gare mu. A karanta Jumlar Sirri ta Microsoft ("Jumlar Sirri "ɗin) tana bayyana nau’o’in bayanai da muke karɓa daga na’urorinka ("Bayanai"), yadda muke amfani da Bayananka, da kuma dalilai na doka da suke sa mu aiwatar da Bayananka. Haka nan kuma Jumlar Sirri ɗin tana bayyana yadda Microsoft take amfani da ƙunshiyarka, wadda ita ce sadarwa tsakaninka da wasu; saƙo da ka miƙa zuwa ga Microsoft ta hanyar Sabis-sabis; da kuma fayiloli, hotuna, daftarori, murya, ayyukan dijital, saƙon bidiyo nan-take da kuma bidiyoyi da ka ɗora, adana, watsa ko raba ta hanyar Sabis-sabis ("Ƙunshiyarka"). Muna aiwatarwa bisa la’akari da yardarka zuwa wa’adin da doka ta ƙyale, ta yarda da waɗannan Sharuɗɗa, ka amince da tattarawar Microsoft, amfani da kuma bayyana Ƙunshiyarka da Bayanai kamar yadda aka bayyana a cikin Jumlar Sirri. A wasu lokuta, za mu samar da keɓaɓɓiyar sanarwa da kuma buƙatar yardarka kamar yadda yake a cikin Jumlar Sirri.

Cikakken rubutu
ƘunshiyarkaƘunshiyarka2_yourContent
Taƙaitawa

2. Ƙunshiyarka. Mafi yawan Sabis-sabis ɗinmu suna ba ka damar adana ko raba Ƙunshiyarka ko karɓar kayayyaki daga wasu. Ba ma iƙirarin mallakar Ƙunshiyarka. Ƙunshiyarka tana kasancewa Ƙunshiyarka kuma kai ke da alhaki da ita.

 • a. Idan ka raba Ƙunshiyarka tare da sauran mutane, ka fahimci cewa ƙila za su iya samun damar, ta hanyar intanet, amfani, adana, ɗauka, sake samarwa, watsawa, nuna (da kuma share HealthVault) Ƙunshiyarka ba tare da biyanka diyya ba. Idan ba ka son wasu su sami dama, kada ka yi amfani da Sabis-sabis ɗin don raba Ƙunshiyarka. Ka nuna kuma yarda cewa tsawon lokacin waɗannan Sharuɗɗa da kake da su (ko za ka same su) duk hakkoki na wajibi ga Ƙunshiyarka da ake lodawa, adanawa, ko rabawa a kan ko ta hanyar Sabis-sabis da kuma cewa tattara, amfani, da kuma riƙe Ƙunshiyarka ba zai zama keta duk wata doka ko hakkokin wasu ba. Microsoft ba da mallaka, sarrafa, tabbatar, biya, ko shawarta ko kuma ɗaukar duk wani nauyi bisa Ƙunshiyarka kuma ba za a riƙe ta da alhaki na Ƙunshiyarka ko sauran kayayyaki da aka loda, adana ko rana ta amfani da Sabis-sabis ɗin.
 • b. Zuwa iya iyakar wajibci na samar maka da Sabis-sabis da kuma wasu, don kare ka da kuma Sabis-sabis ɗin, da kuma inganta samfurori da Sabis-sabis ɗin Microsoft, ka ba wa Micorosft hakki ga hanyar kayanka na intanet da kuma amfani da lasisin hakkin mallakar ilimi ga Ƙunshiyarka, misali, samar da kwafi, riƙewa, watsawa, sake tsarawa, nunawa, da kuma rarrabawa ta hanyar kayayyakin sadarwa da Ƙunshiyarka a kan Sabis-sabis ɗin. Idan ka wallafa Ƙunshiyarka a cikin yankuna na Sabis-sabis in da yake samuwa a kan layi ba tare da taƙaitawa ba, ƙila Ƙunshiyarka ta bayyana a cikin misali ko kayayyaki da suke tallata Sabis ɗin. Wasu Sabis-sabis da talla yake goyon baya. Sarrafawa don yadda Microsoft yake keɓance talla suna samuwa a kan shafin Tsaro da sirri na shafin yanar-gizo na gudanarwar da asusun Microsoft ɗin. Ba ma amfani da abin da ka ce a cikin imel, taɗi, kiran bidiyo na saƙon murya, ko daftaranka, hotuna ko sauran keɓaɓɓun fayiloli don turo maka talla. Ana kula da dokokin talla namu a cikakken bayani a cikin Jumlar Sirri ɗin.
Cikakken rubutu
Dokar Ɗa’ar Ma’aikataDokar Ɗa’ar Ma’aikata3_codeOfConduct
Taƙaitawa

3. Dokar Ɗa’ar Ma’aikata.

 • a. Ta yarda da waɗannan Sharuɗɗa, ka yarda cewa, a yayin amfani da Sabis-sabis ɗin, za ka bi waɗannan sharuɗɗa:
  • i. Kada ka aikata haramtaccen abu.
  • ii. Kada ka saka kanka cikin wani aiki da yake lalata, cutar, ko barazanar cutar da ƙananan yara.
  • iii. Kada ka aika saƙon bogi. Saƙon bogi wani imel ne da ba a so kuma wani tarin imel ne da ba a so, turawa, buƙatun tuntuɓa, SMS (rubutattun saƙonni), ko saƙonnin nan-take.
  • iv. Kada ka nuna a bainar jama’a ko amfani da Sabis-sabis don raba ƙunshiya ko kayayyaki da ba su dace ba (da suka haɗa misali tsiraici, fasiƙanci tsakanin ɗan’adam da dabba, finafinai na fasiƙanci, kalaman ɓatanci, zane na tashin hankali, ko aikata laifi) ko Ƙunshiyarka ko kayayyako da ba su bin dokoki da ƙa’idoji na gida.
  • Kada ka sa kanka cikin wani aiki da yake na ƙarya ko na yaudara (misali, tambayar kuɗi bisa dalili na ƙarya, yin sojan gona, yi wa Sabis-sabis dabara don ƙara ƙidayar kunnawa, ko shafar girma, kimantawa, ko sharhohi) ko ƙazafi.
  • vi. Kada ka yi dabara ga duk wani abu da aka taƙaita iso ko samuwar Sabis-sabis.
  • vii. Kada ka sa kanka cikin aikin da zai cutar da kai, Sabis-sabis ɗin ko wasu (misali, watsarwa ƙwayoyin cuta, sa-ido, aikawa ƙunshiyar ɗan ta'adda, sadarwa da mummunan lafazi, ko kira da fitina ga wasu).
  • viii. Kada ka keta hakkin wasu (misali, raba waƙa mai hakkin mallaka da ba a bayar da izini ba ko sauran kayayyaki masu hakkin mallaka, sake sayarka ko sauran raba taswirorin Bing, ko hotuna).
  • ix. Kada ka sa kanka cikin wani aiki da ya keta sirri ko kariyar hakkin mallaka ta wasu.
  • x. Kada ka taimakawa wasu karya waɗannan dokoki.
 • b. Tilastawa. Idan ka keta waɗannan Sharuɗɗa, ƙila za mu, bisa ganin damarmu, dakatar da samar maka da Sabis-sabis ko ma ƙila mu rufe asusun Microsoft ɗinka. Haka nan ƙila za mu iya toshe isar da saƙo (kamar imel ko saƙon nan-take) zuwa ko daga Sabis-sabis wajen ƙoƙarin tilasta waɗannan Sharuɗɗa, ko ƙila mu cire ko hana wallafa Ƙunshiyarka bisa kowane irin dalili. A yayin bincika tuhumar keta waɗannan Sharuɗɗa, Microsoft tana da hakki na bitar Ƙunshiyarka don warware matsalar, kuma a nan ka ba da izinin wannan bita. Kodayke, ba za mu sa-ido ga ɗaukacin Ayyuka ba kuma ba za mu yi ƙoƙarin aikata hakan ba.
 • c. Nema zuwa Sabis-sabis na Xbox. Danna nan don ƙarin bayani game da yadda wannan Dokokin Ɗa'ar Ma'aikata yana shafa ga Xbox Live, Wasanni don Windows Lice da kuma wasannin Microsoft Studios, manahajoji, sabis-sabis da ƙunshiya da aka samar da ta wajen Microsoft. Keta dokar Ɗa’ar Ma’aikata ta hanyar Sabis-sabis ɗin Xbox (da aka bayyana a sashe na 13(a)(i)) zai iya haifar da dakatarwa ko haramta shiga kowace iri cikin Sabis-sabis ɗin Xbox, da suka haɗa da ƙwace lasisin ƙunshiya, Lokacin Xbox Gold Membership, da kuma ragowar kuɗin asusun Microsoft da suka shafi asusun.
Cikakken rubutu
Amfani da Sabis-sabi da Goyon BayaAmfani da Sabis-sabi da Goyon Baya4_usingTheServicesSupport
Taƙaitawa

4. Amfani da Sabis-sabi da Goyon Baya.

 • a. Asusun Microsoft. Za ka buƙaci wani asusun Microsoft don samun iso ga Sabis-sabis ɗin. Asusun Microsoft ɗinka yana ba ka damar shiga samfurori, shafukan yanar gizo da kuma sabis-sabis da Microsoft da wasu abokan hulɗar Microsoft suke samarwa.
  • i. Ƙirƙirar Asusu. Za ka iya ƙirƙirar asusun Microsoft ta yin rajista a kan layi. Ka amince ba za ka yi amfani da duk wani bayani na ƙarya ko ba daidai ba ko a yayin rajista don asusun Microsoft. A wasu lokuta, wani daban, kamar mai samar maka da sabis na Intanet, ƙila ya sanya maka wani asusun Microsoft. Idan ka karɓi asusun Microosft ɗinka daga wani daban, ƙila wannan ɗin yana da ƙarin hakki a kan asusunka, kamar damar samun iso ko share asusun Microsoft ɗinka. Yi bitar ƙarin sharuɗɗa da wani ya samar maka, don Microsoft ba ta da nauyi da ya shafi waɗannan ƙarin sharuɗɗa. Idan ka ƙirƙiri wani asusun Microsoft a madanin wani abu, kamar kasuwancinka ko ma’aikaci, ka wakilci wannan cewa kana da hakki na bin waɗannan Sharuɗɗa don wannan abu. Ba za ka iya miƙa bayananka na asusun Microsoft ga wani mai amfani ko wani abu ba. Domin kare asusunka, ajiye muhimman bayanan asusu da kuma kalmar sirri a airce. Kai ke da alhaki na duk wasu ayyuka da suka auku a ƙarƙashin asusun Microsoft ɗinka
  • ii. Amfanin Asusu. Dole ne ka yi amfani da asusun Microosft don barin sa aiki. Wannan yana nufin dole ne ka shiga aƙalla sau ɗaya a cikin shekara biyar don ajiye asusun Microosft ɗinka, da kuma Sabis-sabis da suka shafe shi, yin aiki, sai dai kuma idan an samar da shi ne a wani ɓangare na biyan kuɗi na Sabis-sabis ɗin. Idan ba ka shiga a cikin wannan lokacin ba, za mu sa ran asusun Microsoft ɗinka ba ya aiki kuma za mu rufe maka shi. A duba sashe na 4(a)(iv)(2) don sakamako na asusun Microsoft da aka rufe. Dole ne ka shiga akwatin saƙon Outlook.com ɗinka da kuma OneDrive (a ware) aƙalla sau ɗaya a shekara, idan ba haka ba za a rufe maka akwatin saƙonka na Outlook.com inbox da kuma OneDrive ɗinka Dole ne ka shiga cikin Sabis-sabis ɗin Xbox aƙalla sau ɗaya cikin wa’adin shekara biyar don barin alamar-ɗan-wasa da yake da alaƙa da asusun Microsoft ɗinka. Idan mun zargi cewa wani daban yana amfani da asusun Microsoft ɗinka don zama (misali a sanadiyyar satar asusunka), Microsoft za ta iya dakatar da asusunka har sai ka tabbatar da mallakinsa. Dogara da halin sulhu, muna iya buƙara a naƙasa iso ga zuwa wasu ko dukan Ƙunshiyarka. Idan kana samun matsala wajen isowa ga asusun Microsoft ɗinka, don Allah ziyaci wannan shafin yanar-gizo: https://go.microsoft.com/fwlink/?LinkId=238656.
  • iii. Yara da Asusu-asusu. Ta amfani da Sabis-sabis ɗin, ka nuna cewa ka kai shekarun “balaga” ko “na ɗaukar nauyin shari’a” a inda kake zaune ko kae da iyaye ko amincewar mai kulawa don bin waɗannan Sharuɗɗa. Idan ba ka sani ko ka kai shekara na mafi yawa ko “ɗaukar nauyi bisa doka” a inda kake zaune, ko ba ka fahimci wannan sashe ba, tambayi iyayenka ko mai kula da kai bisa doka don taimako da kuma yardarka kafin ƙirƙirar wani asusun Microsoft. Idan ku iyaye ne ko mai kulawa da yaro bisa shari’a ka ƙirƙiri wani asusun Microsoft, kai da yaron kun yarda da waɗanann Sharuɗɗa da kuma ɗaukar nauyi na duk amfani da asusun Microsoft, ko Sabis-sabis, da suka haɗa da sayayya, ko an buɗe asusun yaron yanzu ko an ƙirƙira daga baya.
  • iv. Rufe Asusunka.
   • 1. Za ka iya soke wasu keɓaɓɓun Sabis-sabi ko rufe asusun Microsoft a kowane lokaci bisa kowane dalili. Domin rufe asusun Microsoft ɗinka, ziyarci https://go.microsoft.com/fwlink/p/?linkid=618278. Idan muka umarce ka ka rufe asusun Microsoft ɗinka, za mu ɗan dakatar da shi na tsawon kwanaki 60 idan wataƙila ka canza shawara. Bayan kwana 60, za a rufe asusun Microsoft ɗinka. Duba sashe na 4(a)(iv)(2) da yake ƙasa domin cikakken bayani kan abin da yake faruwa idan an rufe asusun Microsoft ɗinka. Sake shiga cikin kwana 60 zai sake dawo da asusun Microsoft ɗinka.
   • 2. Idan an rufe asusun Microsoft ɗinka (kai da kanka ko mu), wasu abubuwa kaɗan suna faruwa. Da farko, damarka ta amfani da asusun Microsoft ɗin don samun iso ga Sabis-sabis tana tsayawa nan-da-nan. Na biyu, za mu share Bayananka ko Ƙunshiyarka da ta shafi asusun Microsoft ɗinka ko kuma mu raba ta kai da asusunka na Microsoft (sai dai idan doka ta buƙaci mu ajiye ta, dawo da ita, ko miƙa ta gare ka ko wasu da ka amince). Za ka sami wani tsarin wararriyar ajiya koyaushe saboda Microsoft ba zai iya dawo da Ƙunshiyarka ko Bayanai da zarar an rufe asusunka ba. Na uku za ka iya rasa samun iso ga samfurorin da ka buƙata.
 • b. Asusu-asusun Aiki ko Makaranta. Kana iya shiga cikin wasu sabis-sabis na Microsoft da wani adireshin imel na aiki ko makaranta. Idan ka yi, ka yarda cewa mai wurin da ya shafi adireshin imel ɗinka zai iya sarrafa da kuma gudanar da asusunka, da kuma samun dama da aiwatar da Bayananka, da suka haɗa da ƙunshiyarka ta sadarwa da fayiloli, kuma Microsoft za ta iya sanar da mai wurin idan an fallasa asusun ko Bayanan. Ka ƙara yarda da cewa amfaninka da sabis-sabis ɗin yana iya gana wa yarjejeniyar da Microsoft yake da tare da kai ko ƙungiyarka kuma waɗannan Sharuɗɗa ba su shafa ba. Idan kana yi amfani da wani adireshin imel na aiki ko makaranta don iso ga Sabis-sabis da ake kula da a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa, ta yiwo a tambaye ka ka sabunta adireshin imel da aka danganta da asusun Microsoft ɗinka domin a ci gaba da isowa ga irin waɗannan Sabis-sabis.
 • c. Ƙarin Na’ura/Tsare-Tsaren Bayanai. Don yin amfani da Sabis-sabis masu yawa, za ka buƙaci wani haɗin intanet da kuma/ko bayanai/tsarin salula. Haka nan ƙila za ka buƙaci ƙarin na’urori, kamar wani kan waya, kyamara ko makarufo. Kai ke da alhaki na samar da duk haɗe-haɗe, tsare-tsare, da kuma/ko na’urori da ake buƙata don amfani da Sabis-sabis ɗin da kuma biyan duk wasu kuɗi da mai samar da haɗe-haɗenka, tsare-tsare, da kuma na’ura ya buƙata Waɗannan kuɗaɗe ƙari ne ga duk wani kuɗi da ka biya mu na Sabis-sabis kuma ba za mu dawo maka da waɗannan kuɗi ba. Bincika mai samarwarka don ƙayyade idan akwai waɗannan kuɗi da za a iya sanya maka.
 • c. Sanarwar Sabis. Idan akwai wani abu mai muhimmanci mu sanar da kai game da Sabis ɗin da kake amfani da shi, za mu aika maka sanarwar Sabis ɗin. Idan ka ba mu imel ɗinka ko lambar wayarka dangane da asusun Microsoft ɗinka, saannan za mu iya aika maka sanarwar Sabis ta hanyar SMS (saƙon rubutu), da ya haɗa tabbatar da shaidarka kafin a yi rajista lambar wayar hannu ɗinka. Haka nan kuma ƙila mu aika maka da sanarwar Sabis ta sauran hanyoyi (misali ta hanyar saƙonin cikin-samfuri). Ƙila a saka kuɗin bayanai ko aika saƙo a yayin karɓar sanarwar ta hanyar SMS.
 • e. Goyon baya. Tallafin abokan ciniki na wasu Sabis-sabis suna samuwa a support.microsoft.com. Wasu Sabis-sabis suna iya samar da wani keɓaɓɓe ko ƙarin tallafin abokin ciniki, ta la’akari da sharuɗɗa da suke samuwa a www.microsoft.com/support-service-agreement, face sai idan an fayyace. Ta yiwu tallafi ba zai samu ga sigogi na fara duba ko gwaji ba na siffofi ko Sabis-sabis. Ƙila Sabis-sabis ɗin ba za su jitu da manhaja ko sabis-sabis da wasu suka samar ba, kuma kai ke da alhaki na sanin buƙatun jituwar.
 • f. Ƙare Sabis-sabis ɗinka. Idan an soke Sabis-sabis ɗinka (kai da kanka ko mu), da farko damarka ta samun iso ga Sabis-sabis suna tsayawa nan-da-nan kuma lasisinka na manhajar da ya shafi Sabis-sabis ɗin yana ƙarewa. Na biyu, za mu share Bayanai ko Ƙunshiyarka da suka shafi Sabis-sabis ɗinka ko kuma mu raba ta da kai da asusun Microsoft ɗinka (sai dai idan doka ta buƙaci mu ajiye ta, dawo da ita, ko miƙa ta gare ka ko wasu da ka amince). A sakamakon haka, ta yiwu ka daina samun iso ga kowane daga cikin Sabis-sabis ɗin (ko Ƙunshiyarka da ka adana a kan waɗannan Sabis-sabis ɗin). Ka kasance kana da tsarin adanin bayanai akai-akai. Na uku za ka iya rasa samun iso ga samfurorin da ka buƙata. Idan ka soke asusun Microsoft ɗinka kuma ba ka da wani asusu da zai samu iso ga Sabis-sabis, ta yiwu a soke Sabis-sabis ɗinka nan-da-nan.
Cikakken rubutu
Amfani da Manhajoji da Sabis-Sabis na WasuAmfani da Manhajoji da Sabis-Sabis na Wasu5_usingThird-PartyAppsAndServices
Taƙaitawa

5. Amfani da Manhajoji da Sabis-Sabis na Wasu. Sabis-sabis ɗin ƙila su ba ka damar samun iso ko mallakar samfurori, sabis-sabis, shafukan yanar gizo, hanyoyi, kayayyaki, wasanni, dabaru, haɗewa, bots ko manhajoji daga wasu mutane masu zaman kansu (kamfanoni ko mutane waɗanda ba Microsoft ba) ("Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu"). Mafi yawan Sabis-sabis ɗinmu haka nan suna taimaka maka samun Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu, ko su ƙyale ka raba Ƙunshiyarka ko Bayanai, kuma ka fahimci cewa kana amfani da Sabis-sabis ɗinmu don samar maka da Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu. Haka nan ƙila waɗannan Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu za su iya ƙyale ka ka adana Ƙunshiyarka ko Bayanai ba tare da mawallafin ba, mai samarwa, ko mai sarrafa Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu ɗin. Ƙila Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu su gabatar maka da dokar tsare sirri ko su buƙaci ka yarda da ƙarin sharuɗɗa don amfani kafin ka iya sa ko amfani da Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu. Duba sashe na 13(b) don ƙarin sharuɗɗa na manhajoji da ake buƙata ta hanyar Wurin Adanar Office, Wurin Adanar Xbox ko Wurin Adanar Windows. Za ka yi bitar ƙarin sharuɗɗa da dokokin tsare sirri kafin samu, amfani, buƙata, ko haɗa Asusun Microsoft ɗinka da duk wasu Manhajoji da kuma Sabis-sabis na Wasu. Duk wasu ƙarin sharuɗɗa ba sa gyara waɗannan Sharuɗɗa. Microsoft ba ta bayar da lasisin duk wani hakkin mallaka na ilimi gare ka a zaman duk wasu Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu. Ka yarda ka ɗauki duk wani nauyi da ya taso daga amfani da waɗannan Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu da kuma cewa Microsoft ba ta da alhaki na duk wata matsala da ta taso ta amfani da su. Microsoft ba ta da alhaki gare ka ko wasu na bayani ko sabis-sabis da duk Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu suka samar.

Cikakken rubutu
Samuwar SabisSamuwar Sabis6_serviceAvailability
Taƙaitawa

6. Samuwar Sabis.

 • a. Sabis-sabis ɗin, Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu, ko kaya ko samfurori da aka samar ta hanyar Sabis-sabis ɗin ƙila za su iya ƙin samuwa daga lokaci zuwa lokaci, ƙila a samar da su a taƙaice, ko ƙila su bambanta ta la’akari da yankinka ko na’ura. Idan ka sauya wuri da ya shafin asusun Microsoft ɗinka, ƙila ka buƙaci sake samun kaya ko manhajoji da aka samar maka ta hanyar biya da ka yi a yankinka na da. Ka yarda ba za ka sami iso ga ko amfani da kaya ko Sabis-sabis waɗanda suke haramtattu ba ko da ba bayar da lasisi don amfani a ƙasarka wadda daga ciki ka sami iso ko amfani da waɗannan kaya ko Sabis-sabi, ko don soke ko rashin wakiltar wurinka ko shaida don samun iso ko amfani da waɗannan kaya ko Sabis-sabis.
 • b. Muna jajircewa wajen sa Sabis-sabis aiki; amma, duk sabis-sabis na kan layi suna samun katsewa da dakatarwa lokaci-lokaci, kuma Microosft ba shi ne da alhaki na duk wata katsewa ko asara da za a iya fuskanta a sakamakon haka ba. A hali na dakatarwa, ƙila ba za ka iya samun damar dawo da Ƙunshiyarka ko Bayanai da ka adana ba. Muna shawartarka da ka riƙa adani akai-akai na Ƙunshiyarka da kuma Bayanai da ka adana kan Sabis-sabis ko wurin adana ta amfani da Sabis-sabis da Manhajoji na Wasu.
Cikakken rubutu
Sabuntawa ga Sabis-Sabis ko Manhaja, da kuma Sauye-sauye ga Waɗannan SharuɗɗaSabuntawa ga Sabis-Sabis ko Manhaja, da kuma Sauye-sauye ga Waɗannan Sharuɗɗa7_updatesToTheServicesOrSoftwareAndChangesToTheseTerms
Taƙaitawa

7. Sabuntawa ga Sabis-Sabis ko Manhaja, da kuma Sauye-sauye ga Waɗannan Sharuɗɗa.

 • a. Ƙila za mu iya sauya waɗannan Sharuɗɗa a kowane lokaci, kuma za mu sanar da kai idan mun aikata hakan. Amfani da Sabis-sabis ɗin bayan sauye-sauyen sun fara aiki yana nufin ka yarda da sababbin sharuɗɗan. Idan ba ka yarda da sababbin sharuɗɗan ba, dole ne ka dakatar da amfani da Sabis-sabis ɗin, rufe asusun Micorosoft ɗinka, idan kai uba ne ko mai kulawa, ka taimaki ƙaramin yaro ya rufe asusun Micorosft ɗinsa/ɗinta.
 • b. A wasu lokuta za ka buƙaci sabunta manhaja don ci gaba da amfani da Sabis-sabis ɗin. Muna iya bincika sigarka ta sofwaya ɗin ta otomatik da kuma zazzage sabuntawan sofwaya ko canje-canjen tsarin. Haka nan ƙila a buƙaci ka sabunta manhajar don ci gaba da amfani da Sabis-sabis ɗin. Waɗannan sabuntawa sun shafi waɗannan Sharuɗɗa sai dai idan an haɗo da wasu sharuɗɗa a sabuntawa, a wannan lokaci za a sanya sauran sharuɗɗan. Ba a tilastawa Microsoft samar da duk wasu sabuntawa ba kuma ba ta bayar da tabbaci na cewa za mu tallafawa sigar sistem ɗin da ka saya ko aka ba ka lasisin manhajar, ƙunshiya ko sauran samfurori. Waɗannan sabuntawa ƙila ba za su jitu da manhaja ko sabis-sabis da wasu saka samar ba. Ƙila ka iya janye amincewarka ta sabunta manhaja na gaba a kowane lokaci ta cire manhajar.
 • c. Ƙari ga wannan, akwai wasu lokuta da muke buƙatar cire ko sauya siffofi ko aiki na Sabis ɗin ko dakatar da samar da wani Sabis ko samun iso ga Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu a tare. Sai dai har iyakacin da dokar yake shafa take buƙata, ba mu da wajibi na samar da wani sake-zazzage ko mayewa na kowane kaya, Kayayyakin Dijital (da aka bayyana a sashe na 13(k)), ko manhajoji da aka saya a baya. Ƙila za mu iya sakin Ayyukan ko siffofinsu a cikin wata sigar gwaji, wanda ƙila ba zai yi aiki daidai ba ko a cikin wata hanya iri da sigar ƙarshe za ta iya aiki.
 • d. Saboda ka iya amfani da kaya da aka kare da gudanarwar hakkin dijital (DRM), kamar wasu waƙoƙi, wasanni, finafinai da sauransu. manhajar DRM ƙila za ta iya tuntuɓar sabar hakkin mallaka ta kan layi da kuma sauke da saka sabuntawar DRM ta otomatik.
Cikakken rubutu
Lasisin ManhajaLasisin Manhaja8_softwareLicense
Taƙaitawa

8. Lasisin Manhaja. Sai dai idan ya zo da wata wararriyar yarjejeniyar lasisin Microosft (misali, idan kana amfani da wata manhajar Microsoft da ta haɗa da wani ɓangare na Windows, a kokacin Sharuɗɗan Lasisin Manhajar Microsoft na Windows Operating System yake kula da wannan sofwaya), duk wata sofwaya da muka samar gare ka a zaman wani ɓangare na Sabis-sabis ɗin ya shafi waɗanann Sharuɗɗa. Manhajar da aka samu ta hanya Wurin Adana na Office, Wurin Adana na Windows, da kuma Wurin Adana na Xbox sun ta’allaka da sashen 13(b)(i) da yake ƙasa.

 • a. Idan ka bi waɗannan Sharuɗɗa, mun ba ka dama ta saka da kuma amfani da kwafi ɗaya na manhajar a na’ura ɗaya ta la’akari da faɗin-duniya don amfani kawai ga mutum ɗaya a zaman wani ɓangare na amfani da Sabis-sabis da kake yi. Ga wasu na’urori, akan fara saka wanann manhaja don amfanin kanaka, amma ba amfani da Sabis-sabis ɗin ba don kasuwanci. Manhajar ko shafin yanar gizon wani ɓangare ne na Sabis-sabis ƙila ya haɗa da lambar sirrin wasu. Duk wani rubutu na wasu ko lambar sirri, da aka haɗa aka nuna daga manhajar ko shafin yanar gizon, masu wannan lambar sirrin ne suka baka lasisin, amma ba Microsofy ba. Sanarwa, idan akwai, ta lambar sirrin wasu ana sa maka ita ne kawai don bayani.
 • b. Manhajar mai lasisi ce, ba sayarwa ba, kuma Microsoft ita ke da duk hakkoki ga manhajar da ba a bayyana ko bayarwa daga Microsoft ba, ko a kaikaice, da shaida, ko akasin haka. Wannan lasisi bai ba ka wani hakkki don yin, kuma ƙila ba za ka iya:
  • i. dabara ko kaucewa duk wasu hanyoyin kariyar kimiyya a ciki ko da suka shafi manhajar ko Sabis-sabis ɗin;
  • ii. sake haɗawa, buɗewa, shiga, kwafi, ci-da-gumi, ko juya kimiyya ta duk wata manhaja ko wani ɓangare na Sabis-sabis da aka saka a ciki ko ake iso ta hanyar Sabis-sabis ɗin, ban da kawai zuwa wa’adin da dokar hakkin mallakar da ta shafa ta ƙyale aikata hakan;
  • iii. ware kayan manhajar ko Sabis-sabis don amfani a kan wasu na’urori daban;
  • iv. wallafa, kwafi, haya, bayar da haya, sayarwa, fitarwa, shigarwa, rarrabawa, ko bayar da aron manhajar ko Sabis-sabis ɗin, sai dai idan Microsoft ta ba da izinin haka a rubuce;
  • v. mayar da manhaja ko wani lasisin manhaja zuwa wani, ko duk wani hakki na samun iso ko amfani da Sabis-sabis ɗin;
  • vi. yin amfani da Sabis-sabis ta duk wata hanya da ba a bayar da izini ba za ta iya katse amfani da wani yake yi da su ko samun iso ga duk wani sabis, bayani, asusu, ko hanyar sadarwa;
  • vii. ƙyale samun iso zuwa Sabis-sabis ko gyara duk wata na’urar Microosft mai izini (misali Xbox One, Xbox 360, Microsoft Surface, da sauransu) ga manhajojin wasu da ba a ba wa izini ba.
Cikakken rubutu
Sharuɗɗan Biyan KuɗiSharuɗɗan Biyan Kuɗi9_paymentTerms
Taƙaitawa

9. Sharuɗɗan Biyan Kuɗi. Idan ka sayi wani Sabis, ana sanya waɗannan sharuɗɗan biyan kuɗi ga sayayyarka kuma ka yarda da su.

 • a. Cajin kuɗi. Idan akwai wani caji da ya shafi wani ɓangare na Sabis-sabis ɗin, ka amince ka biya wannan caji a cikin kuɗin da aka fayyace. Farashin da aka bayyana a cikin Sabis-sabis bai haɗa da kuɗaɗen haraji da na canjin kuɗi ba, sai dai idan an bayyana akasin haka. Duk farashin samfurorin Skype da aka biya sun haɗa da haraji da aka saka, sai dai idan an bayyana akasin haka. Kai ke da alhaki na biyan waɗannan haraji ko sauran caji. Skype yana lissafta haraji ne ta la’akari da adireshin wurin da kake da ya shafi bayanin biyan kuɗinka. Kai ke da alhaki na tabbatar da cewa wannan adireshi yana aiki kuma daidai ne. Ban da kawai samfurorin Skype, ana lissafta haraji ne ta la’akari da wurin da kake a lokacin da aka yi rajistar asusun Microsoft ɗinka sai dai idan dokar ƙasa ta buƙaci wani dalili daban na lissafin. Ƙila mu dakatar ko soke Ayyukan idan ba mu sami wani cikakken biyan kuɗi daga gare ka a kan loaci ba. Dakatar ko soke Ayyuka a sanadiyyar rashin biyan kuɗi zai iya haifar da rasa samun dama da kuma amfani da asusunka da kuma abun ciki nasa. Haɗi da Intanet ta hanyar kamfani ko sauran keɓaɓɓun hanyar sadarwa wanda yake toshe wajenka ƙila ya haifar da caji ya zama daban daga waɗanda ake nunawa ga ainihin wajenka. Dangane da wurinka, mai yiwuwa wasu cinikayya su buƙata musayar kuɗin ƙasasshe waje ko a sarrafa a cikin wata ƙasa dabam. Mai yiwuwa bankinka ya caje ka ƙarin kuɗi don waɗannan sabis-sabis idan ka yi amfani da wani katin deɓe kuɗi ko amsar kuɗi. Don Allah tuntuɓi bankinka don cikakkun bayanai.
 • b. Asusunka na Biyn Kuɗi. Don biyan caji na wani Sabis, za a buƙace ka da ka samar da wata hanyar biyan kuɗi a lokacin da ka yi rajistar wannan Sabis. Kana iya iso ga da kuma canza bayanin caji kuɗi ɗinka da kuma hanyar biyan kuɗi a kan Shafin yanar gizo na gudanarwar da asusun Microsoft da kuma don Skype ta shiga cikin shafin asusunka a https://skype.com/go/myaccount. Ƙari ga wannan, ka yarda ka ƙyale Microsoft ya yi amfani da duk wani bayanin sabunta asusu da ya shafi hanyar biyan kuɗi da aka zaɓa da bankinka ya samar ko hanyar biyan kuɗi da aka sa. Ka yarda a sabunta asusunka da sauran bayaninka nan da nan, da suka haɗa adireshin imel da cikakkun bayanan hanyar biyan kuɗi ɗinka, domin mu iya kammala cinikayyarka da kuma tuntuɓe ka yadda ake buƙata dangane da cinikayyarka. Sauye-sauye da aka yi ga asusun biyan kuɗinka ba zai shafi sauye-sauyen da muka miƙa zuwa asusun biyan kuɗinka kafin mu iya tsayawa a madadinka a kan sauye-sauye ga asusun biyan kuɗinka ba.
 • c. Byan kuɗi. Ta samarwa da Microsoft wata hanyar biyan kuɗi, ka (i) bayyana cewa ka kana da izini na amfani da hanyar biyan kuɗin da ka samar kuma cewa duk wani bayani na biyan kuɗin da ka samar gaskiya ne kuma daidai ne; (ii) ka ba wa Microsoft izini na cajin Sabis-sabis ɗinka ko ƙunshiya mai samuwa ta amfani da hanyar biyan kuɗinka; kuma (iii) ka ba wa Microsoft izini na cajin duk wata siffar Sabis-sabis ɗin ta biya da ka zaɓa don rajista ko amfani yayin tilasta waɗannan Sharuɗɗa. Ƙila mu iya cajinka (a) tun kafin lokaci; (b) a lokacin sayayya; (c) jim kaɗan bayan sayayya; ko (d) a wasu lokuta na sake aukuwar rajistar Ayyuka. Asimismo, es posible que le cobremos hasta el importe que haya autorizado y le notificaremos con antelación cualquier cambio respecto al importe de los Servicios de suscripción periódicos que se le vaya a cobrar. Ƙila mu caje ba a lokaci guda na sama da ɗaya daga cikin lokutanka da ka fi so na biyan kuɗi na adadin kuɗin ba a riga an aiwatar a baya ba.
 • d. Maimaita Biyan Kuɗi. Idan ka sayi wani Sabis-sabis ta hanyar rajista (misali wata-wata, kowane watanni 3 ko shekara-shekara), ka amince kuma ka yarda cewa bayar ga izini da maimaita biyan kuɗi, da kuma biyan kuɗi za a yi ne ga Microsoft ta hanyar da ka zaɓa a tazarar maimaitawar da ka yarda da ita, har sai ka ƙarar ko Microsoft ta ƙarar da rajistar wannan Sabis. Ta bayar da izini maimaita biyan kuɗi, ka ba wa Microsoft izini na aiwatar da wannan biyan kuɗi ko ta hanyar ɗebewar lantarki ko tiransifar kuɗi, ko a zaman biyan kuɗi ta hanyar lantarki daga asusunka (misali kamar Automated Clearing House ko biyan kuɗi mai kama da haka), ko caje-caje ga asusunka (misali idan katin bashi ne ko biyan kuɗi mai kama da haka) (a tare gaba ɗaya, "Biyan Kuɗi ta Hanyar Lantarki"). Ana lissafta kuɗin rajista ne ko caji tun kafin lokacin biyan rajistar ya shafa ya kewayo. I dan aka dawo da kuɗi da ba a biya ba ko idan aka ƙi karɓar ko ƙin yarda da wani katin bashi ko hada-hada mai kama da haka, Micrsoft ko mai samar masa da sabis yana da hakki na karɓar duk wani abu da aka dawo da shi, ƙin karɓa ko kuɗi da ba su cika ba don aiwatar da wannan biyan kuɗi a zaman Biyan Kuɗi ta Hanyar Lantarki.
 • e. Sabuntawar Otomatik. Muddin an ƙyale sabuntawa na otomatik a ƙarƙashin doka da take shafa, kana iya zaɓa a sabunta Sabis-sabis ta otomatik a ƙarshen wani ƙayyadadden lokacin sabis. Za mu tuna maka ta imel kafin a sabunta kowaɗane Sabis-sabis don wani sabon sharuɗɗa, kuma mu sanar da kai da kowaɗane canje-canjen farashi dangane da sashe na 9(k). Da zarar mun tunar maka cewa an zaɓe ka ka sabunta Sabis-sabis ta otomatik, muna iya sabunta Sabis-sabis ɗinka ta otomatik a ƙarshen lokacin sabis na yanzu kuma mu caje ka farashin na lokacin da sharuɗɗan sabunta, sai dai ka zaɓa ka soke Sabis-sabis ɗin yadda aka bayyana a ƙasa. Haka nan kuma za mu iya tunatar da kai cewa za mu caji hanyar biyan kuɗi da ka samar don sabunta Ayyuka, ko dai yana kan fayil a kan ranar sabuntawa ko mu samar daga baya. Haka nan za mu samar maka da umurnai a kan yadda za ka iya soke Ayyukan. Dole ne ka soke Ayyukan kafin ranar sabuntawa don gujewa cajin sabuntawar.
 • f. Jawabi na kan Layi da Kurakurai. Microsoft za ta samar maka wani bayanin cajin kuɗi na kan layi a Shafin Yanar Gizo na Gudanar da asusun Microsoft, a inda za ka iya duba da kuma ɗab’in bayaninka. Don Skype, za ka iya samun iso ga lissafin kuɗinka na kan layi ta shiga cikin asusunka a www.skype.com. Wannan ne kawai bayanin ajiya da muke samarwa. Idan mun yi wani kuskure wajen cajinka, dole ne ka sanar da mu cikin kwanaki 90 da bayyanar wannan kuskure a kan cajinka. Sannan za mu fara binciken cajin. Idan ba ka sanar da mu ba cikin wannan lokaci, ka sake mu daga duk nauyi da ƙorafe-ƙorafe na rashi da ya samu daga kuskuren kuma ba za a buƙata mu gyara kuskuren ko samar da mayarwa kuɗi ba, sai dai idan doka ta buƙata haka. Idan Microsoft ta gano wani kuskuren cajin kuɗi, za mu gyara wannan kuskure cikin kwanaki 90. Wannan dokar ba ta shafi duk wasu hakkoki na shari’a ba da za a iya sanyawa.
 • g. Dokar Ramuwa. Sai dai kuma idan doka ta samar ko samarwar wani keɓaɓɓen Sabis, duk sayayya ita ce ƙarshe kuma babu ramuwa. Idan ka yi imani Microsoft ta caje ka bisa kuskure, dole ne ka tuntuɓe mu cikin kwanaki 90 da yin wannan caji. Babu mayarwa kuɗi da za a bayar da don kowaɗane caje-caje sama da kwanaki 90, sai dai idan doka ta buƙata haka. Muna da hakki na samar da ramuwa ko bashi bisa ganin damarmu. Idan mun bayar da ramuwa ko bashi, ba ma ƙarƙashin wani wajibci na samar da ramuwa ɗaya ko mai kama ga matsala ta gaba. Wannan dokar ramuwa ba ta shafi duk wasu hakkoki na shari’a ba da za a iya sanyawa. Don ƙarin bayanin mayarwa kuɗi, don Allah ziyarci namu batun taimako. Idan kana da zama a Taiwan, don Allah lura cewa gwargwadon Dokar Kariyar Mai amfani na Taiwan da muhimman ƙa'idojinsa, dukan saye-saye da suka shafa ƙunshiyar dijital da aka samar da ta hanyar tsari maras taɓawa da kuma/ko sabis-sabis na kan layi ƙarshe ne da kuma maras-mayarwa idan aka samar da irin wannan ƙunshiya ko sabis a kan layi. Ba ka da damar neman wani lokacin shan iska ko wata mayarwa kuɗi ba.
 • h. Soke Sabis-sabis ɗin. Za ka iya soke wani Sabis a kowane lokaci, tare ko ba tare da dalili ba. Don a soke wani Sabis da kuma buƙata wata mayarwa kuɗi, idan kana da damar samu wata, ziyarci Shafin yanar=gizo na gudanarwar da asusun Microsoft. Ga Skype, kammala Fam na Janyewa ta amfani da bayanan da aka samar a nan. Za ka koma baya zuwa gasar da take bayyana Ayyukan a zaman (i) ƙila ba za ka karɓi wata ramuwa a lokacin sokewar ba; (ii) ƙila a wajabta maka biyan kuɗin sokewa; (iii) ƙila a wajabta maka biyan duk caje-cajen ga asusunka na biyan kuɗi na Ayyukan kafin ranar sokewar; ko (iv) ƙila ka rasa samun dama ga asusunka idan ka soke Sabis-sabis ɗin; ko, idan kana da zama a Taiwan, (v) kana iya ka karɓi wata mayarwa kuɗin a yawan da ya yi daidai da kuɗin da ka biya don wani Sabis da ba a yi amfani da su ba wanda ake lissafawa a lokacin sokewa ɗin. Za mu aiwatar da Bayananka kamar yadda aka bayyana a sashe na 4. Idan ka soke, samun isonka ga wannan Sabis zai ƙare daga lokacinka na ƙarshe na Sabis ko, idan muna cajin asusunka ta lokaci ne, a ƙarshen lokacin da ka soke.
 • i. Garaɓasoshin Wa’adi na Gwaji. Idan ana damawa da kai cikin wata garaɓasa ta gwaji, dole ne ka soke Sabis ɗin a ƙarshen wa’adin gasar don gujewa sabon cajin kuɗi, in ba haka ba, sai dai idan mun sanar da kai a’a. Idan ba ka soke Sabis ɗin gwajin ba a ƙarashen wa’adin gwajin, ƙila mu caje ka kuɗi don Sabis ɗin.
 • j. Garaɓasoshi na Gasanni. Daga lokaci-zuwa-lokaci, Microsoft ƙila za ta iya samar da Sabis-sabis a kyauta a yayin lokacin gwaji. Microsoft tana da alhaki na cajinka ga waɗannan Sabis-sabis (a farashi na daidai) a yayin da Microsoft ya gano (bisa zaɓin kansa) cewa kana cin zarafin sharuɗɗan wannan gasa.
 • k. Sauye-sauyen Farashi. Ƙila mu sauya farashin Sabis-sabis ɗin a kowane lokaci kuma idan kana da wata sayayya mai sake aukuwa, za mu sanar da kai ta hanyar imel aƙalla kwanaki 15 kafin sauya farashin. Idan ba ka yarda da canza farashin ba, dole ne ka soke da kuma dakatar da amfani da Ayyukan kafin canza farashin ya fara aiki. Idan akwai wani sharaɗi da aka saka wa’adi da kuma farashi na Sabis ɗin da aka samar maka, wannan farashin zai kasance cikin tilastawa zuwa wa’adin da aka saka.
 • l. Biyan Kuɗi Gare ka. Idan kana bin mu kuɗi, ka yarda ka samar mana da duk wani bayani da muke buƙata don yi maka biyan cikin lokaci da kuma daidaito. Kai ke da alhaki na duk wasu harajoji da kuma caje-caje da zai iya faruwa a sakamakon wannan biyan kuɗi gare ka. Haka nan dole ka bi duk wasu sauran sharuɗɗa da muka sa a kan hakkinka na duk wani biyan kuɗi. Idan ka sami wani biyan kuɗi bisa kuskure, ƙila mu iya warware ko mu buƙaci dawo da biyan kuɗin. Ka yarda ka bayar da haɗin gai gare mu wajen ƙoƙarin mu na aikata wannan. Ƙila kuma za mu iya rage biyan kuɗi gare ka ba tare da sanarwa don daidaita duk wani biyan kuɗi fiye da ƙima na baya ba.
 • m. Katinan Kyauta. Karɓa da kuma yin amfani da katinan kyauta (fiye da katinan kyauta na Skype) yana ƙarƙashin kulawar Sharuɗɗa da Ƙa’idoji na Microsoft. Bayani kan katinan kyauta na Skype yana samuwa a kan shafin Taimako na Skype.
 • n. Asusun Bank da Hanyar Biyan Kuɗi. Za ka iya rajistar wani asusun banki da ya cancanta tare da asusun Microsoft ɗinka don amfani da shi a matsayin wata hanyar biyan kuɗi. Asusu-asusun da suka cancanta sun haɗa da asusu-asusu da ake da su a cibiyoyin hada-hadar kuɗi da suke iya karɓar ɗebe kuɗi na kai tsaye (misali wata cibiyar sha’anin kuɗi na Amurka da take goyon bayan automated clearing house ("ACH"), wani cibiyar hada-hadar sha’anin kuɗi da take goyon bayan Single Euro Payments Area ("SEPA") ko "iDEAL" a ƙasar Netherlands). Ana sanya sharuɗɗan da ka yarda da su wajen ƙara asusun bankinka a matsayin wata hanyar biyan kuɗi a cikin asusun Microsoft ɗinka (misali, “dokar” dangane da abin da ya shafi SEPA). Ka amince ka bayar da tabbacin cewa asusun bankinka cikin sunanka yake kuma an ba ka izinin yin rajista da kuma amfani da wannan asusun banki a matsayin wata hanyar biyan kuɗi. Ta yin rajista ko zaɓar asusun bankinka a matsayin hanyar biyan kuɗinka, ka ba wa Microsoft (ko jami’anta) izini na fara ɗiba ɗaya ko fiye da haka daga jumullar sayayyarka ko kuɗin rajista (bisa dacewa da sharuɗɗan sabis na rajista) daga bankinka (kuma, idan ya zama wajibi, fara ɗaukar kuɗi daga asusunka don gyara kurakurai, bayar da ramuwa ko wani dalili mai kama da haka), kuma ka ba wa cibiyar hada-hadar sha’anin kuɗi izini na riƙe asusun bankinka don ɗebe wannan kuɗi ko karɓar wannan kuɗi. Ka fahimci cewa izinin zai kasance cikin amfani da kuma aiki har sai ka cire bayanin bankinka daga asusun Microsoft. Tuntuɓi cibiyar tallafin abokin ciniki kamar yadda aka ambata a sama a sashen 4(e) cikin gaggawa idan kana da yaƙinin an caje ka bisa kuskure. Dokoki da suka shafi ƙasarka haka nan suna taƙaita nauyinka kan duk wata zamba, kuskure ko hulɗa marar izini daga asusun bankinka. Ta yin rajista da kuma zaɓar wani asusun banki a matsayin hanyarka ta biyan kuɗi, ka amince ka karanta, fahimci da kuma yarda da waɗannan Sharuɗɗa.
Cikakken rubutu
Abin da ake Kwangila kansa, Zaɓin Shari’a, da kuma Wuri na Warware SaɓaniAbin da ake Kwangila kansa, Zaɓin Shari’a, da kuma Wuri na Warware Saɓani10_11_contractingEntityChoiceOfLaw
Taƙaitawa

10. Abin da ake Kwangila kansa, Zaɓin Shari’a, da kuma Wuri na Warware Saɓani. Don amfani da Sabis-sabis masu samfurin-Skype na kyauta ko biyan kuɗi, kana kwangila ne da, kuma duk nuni da “Microsoft” a cikin waɗannan Sharuɗɗa suna nufin Skype Communications S.à.r.l, 23 – 29 Rives de Clausen, L-2165 Luxembourg. Amfani da sabis-sabis na samfurin Skype da kake yi a kyauta ko biya, Luxembourg ce ke kula da fashin-baƙi na waɗannan Sharuɗɗa da kuma ƙorafe-ƙorafe kan keta su, koda kuwa wace irin babbar doka ce ta saɓanin. Dokokin gunduma ko ƙasar da kake zaune ita ke kula da duk sauran ƙorafe-ƙorafe (da suka haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci da kuma koke-koke kan lahani). Idan ka amince da waɗannan Sharuɗɗa ta ƙirƙirar asusun Skype ko ta amfani da Skype, kai da mu duk mun amince da kotunan Luxembourg su zama wajen shari’a da kuma warware duk wasu saɓani da suka taso dangane da ko suka shafi waɗannan Sharuɗɗa na Amfani da Sabis-Sabis na Samfurin Skype. Ga duk sauran Sabis-sabis, idan ka amince da waɗannan Sharuɗɗa ta ƙirƙirar asusun Microsoft ko amfani da wani Sabis, abin da kake kwangila akai, da dokar da take kulawa, da kuma wurin warware saɓani yana tafe:

 • a. Canada. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Canada, kana yin kwangila ne tare da Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. Dokoki na gundumar da kake zaune (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) su ke kula da fashin-baƙi na waɗannan Sharuɗɗa, da kuma ƙorafe-ƙorafe kan keta su, da duk sauran koke-koke (da suka haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci da kuma koke-koke kan lahani), koda kuwa wace irin babbar doka ce ta saɓanin. Kai da mu duk mun amince da kotunan Ontario su zama wajen shari’a da kuma warware duk wasu saɓani da suka taso dangane da ko suka shafi waɗannan Sharuɗɗa na Amfani da Sabis-Sabis.
 • b. Amurka ta Arewa ko Kudu wajen Amurka da kuma Canada. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Amurka ta Arewa ko Kudu wajen Amurka da kuma Canada, kana yin kwangila ne tare da Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. Dokar Jihar Washington ce ke kula da fashin-baƙi na waɗannan Sharuɗɗa da kuma ƙorafe-ƙorafe kan keta su, koda kuwa wace irin babbar doka ce ta saɓanin. Dokokin ƙasar da muka tura Sabis-sabis ɗin ke kula da duk ƙorafe-ƙorafe (da suka haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci da kuma koke-koke kan lahani).
 • c. Gabas ta Tsakiya ko Afirka. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Gabas ta Tsakiya ko Afirka, kuma kana amfani da wasu ɓangarori na Sabis-sabis (kamar Bing da MSN), kana yin kwangila ne tare da Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. Idan ka biya don amfani da wani ɓangare na Sabis-sabis ɗin, kana kwangila ne tare da Microsoft Ireland Operations Limited, One Microsoft Place, South County Business Park, Leopardstown, Dublin 18, Ireland. Ga Sabis-sabis na kyauta da kuma na biya, dokokin Ireland ke kula da fashin-baƙi na waɗannan Sharuɗɗa da kuma ƙorafe-ƙorafe kan keta su, koda kuwa wace irin babbar doka ce ta saɓanin. Dokokin ƙasar da muka tura Sabis-sabis ɗin ke kula da duk ƙorafe-ƙorafe (da suka haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci da kuma koke-koke kan lahani). Kai da mu duk mun amince da kotunan Ireland su zama wajen shari’a da kuma warware duk wasu saɓani da suka taso dangane da ko suka shafi waɗannan Sharuɗɗa na Amfani da Sabis-Sabis.
 • d. Asiya ko South Pacific, sai dai idan an cire ƙasarka musamman a ƙasa. Idan kana zaune a cikin (ko, idan wani kasuwanci, cibiyar kasuwancin tana cikin) Asiya (ban da Sin, Japan, da Tarayyar Koriya, ko Taiwan) ko Kudancin Pacific, kana amfani ni ne da ɓangarorin kyauta na Sabis-sabis ɗin (kamar Bing da MSN), kana kwangila ne da Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. Idan ka biya don amfani da wani ɓangare na Sabis-sabis ɗin, ko kana amfani da sabis ɗin Outlook.com na kyauta a Singapore ko Hong Kong, kana kwangila ne da Microsoft Regional Sales Corp., wani kamfani da aka samar a ƙarƙashin dokokin Jihar Nevada, a Amurka, tare da rassa a Singapore da kuma Hong Kong, wanda yake da babbar cibiyar kasuwancinsa a 438B Alexandra Road, #04-09/12, Block B, Alexandra Technopark, Singapore, 119968; haka kuma, idan kana zaune ne a cikin (ko, idan wani kasuwanci, cibiyar kasuwancin tana cikin) Australiya, kana kwangila ne da Microsoft Pty Ltd, 1 Epping Road, North Ryde, NSW 2113, Australia idan kuma kana zaune a cikin (ko, idan wani kasuwanci, cibiyar kasuwancin tana cikin) New Zealand, kana kwangila ne da Microsoft New Zealand Limited, Level 5, 22 Viaduct Harbour Avenue, PO Box 8070 Symonds Street, Auckland, 1150 New Zealand. Don Sabis-sabis na kyauta da na biyan kuɗi, dokar Jihar Washington ke kula da fassara waɗannan Sharuɗɗa da kuma ƙarafe-ƙorafe na keta dokarsu, ba bisa la’akari da saɓani na manyan dokokin ba. Dokokin ƙasar da muka tura Sabis-sabis ɗin ke kula da duk ƙorafe-ƙorafe (da suka haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci da kuma koke-koke kan lahani). Duk wani saɓani da ya taso ko da ya shafi waɗannan Sharuɗɗan Sabis-sabis baya ga Skype, da ya haɗa da duk wata tambaya da ta shafi samuwarsu, inganci, ko ƙarewa, za a tura shi ne zuwa da kuma warwarewa daga ƙarshe a Singapore ta hanyar sauraren ƙara tare da Dokokin Sauraron Ƙara na Singapore International Arbitration Center (SIAC), wanda aka haɗe wasu dokokinta ta nuni da wannan yankin jumla. Kotun Sauraron Ƙarar za ta ƙunshi alƙali ɗaya da Shugaban SIAC zai naɗa. Harshen saurarn ƙarar zai kasance Ingilishi. Hukuncin da alƙalin ya yanke shi zai zama na ƙarshe, yankewa, da kuma ba za a daɗa tayar da ita ba, kuma ƙila a yi amfani da ita a matsayin samfuri na yanke hukunci a kowace ƙasa ko yanki.
 • e. Japan. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Japan kuma kana amfani da wasu ɓangarori na Sabis-sabis (kamar Bing da MSN), kana yin kwangila ne tare da Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. Idan ka biya don amfani da wani ɓangare na Sabis-sabis ɗin, kana kwangila ne tare da Microsoft Japan Co., Ltd (MSKK), Shinagawa Grand Central Tower, 2-16-3 Konan Minato-ku, Tokyo 108-0075. Ga Sabis-sabis na kyauta da kuma na biya, dokokin Japan ke kula da fashin-baƙi na waɗannan Sharuɗɗa da kuma ƙorafe-ƙorafe kan keta su, koda kuwa wace irin babbar doka ce ta saɓanin. Kai da mu duk mun amince da Kotun Gundumar Tokyo ta zama wajen shari’a da kuma warware duk wasu saɓani da suka taso dangane da ko suka shafi waɗannan Sharuɗɗa na Amfani da Sabis-Sabis.
 • f. Jamhuriyar Korea. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Jamhuriyar Korea, kuma kana amfani da wasu ɓangarori na Sabis-sabis (kamar Bing da MSN), kana yin kwangila ne tare da Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. Idan ka biya don amfani da wani ɓangare na Sabis-sabis ɗin, kana kwangila ne tare da Microsoft Korea, Inc., Bene na 11, Tower A, K-Twin Tower, Jongro 1 gil 50, Jongro-gu, Seoul, Jamhuriyar Korea, 110-150. Ga Sabis-sabis na kyauta da kuma na biya, dokokin Jamhuriyar Korea ke kula da fashin-baƙi na waɗannan Sharuɗɗa da kuma ƙorafe-ƙorafe kan keta su, koda kuwa wace irin babbar doka ce ta saɓanin. Kai da mu duk mun amince da Babbar Kotun Gundumar Seoul ta zama wajen shari’a da kuma warware duk wasu saɓani da suka taso dangane da ko suka shafi waɗannan Sharuɗɗa na Amfani da Sabis-Sabis.
 • g. Taiwan. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Taiwan, kuma kana amfani da wasu ɓangarori na Sabis-sabis (kamar Bing da MSN), kana yin kwangila ne tare da Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. Idan ka biya don amfani da wani ɓangare na Sabis-sabis ɗin, kana kwangila ne tare da Microsoft Taiwan Corp., 18F, No. 68, Sec. 5, Zhongxiao E. Rd., Xinyi District, Taipei 11065, Taiwan. Ga Sabis-sabis na kyauta da kuma na biya, dokokin Taiwan ke kula da fashin-baƙi na waɗannan Sharuɗɗa da kuma duk wasu batutuwa da suka taso dagange ko suka shafe su ko Sabis-sabis. Domin ƙarin bayani dangane da Microsoft Taiwan Corp., duba shafin yanar gizon da Ministry of Economic Affairs R.O.C. ta samar da shi. Kai da mu duk mun amince da Kotun Gundumar Taipei ta zama wajen shari’a ta farko a kan duk wani saɓani da ya taso ko ya shafi waɗannan Sharuɗɗa na Amfani da Sabis-Sabis, zuwa iyakar da dokokin ƙasar Taiwan suke ƙyale.

Dokokin ƙasarka ta masu amfani da kaya suna buƙatar wasu dokin ƙasa don kulawa ko ba ka hakki na warware saɓani a wani zaure duk da waɗannan Sharuɗɗa. Idan haka ne, za a saka zaɓin doka da kuma samar da zaure a cikin sashe na 10 yadda dokokin masu amfani da kaya ta ƙyale.

Cikakken rubutu
YarjejeniyoyiYarjejeniyoyi12_Warranties
Taƙaitawa

11. Yarjejeniyoyi.

 • a. MICROSOFT, DA KUMA RASSANMU, MASU SAYARWA, MASU RARRABAWA, DA KUMA MASU SAYARWA, MAKE NO WARRANTIES, EXPRESS OR IMPLIED, GUARANTEES OR CONDITIONS WITH RESPECT TO YOUR USE OF THE SERVICES. KA FAHIMCI CEWA AMFANI DA SABIS-SABIS ƊIN ZAƁINKA NE KUMA CEWA MUN SAMAR DA SABIS-SABIS ƊIN NE “KAMAR YADDA SUKE” TARE DA DUK LAHANONI” DA KUMA “KAMAR YADDA YAKE SAMUWA.” MICROSOFT BA TA BAYAR DA TABBACI KO DAIDAITO KO AIKI CIKIN LOKACI NA SABIS-SABIS ƊIN BA. ƘILA KANA DA WASU HAKKOKI A ƘARƘASHIN DOKAR ƘASARKA. BA WANI ABU A CIKIN WAƊANNAN SHARUƊƊA DA YAKE NUFIN SHAFAR WAƊANNAN HAKKOKI, IDAN AKWAI SU. KA AMINCE CEWA KWAMFUTA DA SISTEM NA SADARWA BA WAI BA SA SAMUN MATSALA BA, A WASU LOKUTA SUKAN SAMU MATSALA. BA MA BAYAR DA TABBACIN CEWA DUK SABIS-SABIS ƊIN BA ZA SU KATSE BA, CIKIN LOKACI, TSARO, KO BA ZA SU SAMU MATSALA BA KO BA ZA A IYA ASARAR ƘUNSHIYA BA, HAKA NAN BA MA KUMA BAYAR DA TABBACIN DUK WANI HAƊI ZUWA KO WATSAWA DAGA KWAMFUTAR.
 • b. ZUWA GA ƘUREWAR DA DOKAR ƘASARKA TA BAYAR, BA MA CIRE DUK WASU YARJEJENIYOYI DA AKA SANYA, DA SUKA HAƊA DA NA KASUWANCI, GAMSUWA, INGANCI, DACEWA DA WATA BUƘATA, JAJIRCEWAR AIKI, DA KUMA RASHIN-KETA DOKA.
 • c. Ga masu amfani da suke zaune a Australia: Kayayyakinmu suna zuwa ne da garanti da ba za a iya cirewa a ƙarƙashin Dokar Masu Amfani da Kayayyaki ta Autralia ba. Kana da hakki na musanya ko ramuwa na bisa kasawa babba da kuma karɓar diyya ga duk wata asara da lalacewa da aka iya hangowa. Haka nan kana da hakki na gyara maka kayayyakin ko musanya su idan kayayyakin suk kasa cim ma ingancin da ake buƙata da kuma kasawar ba ta cim ma babbar kasawa ba
 • d. Ga masu amfani da suke zaune a New Zealand, ƙila kana da hakkoki na shari’a a ƙarƙashin Dokar Garanti ta Masu Amfani da Kayayyaki ta, kuma babu wani abu a cikin waɗannan Sharuɗɗa da zai shafi waɗannan hakkoki.
Cikakken rubutu
Iyakacin Ɗaukar NauyiIyakacin Ɗaukar Nauyi13_limitationOfLiability
Taƙaitawa

12. Iyakacin Ɗaukar Nauyi.

 • a. Idan kana da wata hujja na karɓar diyya (da ya haɗa da keta waɗannan Sharuɗɗa), zuwa iyakar da dokar da ta shafa ta ƙyale, ka yarda cewa magancewar ita ce maidowa, daga Maicrosoft duk ko duk rassansa, masu sake sayarya, masu rarrabawa, Aikace-aikacen Wasu da kuma masu samar da Sabis-sabis, da dillalai, diyya ta kai tsaye wanda yake daidai da kuɗin Sabis-sabis ɗinka na watan da asarar ko keta dokar ta auku (ko har zuwa Dalar Amurka $10.00 idan Sabis-sabis ɗin kyauta suke).
 • b. Har iyakanci da dokar da take shafa take yarda da, ba za ka iya dawo duk wata (i) babbar lalacewa ko asara ba; (ii) asarar anihin riba ko wadda ake sa-rai (kai tsaye ko kaikaice); (iii) asarar ainihin kuɗin shiga ko wanda ake sa-rai (kai tsaye ko kaikaice); (iv) rasa kwangila ko kasuwanci ko sauran asarori ko lalacewa da suka taso sanadiyyar amfani da Sabis-sabis da kake yi a matsayi wanda ba keɓaɓɓe ba; (v) lalacewar musamman, ko a kaikaice, lalacewa ko asarar da ba ta gangan ba; kuma (vi) zuwa wa’adin da doka ta ƙyale, asarori ko lalacewa na kai tsaye fiye da wanda aka bayyana a sashe na 12(a) da ke sama. Waɗannan iyakoki da kuma wariya sun shafi idan ba a biya ka cikakkiyar diyar wannan warwarewa ba na duk wata asara ko kasa ainihin dalilinsa ko idan mun sani ko ba mu sani ba game da yiwuwar lalacewar. Zuwa wa’adin da doka ta ƙyale, waɗannan iyakoki da wariya da aka sa ga komai ko duk wasu koke-koke da suka shafi waɗannan Sharuɗɗa, Sabis-sabis ɗin, ko manhaja da ta shafi Sabis-sabis ɗin.
 • c. Microsoft ba ta da alhaki ko ɗaukar nauyi ga duk wata kasawa ta aiki ko jinkiri wajen aiwatar da wajibcinsa a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa zuwa iyakar kasawa ko jinkiri da ya auku da ya fi ƙarfin hakkin Microsoft (misali taƙaddama kan biyan lada, dalilai daga Ubangiji, yaƙi ko aikin ƴan ta’adda, lalacewa mai cutarwa, haɗari ko bin duk wata doka ko dokar gwamnati da aka saka). Microsoft za yi ƙoƙarin taƙaita sakamako na ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan aukuwa don aiwatar da wajibcinsa da ba a shafe su ba.
Cikakken rubutu
Sharuɗɗan Keɓaɓɓen-SabisSharuɗɗan Keɓaɓɓen-Sabis14_service-SpecificTerms
Taƙaitawa

13. Sharuɗɗan Keɓaɓɓen-Sabis. Sharuɗɗan kafin da kuma bayan sashe na 13 an sanya su gaba ɗaya ga duk Sabis-sabis. Wannan sashe ya ƙunshi sharuɗɗan keɓɓɓen-sabis da suke ƙari ne ga sharuɗɗa na gaba ɗayan. Waɗannan sharuɗɗa suna aiki ne idan akwai wasu saɓani ga sharuɗɗa na gaba ɗayan.

Cikakken rubutu
Xbox Live da Wasannin Microsoft Studios da kuma ManhajojiXbox Live da Wasannin Microsoft Studios da kuma Manhajoji14a_XboxLive
Taƙaitawa
 • a. Xbox Live da Wasannin Microsoft Studios da kuma Manhajoji.
  • i. Amfani na kai da ba na Kasuwanci ba. Xbox Live, Wasanni na Windows Live da kuma wasannin Microsoft Studio, manhajoji, sabis-sabis da kuma ƙunshiya da Microsoft ta samar (a tattare, wato "Sabis-sabis ɗin Xbox") kawai don amfaninka ne kawai amma ba amfani na kasuwanci ba.
  • ii. Sabis-sabis na Xbox. Idan ka yi rajistar Xbox Live da kuma/ko karɓar Sabis-sabis na Xbox, ana sa-ido ga bayani game da buga wasanka, ayyuka, da kuma amfani da wasanni, kuma za a bi sawun Sabis-sabis na Xbox da kuma raba su ga wasu masu samar da wasa da suka shafa don ba wa Microsoft da wasu masu samar da wasa sarrafa wasanninsu da kuma isar da Sabis-sabis na Xbox. Idan ka zaɓa ka haɗa asusun Sabis-sabis na Microsoft Xbox tare da asusunka a kan wani sabis da ba na Microsoft ba (alal m isali, wani mawallafin wasa da ba na Microsoft ba na Ka'idodi da Sabis-sabis na Wasu), ka yarda da cewa: (a) Microsoft yana iya raba taƙaitaccen bayanin asusu (da ya haɗa ban da taƙaitawa tambarin mai wasa, makin mai wasa, makin wasa, tarihin wasa, da jerin abokanai), tare da wancan wasu wanda ba Microsoft ba yadda aka bayyana a cikin Jumlar Sirri ta Microsoft, kuma (b) idan aka bari ta saittunan sirri na Xbox ɗinka, wasu wanda ba Microsoft ba yana iya kuma samun iso ga zuwa Ƙunshiyarka daga sadarwar cikin wasa idan ka shiga cikin asusunka tare da wancan wasu da ba Microsoft ba. Haka nan, idan saitunan sirri na Xbox ɗinka ya ƙyale, Microsoft ɗa ta iya wallafa suna, alamar-ɗan-wasa, take, abata, bidiyon ɗan-wasa da kuma wasanni da ka buga cikin sadarwa da mutanen da ka ƙyale.
  • iii. Ƙunshiyarka. A zaman wani ɓangare na gina al’ummar Sabis-sabis ɗin Xbox, kana ba wa Microsoft, rassanta da kuma ƙananan masu lasisi haƙƙi na kyauta da kuma na gamegari, don yin amfani da, gyara, sake sarrafa, rarraba, da kuma nuna Ƙunshiyarka ko sunanka, tambarin mai wasa, take, ko avatar da ka aika don wasu Sabis-sabis ɗin Xbox.
  • iv. Manajojin Wasa. Wasu wasanni ƙila su yi amfani da manajojin wasa da kuma masu shirya wasa. Manajojin wasa da kuma masu shirya wasa ba su ne masu magana da yawun Microsoft da suke da izini ba. Abubuwan da suke tunani ba dole ba ne ya dace da na Microsoft.
  • v. Yara a kan Xbox. Idan kai ƙaramin yaro ne kake amfani da Xbox Live, iyayenka ko mai kula da kai zai iya samun dama a kan abubuwa da dama na asusunka kuma ƙila ya sami rahoto game da yadda kake amfani da Xbox Live.
  • vi. Kuɗin Wasa ko Kayayyaki na Tafi da Gindaka. Sabis-sabis ɗin ƙila su haɗa da kuɗin tafi da gindaka ko na wasa (kamar zinare, sulalla ko maki) da ƙila za a iya saye daga Microsoft ta amfani da kuɗi na gaske idan ka kai shekarun “balaga” a inda kake zaune. Ayyukan ƙila haka nan su haɗa da tafi da gindaka, abubuwa ko kayayyakin dijital da ƙila za a iya saye daga Microsoft ta amfani da kuɗi na gaskiya ko kuɗin wasa. Kuɗin wasa ko kayayyaki na tafi da gidanka ƙila ba za a iya karɓarsu don kuɗi na gaske ba, kayayyaki da kuma sauran abubuwa na darajar kuɗi daga Microsoft ko wani daban. Fiye da taƙaitacce, keɓaɓɓe, wanda za a iya sokewa, wanda ba za a iya turawa ba, wanda ba za a iya ƙaramin lasisi ba don amfani da kuɗin wasa ko kayayyaki na tafi da gidanka a cikin Sabis-sabis ɗin kawai, ba ka da wani hakki ko dama a ciki ko ga wannan kuɗi na wasa ko kayayyaki na tafi da gidanka da suke bayyana ko samo tushe a cikin Sabis-sabis ɗin, ko duk wasu sauran hanyoyi da alaƙanta su ga amfani da Sabis-sabis ɗin ko aka adana su a cikin Sabis-sabis ɗin. Microsoft a kowane lokaci tana kulawa, sarrafa ko gyara da kuma/ko ɓatar da kuɗin wasa da kuma/ko kayayyakin tafi da gidanka da ta ga ya dace bisa tunaninta.
  • vii. Sabuntawan Sofwaya. Ga duk wata na’ura da ba za ta iya haɗi da Sabis-sabis na Xbox ba, ta yiwu mu bincika sigar sofwaya na Xbox console ɗinka kai tsaye ko sofwayar manhajar Xbox da kuma sauke Xbox console ko sabunta sofwayar manhajar Xbox ko saita sauye-sauye, da suka haɗa da waɗanda suke hana ka samun iso ga Sabis-sabis na Xbox, ta amfani da wasannin Xbox marasa izini ko manhajojin Xbox, ko ta amfani da manyan na’urorin hadwaya marasa izini tare da wani Xbox console.
  • viii. Ƙarewar Tambarin mai wasa. Dole na ka shiga cikin Sabis-sabis ɗin Xbox aƙalle sau ɗaya a cikin tsawon lokaci na shekara-biyar, idan ba haka ba kana iya rasa iso ga tambarin mai wasa ɗin da aka dangantaka da asusunka da kuma wancan tambarin mai wasa yana iya samuwa don amfani ta wajen wasu.
  • ix. Arena. Arena wani Sabis ɗin Xbox ne wanda Microsoft ko wasu za su iya samar maka da dama ta shiga ciki ko ƙirƙirar gasar wasannin bidiyo, a wasu lokuta tare da kyauta ("Gasa"). Amfaninka da Arena ya ta’allaƙa da waɗannan Sharuɗɗa, kuma ta yiwu a buƙaci ka yarda da ƙarin wasu sharuɗɗan Gasa, sharuɗɗa da kuma dokoki da masu shirya Gasar a yayin rajista ("Sharuɗɗan Gasa"). Ƙila a saka dokokin cancanta, kuma ƙila su bambanta bisa iko. Gasa tana lalacewa a yayin da doka ta hana ko ta taƙaita. Keta waɗannan Sharuɗɗa (da suka haɗa da Dokar Ɗa’a) ko Sharuɗɗan Gasa za su iya haifar da horo ko hana shiga Gasar. Idan ka ƙirƙiri wata Gasa, ta yiwu ba za ka buƙaci wasu dokokin Gasa da ƙila Microsoft (bisa ganin damarta) ta ga sun saɓa da waɗannan Sharuɗɗa. Microsoft tana da iko na soke duk wata Gasa a kowane lokaci.
  • x. Cuta da kuma Lahanta Sofwaya. Ga duk wata na’ura da za ta iya haɗi da Sabis ɗin Xbox, muna iya bincika na’urarka don hadwaya da ba a ba wa izini ba ko sofwaya da take ƙyale cuta ko lahani wajen keta Dokar Ɗa’a ko waɗannan Sharuɗɗa, da kuma sauke sabunta sofwaya na manhajar Xbox ko saita sauye-sauye, da suka haɗa da waɗanda za su iya hana ka samun iso ga Sabis-sabis ɗin Xbox, ko daga amfani da hadwaya marar izini ko sofwaya da take ƙyale cutarwa ko lahani.
  • xi. Mixer.
   • 1. Asusu-asusun Mixer da Ausu-asusun Microsoft. Idan kana amfani da Sabis ɗin Mixer da wani asusun Mixer, sannan ne wannan amfani zai kasance cikin Sharuɗɗan Sabis na Mixer da yake samuwa a https://mixer.com/about/tos. Idan ka yi amfani da Sabis ɗin Mixer tare da wani asusun Microsoft, sannan amfaninka ya shiga cikin waɗannan Sharuɗɗa Ana sanya waɗannan Sharuɗɗa a inda yake akwai saɓani.
   • 2. Ƙunshiyarka a kan Mixer. "Ƙunshiyarka a kan Mixer" yana nufin duk ƙunshiya, kai, ko wani ya ƙirƙira a madadinka a kan Sabis ɗin Mixer, da suka haɗa amma ban da iyakancewa da saukewar yanzu ko wanda aka yi rikod (da kuma duk wata ƙunshiya, kamar ƙunshiyar kallo, da suka ƙunshi); sunayen samfuri, alamomin kasuwanci, alamomin sabis, sunayen kasuwanci, tambarori, ko alamar asali; sharhohinka, alamomin yanayi, da kuma aiki a cikin tashohin Mixer (da suka haɗa da ƙunshiyar samarwa daga-bot); da kuma duk ƙarin bayanai masu alaƙa. Kowa, haɗe da Microsoft da kuma masu amfani, za su iya gani, amfani, sauka, sake samarwa, gyara, watsawa, wallafawa, ga jama’a da kuma aiwatarwar digital da kuma nunawa, fassarawa, daidata, da kuma ko ba haka ba cin moriyar Ƙunshiyarka a kan Mixer, ta kowace irin hanya, tsara, midiya, ko tashoshi da aka sani a yanzu ko za a samar a nan gaba.
   • 3. Dokar Ɗa’a da ta Shafi Mixer. Danna nan don ƙarin bayani game da Dokar Ɗa’a ta Microsoft da ta shafi Mixer.
   • 4. Amfani da Sabis ɗin Mixer.
    • a. Ƙarancin Shekara. Ta amfani da Sabis ɗin Mixer, ka amince ka kai aƙalla shekara 13, idan kai ɗan ƙasa da shekaru ne a mafi yawan mutanen da kake raye da su, iyaye ko mai kula ne suke lura da amfani da kake yi.
    • b. Ɓoyayye da da Amfani wanda yake ba a Ɓoye ba. Za ka iya amfani da Mixer a ɓoye idan kana son ganin ƙunshiya ne kaɗai. Idan ba haka ba, akwai buƙatar ka ƙirƙiri wani asusu, da shiga, mu kuma za mu ganarwa da wasu masu amfani ta sunanka na Mixer.
    • c. Asusu-asusu da Amfani wanda yake ba a Ɓoye ba. Za ka iya ƙirƙurar wani asusun Microosft da kuma/ko wani asusun Mixer don amfani da Sabis ɗin Mixer wanda yake sananne ba ɓoyayye ba. Za ka iya ƙirƙirar wani asusun Mixer ta yin rajista a kan layi. Dole ne ka yi amfani da asusun Mixer ɗinka don barinsa yin aiki. Shig cikin Sabis ɗin Mixer aƙalla sau ɗaya a cikin tsawon shekara 5 don barin laƙabinka da ya shafi Mixer tare da asusun Microsoft ɗinka.
   • 5. Sanarwar Sabis. Idan akwai wani abu mai muhimmanci mu sanar da kai game da Sabis ɗin Mixer, za mu aika maka sanarwar Sabis zuwa imel ɗin da ya shafi asusun Mixer ɗinka da kuma/ko asusun Microsoft.
   • 6. Goyon baya. Goyon bayan abokan ciniki na Sabis ɗin Mixer yana samuwa a mixer.com/contact.
Cikakken rubutu
Wurin AdanaWurin Adana14b_Store
Taƙaitawa
 • b. Wurin Adana. “Wurin Adana” yana nufin wani Sabis da yake ba ka damar bincika, sauke, saye, da kuma bitar manhajoji (kalmar “manhaja” ta haɗa da wasanni) da kuma sauran ƙunshiyar dijital. Waɗannan Sharuɗɗa sun haɗe da amfani da Wurin Adana na Windows da kuma Wurin Adana na Xbox. "Wurin Adana na Office" yana nufin wani Wurin Adana na samfurorin Office da kuma manhajojin Office 360, SharePoint, Exchange, Access da kuma Project (sigogin 2013 ko na sababbi), ko duk sauran gogewa mai suna Wurin Adana na Office. "Wurin Adana na Windows" yana nufin wani Wurin Adana na Windows kamar waya, kwamfuta da ƙaramar kwamfuta, ko duk sauran gogewa mai suna Wurin Adana na Windows. "Wurin Adana na Xbox" yana nufin wani Wurin Adana na Xbox One da kuma na’urorin Xbox 360, ko duk sauran gogewa mai suna Wurin Adana na Xbox.
  • i. Sharuɗɗan Lasisi. Za mu gano mawallafin kowace manhaja da take samuwa cikin Wurin Adana mabambanta. Sai dai idan an samar da wasu sharuɗɗan lasisi daban tare da manhajar, Standard Application License Terms ("SALT") a ƙarsjen waɗannan Sharuɗɗa wasu yarjejeniyoyi ne tsakaninka da kuma mawallafin manhajar ya saka sharuɗɗan lasisin da suka shafi wata manhaja da ka sauke ta hanyar Wurin Adana na Windows ko Wurin adana na Xbox. Don ganewa, waɗannan Sharuɗɗa sun shafi amfani, da kuma sabis-sabis da Sabis-sabis na Microsoft ya samar. Sashe na 5 na waɗannan Sharuɗɗa haka nan ya shafi Sabis-sabis da Manhajoji na Wasu da aka samu ta wata hanyar wani Wurin adana. Manhajoji da aka sauke ta hanyar Wurin Adana na Office ba sa ƙarƙashin kulawar SLT kuma suna da keɓɓun sharuɗɗan lasisi da aka sanya.
  • ii. Sabuntawa. Microsoft za ta bincika da kuma sauke sabuntawa ta otomatik zuwa manhajojinka, koda idan ba ka shiga zuwa Wurin Adana mabambanta ba. Za ka iya sauya Wurin Adana ko saitunan sistem ɗinka idan ka fi son kada ka karɓi sabuntawar otomatik ga Manhajoji na Wurin Adana. Amma, ya yiwu a sabunta wasu manahajojin Wurin Adana Office da ake sauka cikakke ko wani ɓangare a kan layi a kowane lokaci ta wajen mai ƙira na manahajar kuma ya yiwu ba za a buƙaci izininka don sabuntawa ba.
  • iii. Ƙimance-Ƙimance da Bitoci. Idan ka kimanta ko ka yi bitar wata manhaja a cikin Wurin Adana, ƙila ka sami wani imel daga Microsoft da ya ƙunshi ƙunshiyar daga mawallafin manhajar ko Kayan Dijital. Kowane irin wannan imel yana zuwa daga Microsoft; ba ma raba adireshin imel ɗinka tare da mawallafan manahajoji ko Kayayyakin Dijital da ka samu ta hanyar Wurin Adana.
  • iv. Gargaɗin Kariya. Don gujewa rauni, rashin jin daɗi, ko matsalar ido da yake yiwuwa, ya kamata ka ɗauki hutu lokaci-lokaci daga yin amfani da wasanni da sauran manahajoji, musamman idan kana jin wani ciwo ko kasala a sanadiyyar amfanin. Idan ka ɗanɗana rashin jin daɗi, ɗauki hutu. Rashin jin daɗi yana iya haɗa jiwa na tashin zuciya, ciwon motsi, hajijiya, yamutsi, ciwon kai, gajiya, matsalar ido, ko ƙeƙasattun idanu. Yin amfani da manahajoji yana iya ɗauke maka hankali da kuma yi wa muhallanka babakere. A kauce haɗarorin tuntuɓe, matakala, silin da ya yi ƙasa, abubuwan aras ko masu ƙima da suke iya lalacewa. Wani kason mutane ƙasan ƙila su iya fuskantar kamuwa a yayin kallon wasu hotuna kamar wuta mai walƙiya ko samfurorin da ƙila za su bayyana a cikin manhajojin. Ko da mutane waɗanda ba su da tarihin kamuwa ƙila su sami wani hali da ba a bincika ba da zai haddasa waɗannan kamuwa. Alamomi da suka haɗa da jiri, matsalar gani, kumburi, kakarewa ko motsa laɓɓa, ruɗewa da kuma rasa nutsuwa, ko farfaɗiya. Dakatar da amfani nan-da-nan ka kuma tuntuɓi likita idan ka fuskanci ɗaya daga cikin waɗannan alamomi, ko ka tuntuɓi likita kafin amfani da manhajar idan ka taɓa fuskantar alamomi da aka dangata su da kamuwa. Iyaye za su kula da amfani da ƴaƴansu suke yi da manhajojin don alamomi na kamuwa.
Cikakken rubutu
Fuskokin Iyali na MicrosoftFuskokin Iyali na Microsoft14c_MicrosoftFamily
Taƙaitawa
 • c. Fuskokin Iyali na Microsoft. Iyaye da yara suna iya yin amfani da fuskokin iyali na Microsoft don gina aminci dogara da wata fahimtar juna kan waɗanne halaye, shafukan yanar gizo, manahajoji, wasanni, wurare na zahiri, da kuma kashe kuɗi da suka dace a cikin iyalinsu. Iyaye suna iya ƙirƙirar wani iyali ta zuwa https://account.microsoft.com/family (ko ta bin umurnu a kan na’urorin Windows ko na’urar Xbox ɗinsu) da kuma gayyaci yara ko sauran iyaye don shiga. Akwai fuskoki da dama da suke samuwa ga mambobin Iyali, saboda haka ka yi bitar bayanin da ka samar a hankali a lokacin da kake yarda ka ƙirƙiri ko shiga wani iyali da kuma a lokacin sayen Kayayyakin Dijital don samun iso na iyali. Ta ƙirƙira ko shiga wani iyali, ka nuna cewa za ka yi amfani da iyali ta bin manufarsa kuma ba za ka yi amfani da shi a cikin wata hanya marar izini da ta saɓawa doka don samun iso ga bayanan wani ba.
Cikakken rubutu
Aika saƙo na RukuniAika saƙo na Rukuni14d_GroupMessaging
Taƙaitawa
 • d. Aika saƙo na Rukuni. Iri-irn ayyukan Microsoft suna bari ka aika saƙo zuwa ga wasu ta hanya murya ko SMS ("saƙonni"), da kuma/ko barin Microsoft da masu dangantaka da Microsoft yake sarrafa su aika maka ko ƙarin sauran masu amfani irin waɗannan saƙonni a madadinka. IDAN KA UMURCI MICROSOFT DA KUMA MASU DANGANTAKA DA MICROSOFT YAKE SARRAFA SU AIKA MAKA KO MA WASU IRIN WANNAN SAƘONNI, KANA NUNA KUMA KA TABBATAR MANA CEWA KAI DA KUMA KOWANE MUTUM DA KA UMURCE MU MU AIKA SAƘO YA YARDA YA KARƁI IRIN WAƊANNAN SAƘONNI DA KUMA SAURAN SAƘONNI RUBUTU NA HUKUMA MASU ALAƘA DAGA MICROSOFT DA KUMA MASU DANGANTAKA DA MICROSOFT YAKE SARRAFA. "Saƙon rubutu na hukuma" saƙonnin cinikaya na lokaci-lokaci ne daga wani sabis na Microsoft, da ya haɗa amma bai taƙaice a wani "saƙon maraba" ko umurnu a kan yadda ake tsai da karɓowa saƙonni. Kai ko mambobin rukuni wanda ba ya so ya karɓi irin waɗannan saƙonni ba kuma yana iya fita daga karɓowa ƙarin saƙonni daga Microsoft ko masu dangantaka da Microsoft yake sarrafa a kowane lokaci ta bin umurnun da aka samar da. Idan ba ka so ka karɓi irin waɗannan saƙonni ko hallara cikin rukunin ba kuma, ka yarda da cewa za ka fita ta hanyar umurnun da aka samar da ta wajen shiri ko aiki da ya shafa. Idan kana da dalili don amince cewa wani mamba na rukuni ba ya so ya karɓi iri waɗannan saƙonni ko hallara cikin rukunin ba kuma, ka yarda a cire su daga rukunin. Haka kuma ka nuna da kuma tabbatar mana cewa kai da kuma kowane mutum da ka umurce mu mu aika ma saƙo ya gane cewa kowane mamba na rukuni yake ɗauka nauyin kuɗin kowane saƙonni da aka iso ga ta wajen kamfanin sadarwa ɗinsa ko ɗinta, da ya haɗa kowane caje-cajen saƙonni na ƙasasshe waje da suke iya shafa a lokacin da ake watsar da su daga lambobin dogara da US.
Cikakken rubutu
Skype da GroupMeSkype da GroupMe14e_Skype
Taƙaitawa
 • e. Skype da GroupMe.
  • i. Ba Dama ga Sabis-Sabis na Gaggawa. Akwai muhamman bambance-bambance tsakanin tarho sabis-sabis na tarho da kuma Skype. Ba a buƙatar Skype ya samar da dama ga Sabis-sabis na Gaggawa a ƙarƙashin kowace irin doka ta ƙasa/ko dokokin ƙasa, dokoki ko doka. Ba a niyyar manhajar da samfurin Skype su goyi bayan kiran gaggawa ga duk wani nau’in asibiti, hukumomi, wuraren kula da lafiya ko duk wani nau’in sabis-sabis da yake haɗa mai amfani da sabis-sabis na gaggawa ko wuraren amsa tambayoyin al’umma na kariya ba ("Sabis-Sabis na Gaggawa"). Ka karɓa kuma ka yarda cewa: (i) nauyin ka ne sayen wayar hannu marar waya ta da ko sabis-sabis na layin tarho bayan wannan tayi na samun iso ga Sabis-sabis na Gaggawa, kuma (ii) Skype ba maye gurbi ne na sabis ɗin tarhonka na gida ba.
  • ii. APIs ko Watsawa. Idan kana son amfani da Skype domin haɗi da duk wata watsawa, dole ne ka bi dokokin "Watsa TOS" a https://www.skype.com/go/legal.broadcast. Idan kana son yin amfani da duk wani shirin hulɗa na manhaja ("API") da Skype ta nuna ko ta samar da shi dole ne ka bi sharuɗɗan lasisin da aka sanya, waɗanda suke samuwa www.skype.com/go/legal.
  • iii. Amfani da Dokoki Bisa Adalci. Ƙila a sanya amfani da dokoki bisa adalci ga amfani da Skype da kake yi. Yi bitar waɗannan dokoki waɗanda aka shirya don kare ga daga zamba da kuma cin mutunci kuma ƙila za su iya sa iyakoki a kan nau’i, tsawon lokaci ko ƙara ka kira ko saƙonni da ka sami damar yi. An haɗe waɗannan dokoki a cikin waɗannan Sharuɗɗa bisa nuni. Za ka iya samun waɗannan dokoki a https://www.skype.com/go/terms.fairusage/.
  • iv. Sa Taswira. Skype yana ƙunshe da wasu siffofi da suke ba ka damar miƙa bayani zuwa, ko saka kanka kan wata taswira, wato sabis na sa taswira. Ta yin amfani da waɗancan fuskoki, ka yarda da waɗannan Sharuɗɗa da kuma sharuɗɗan Google Maps da suke samuwa a https://www.google.com/intl/en_ALL/help/terms_maps.html ko irin wancan sharuɗɗan Google Maps da suke samuwa a ƙasarka.
  • v. Masu Amfani Mahukunta. Idan kana son amfani da wani asusun kasuwanci ko Manajan Skype a madadin Hukumar Amurka ko wata ma’aikata da ke ƙarƙashin Hukumar Amurka, waɗannan Sharuɗɗa ba su shafi wannan amfani ba. Ga sharuɗɗa da aka sanya ko ƙarin bayani, a tuntuɓi usgovusers@skype.net.
  • vi. Amfani Keɓaɓɓe/Wanda ba na kasuwanci ba. Amfani da Skype don kanka ne kawai amma ba amfanin kasuwanci ba. An ba ka damar amfani da Skype a wurin aiki don sadarwar kasuwancinka na kanka.
  • vii. Lambar Skype/Skype Yayin Tafiya. Idan Skype ta samar maka da wata Lambar Skype ko lambar Skype To Go, ka yarda cewa ba ka mallaki wannan lamba ba ko ba ka da hakki na riƙe lambar har abada. A wasu ƙasashe, ƙila abokan hulɗar Skype su samar maka da wata lamba amma ba Skype ba, kuma akwai buƙatar ka shiga wata keɓɓiyar yarjejeniya da wannan abokin hulɗa.
  • viii. Manajan Skype. Wani "Asusun Gudanarwa na Manajan Skype" wani asusun Skype ne da aka ƙirƙiri kuma da kake gudanar da shi, wanda yake yi aiki a matsayin wani ɗaiɗaikun mai gudanarwa na wani rukunin Manajan Skype kuma ba a matsayin wani abun kasuwanci ba. Ana iya haɗa asusu-asusun Skype na mutum da wani rukunin Manajan Skype ("Haɗaɗɗen Asusu"). Ƙila za ka iya naɗa ƙarin masu gudanarwa ga rukunin Manajan Skype ɗinka gana wa amincewarsu ga waɗannan Sharuɗɗa. Idan ka kasafta Lambobin Skype zuwa wani Haɗaɗɗen Asusun, kai ke da alhaki na bin duk wasu buƙatu da suka danganta da zama ko wuri na masu amfani da Haɗaɗɗen Asusun ɗinka. Idan ka zaɓa a cire haɗi wai Haɗaɗɗen Asusun daga wani rukunin Manajan Skype, ba za a ɗauko kowaɗane rajistoci, Kuɗin Skype ko Lambobin Skype da aka kasafta ba kuma Ƙunshiyarka ko kaya da suka dangantaka da asusun Skype da aka cire haɗin ba za ka iya iso ga su kuma ba. Ka yarda ka sarrafa kowane keɓaɓɓen bayani na masu amfani na Haɗaɗɗen Asusun ɗinka dangane da dokokin kariyar bayanai da suke shafa.
  • ix. Cajin Kuɗi na Skype. Duk farashin samfurorin Skype da aka biya sun haɗa da haraji da aka saka, sai dai idan an bayyana akasin haka. Cajin da ake biya na kiran wayoyi da suke wajen rajista ya haɗa da kuɗin haɗi (da ake caja sau ɗaya ga kowane kira) da kuma farshin minti kamar yadda aka bayyana a www.skype.com/go/allrates. Za a ɗebe cajin kiran ne daga ragowar Kuɗin Skype. Skype ƙila ta iya sauya farashin kiranta a kowane lokaci ba tare da sanar maka ba ta buga wannan sauyi a www.skype.com/go/allrates. Za a saka sabon farashi ga kiranka na gaba bayan wallafa sabon farashin. Bincika sababbin farashi kafin yin kira. Za a saka cajin kira na lokuta kaɗan da cajinsu a amfani na gaba. A wasu ƙasashe, za a saka sharuɗɗan abokan hulɗa na samfuroin biya na Skype da abokan hulɗar Skype na ƙasa suke samarwa a cikin wannan hada-hada.
  • x. Kuɗin Skype. Skype ba ya bayar da tabbaci cewa zai sami damar yin amfani da ragowar Kuɗin Skype don sayen duk samfurorin biya na Skype. Si no utiliza el Crédito de Skype durante un período de ciento ochenta (180 días), Skype inactivará su Crédito de Skype. Za ka iya sake dawo da Kuɗin Skype ta bin hanyar sake dawowa a https://www.skype.com/go/store.reactivate.credit. Idan kana da zama a Japan kuma ka sayi Kuɗin Skype daga shafin yanar gizo na Skype, jumloli biyu da suka gabata ba su shafe ka ba, kuma Kuɗin Skype ɗinka zai ƙare cikin kwanaki 180 bayan ranar sayen. Da zarar kuɗinka ya ƙare, ba za ka sami damar sake kunna shi ko amfani da shi ba. Za ka iya ƙyale siffar Sabuntar-Oto idan ka sayi Kuɗin Skype ta danna akwatin da ya dace. Idan an ƙyale, za iya ƙara kuɗi a ragowar Kuɗin Skype ɗinka adadin kuɗi ɗaya da kuma zaɓinka na hanyar biyan kuɗi a duk lokacin da ragowar asusun Skype ɗinka ya je ƙasa da wurin da Skype take saitawa daga lokaci-zuwa-lokaci. Idan ka sayi wata rijista tare da wata hanyar biyan kuɗi wadda ba ta katin bashi, PayPal ko Moneybookers (Skrill) ba, kuma ka ƙyale Sabuntawar-Oto, za a caji ragowar Kuɗin Skype ɗinka adadin kuɗi na wajibi don maimaita rajistarka ta gaba. Za ka iya hana Sake Caji na Oto a kowane lokaci ta samun iso da kuma saua saitunanka a cikin asusun Skype.
  • xi. Caje-cajen Saƙo na Ƙasasshen waje. GroupMe yana yin amfani da lambobi dogara da US a yanzu don kowane rukuni da aka ƙirƙiro. Kowane saƙon rubutu da aka aika ko karɓa daga wata lambar GroupMe zai lissafa a zaman wani saƙon rubutu na ƙasasshen waje da aka aika ko karɓa daga Hadaddiyar Daula. Don Allah bincika da mai samarwa ɗinka don kuɗin ƙasashen waje da suka dangantaka.
  • xii. Aika da kuma karɓar kuɗi. Ta amfani da siffar aika da kuma karɓar kuɗi (idan kawai), ka amince cewa Skype ya yi amfani da wasu don samar maka da sabis-sabis na kuɗi da kuma zartar da turawar. Skype ba ya samar da sabis-sabis na biyan kuɗi ko zartar da turawa kuma ba kasuwanci ne na sabis-sabis ɗin kuɗi ba. Aika da kuma karɓar kuɗi a kan Skype wataƙila zai iya samuwa ne kaɗai ga masu amfani da suke ‘yan shekara 18 ko fiye (idan ba haka ba bisa dacewa da sharuɗɗan wasun) da kuma waɗanda suka yi rajista aka kuma amince da asusunsu tare da wasu masu samarwa. Don amfani da siffar aika kuɗi, wataƙila ka buƙaci yin rajista ga sharuɗɗa da ƙa’idoji na wasu da kuma samar da izini don raba bayananka tare da wasun don dalilan samar da sabis ɗin. Idan Skype ta sami sanarwa cewa kana amfani da siffar aika kuɗi da ya keta doka da ƙa’idar wasun, Skype za ta iya ɗaukar mataki a kan asusunka, kamar soke ko dakatar da asusunka. Skype, ko Microsoft ba za su ɗauki alhaki na sabis-sabis ɗin biyan kuɗi da wasu suka samar ba ko ɗaukar duk wani mataki a ƙarƙashin sharuɗɗa da ƙa’idoji na wasun ba. Skype ba ta bada tabbaci, wakilci ko garantoci na cewa siffar aika da kuma karɓar kuɗi za ta samu ko ci gaba da samuwa ba.
Cikakken rubutu
Bing da MSNBing da MSN14f_BingandMSN
Taƙaitawa
 • f. Bing da MSN.
  • i. Kayayyakin Bing da MSN. Maƙalolin, rubutu, hotuna, taswirori, bidiyoyi, fileyoyin bidiyo da kuma kayayyaki na wasu da suke samuwa a kan Bing da kuma MSN, da suka haɗa da Microsoft bots, manhajoji da kuma shirye-shirye, ba na amfanin kasuwanci ba ne, don amfaninka ne kawai. Sauran amfani, sun haɗa da saukewa, kwafi ko rarraba waɗannan kayayyaki, ko amfani da waɗannan kayayyaki ko samfurori don gina samfurori naka na kanka, ana ƙyale su ne kawai musamman zuwa iyakar da Microsoft ko masu mallakar hakkinsu ko dokar da ta shafa ta ƙyale. Microsoft da sauran masu hakkoki su ke da duk hakkoki ga manhajar da ba a bayyana ko bayarwa daga Microsoft ba, ko a kaikaice, da shaida, ko akasin haka.
  • ii. Tawirori na Bing. Ƙila ba za ka iya amfani da hoton Tsuntsu ba na Amurka, Canada Mexico, New Zealand, Australia ko Japan don amfani na kasuwanci ba tare da wararriyar amincewarmu a rubuce ba.
  • iii. Wuraren Bin ko Cibiyar Maƙerin Bin. Yayin da ka samar da Bayananka ko Ƙunshiyarka ga Wuraren Bin ko Cibiyar Maƙerin Bin, ka ba wa Microsoft wani lasisin fusaha gama-gari marar albashi don amfani, sake samarwa, adana, gyara, haɗe, tallata, watsa, nuna ko rarrabawa a zaman wani ɓangare na sabis ɗin, da kuma samar da ƙaramin lasisi na waɗannan hakkoki ga wasu.
Cikakken rubutu
CortanaCortana14g_Cortana
Taƙaitawa
 • g. Cortana.
  • i. Amfani na kai da ba na Kasuwanci ba. Cortana Sabis ne na keɓaɓɓen mataimaki na Microsoft. Siffofin, sabis-sabis, ƙunshiya da kuma Aikace-aikacen Wasu da kuma Sabis-sabis da Cortana take samarwa (gaba ɗayansu "Sabis-sabis na Cortana") don amfani ne na kai ba amfanin kasuwanci ba.
  • ii. Aiki da kuma Ƙunshiya. Cortana tana samar da siffofi masu faɗi, wasu daga cikinsu keɓaɓɓu ne. Sabis-sabis na Cortana zai iya ba ka damar iso ga sabis-sabis, bayani ko aiki da sauran Sabis-sabis na Microsoft ko Sabis-sabis da Manhajojin Wasu suke samarwa. Keɓaɓɓen-sabis na Sharuɗɗa na sashe na 13 haka nan ya shafi amfani da Sabis-sabis na Microsoft da ake samu ta hanyar Sabis-sabis na Cortana. Cortana tana samar da bayani ga dalilai na shirinka kawai kuma kai za ka yanke shawara a yayin bita da kuma dogara da wannan bayani. Microsoft ba ta bayar da tabbaci dogaro, samuwa ko samun sakamako cikin lokaci da Cortana ke samarwa. Microsoft ba ta da hakki idan gudanarwar sadarwar Cortana ta yi jinkiri ko hana ka karɓa, bita ko aika wata sadarwa ko sanarwa ba.
  • iii. Manhajoji da Sabis-Sabis na Wasu. A matsayin wani ɓangare na isar da Sabis-sabis ɗin Cortana, Cortana za ta iya musanyar bayani tare da Manhajoji da Sabis-Sabis na Wasu, kamar lambar zip ɗinka da kuma tambayoyi da kuma amsoshi da Manhajoji da Sabis-Sabis na Wasu suka dawo da su, don cim ma buƙatarka. Ta hanyar haɗa asusu, Cortana zai iya ƙyale masu amfani su yi sayayya ta hanyar Manhajoji da Sabis-Sabis na Wasu ta amfani da fifikon asusu da kuma saitunan da mai amfani ya ƙaddamar kai tsaye da waɗannan Manhajoji da Sabis-Sabis na Wasu. Masu amfani za su iya cire haɗin asusunsu a kowane lokaci. Amfani da da kake yi da Manhajoji da Sabis-Sabis na Wasu yana ƙarƙashin kulawar sashe na 5 na waɗannan Sharuɗɗa. Mawallafan Sabis-sabis da Manhajoji na Wasu za su iya canza ko daina ci gaba da aiki ko siffa ta Sabis-sabis da Manhajoji na Wasu ko haɗewa da Sabis-sabis na Cortana. Microsoft ba ta da alhaki ko nauyi na maƙerin da ya samar da sofwaya ko fimwaya ba.
  • iv. Na’urori Masu Damar Cortana. Na’urori Masu Damar Cortana samfurori ne ko na’urori da suke ƙyale samun iso ga Sabis-sabis Cortana, ko samfurori ko na’urori da suke jituwa da Sabis-sabis na Cortana. Na’urori Masu Damar Cortana sun haɗa da na’urorin wasu ko samfurori da ba mallaki, ƙira ko samarwar Microsoft ba ne. Microsoft ba ta da alhaki na na’urori da samfurori na wasu.
  • v. Sabuntawan Sofwaya. Don kowace na'ura da take iya haɗa da Sabis-sabis ɗin Cortana, muna iya bincika sigarka ta sofwaya na Sabis-sabis ɗin Cortana ta otomatik da kuma zazzage sabuntawan sofwaya ko canje-canjen tsari ko buƙatar duk wasu maƙeran na’urori masu damar Cortana su ci gaba da barin sofwata ɗin sabis-sabis ɗin Cortana cikin sabunta.
Cikakken rubutu
Outlook.comOutlook.com14h_Outlook_com
Taƙaitawa
 • h. Outlook.com. Adireshin imel na Outlook.com (ko @msn, @hotmail, ko @live) da ka yi amfani da shi wajen ƙirƙirar asusun Microsoft ɗinka zai kasance farɗa kawai gare ka matuƙar akwatin saƙon Outlook.com ɗinka ko asusun Microsoft yana aiki. A yayin da aka rufe akwatin saƙonka na Outlook.com inbox ko asusun Microsoft kai kanka ko daga Microsoft kamar yadda yake a cikin waɗannan Sharuɗɗa, ƙila a sake amfani da adireshin imel ɗink ko sunan mai amfani a cikin sistem ɗinmu a kuma bayar da shi ga wani mai amfani.
Cikakken rubutu
Sabis-sabis na OfficeSabis-sabis na Office14i_officeBasedServices
Taƙaitawa
 • i. Sabis-sabis na Office. Office 365 Home, Office 365 Personal, Office 365 University, Office Online, Sway, OneNote.com da kuma wani sauran rajistar Office 365 ko Sabis-sabis masu samfurin Office don amfani ne na kai, ba na kasuwanci ba, sai dai idan kana da iko a ƙarƙashin wata wararriyar yarjejeniya da Microsoft.
Cikakken rubutu
Sabis-sabis na Microsoft HealthSabis-sabis na Microsoft Health14j_MicrosoftHealthServices
Taƙaitawa
 • j. Sabis-sabis na Microsoft Health.
  • i. HealthVault. An samar maka da HealthVault don adana keɓaɓɓun bayananka da suka shafi lafiya da kuma bayani game da mutane (misali iyalinka) bisa amincewarsu. Asusu-asusun HealthVault ba na amfani ne ga asibitoci ko duk wani nau’in kasuwanci ko keɓaɓɓen amfani ba. Bayanin da ke cikin asusunka ba lallai ne koyaushe ya zama daidai ba ko sabo kuma kowane mai kula da lafiya zai gan shi ne kawai a matsayin bayani. Sabis ɗin HealthVault ba ya riƙe bayanai na masu kula da lafiya ko sauran sha’anin lafiya ko domin dalilai na gudanarwa. Misali, bayanan HealthVault ba bayanai bane da aka bayyana a ƙarƙashin dokokin Amurka. Idan wani mai kula da lafiya ya yanke shawarar haɗawa da duk wasu bayanai da aka samar daga HealthVault a cikin bayananka, za ta ajiye wani kwafi a cikin sistem ɗinta na kanta. Idan babu masu adana bayanai a cikin asusunka (saboda ɗayanku ya gayyaci ɗaya), ka nuna cewa mai adanawar yana da cikakken hakki kan bayanan kuma zai iya soke samun isonka ga bayanan, gudanar dadamar iso ta sauran mutane ga bayanan, da kuma duba bayanan da suke haɗa da yadda da kuma lokacin da aka yi amfani da bayanan. Microsoft ba ta goyon bayan bayanan shiga wanda ba Microsoft ba (misali Facebook ko OpenID), saboda haka goyon bayan abokan ciniki na HealthVault ba zai sami damar taimaka maka sa matsalolin shiga na waɗannan ba. Idan ka rasa bayanan shiga ɗinka, ko idan an rufe wurin da ka sami bayanan shiga asusunka, ba za ka sami damar dawo da adanannun bayananka ba. Don taimakawa ci gaba da samun iso, muna shawartarka da ka yi amfani da sama da bayanan shiga ɗaya tare da asusun HealthVault ɗinka. Micorosft ba ta bayar da shawara ko sarrafa, kuma ba ita ce da alhaki na sarrafawa, goyon baya, ko tsaro na wasu bayanan shiga waɗanda ba na Microsoft da ƙila kake amfani da su.
  • ii. Microsoft Band. Na’urar Microsoft Band da kuma manhajoji ba na'urorin lafiya ba ne kuma an yi niyya don maƙasudin kuzari da halin zama ne kawai. Ba a zana ko yi niyya a yi amfani da su cikin ganowa cuta ko sauran halaye ba, ko a warkarwa, ragewa, jiyya, ko hana cuta ba ko sauran wasu halaye. Microsoft ba ta da alhaki da duk wata shawara da ka yanke bisa la’akari da bayanin da ka karɓa daga Microsoft Band.
Cikakken rubutu
Kayayyakin DijitalKayayyakin Dijital14k_DigitalGoods
Taƙaitawa
 • k. Kayayyakin Dijital. Ta hanyar Microsoft Groove, Finafinai da TV na Microsoft, Wurin Adana da sauran sabis-sabis masu alaƙa da kuma na gaba, Microsoft yana iya ba ka damar samun, saurara, duba, ko karanta (yadda ya kasance) kiɗa, hotuna, bidiyo, rubutu, littattafai, wasanni, ko sauran kayayyaki ("Kayayyakin Dijital") da ƙila za ka iya samu a tsarin dijital. Kayayyakin Dijital don amfani na mutum, shaƙatawa mara kasuwanci ne kawai. Ka yarda ba za ka sake rarraba, watsar da, yi aiki ga jama'a ko nuna ga jama'a ko gusar da kowaɗane kwafe-kwafe na Kayayyakin Dijital ba. Ana iya mallaka Kayayyakin Dijital ta wajen Microsoft ko wasu. A dukan halaye, kana gane da kuma yarda da cewa haƙƙoƙinka dangane da Kayayyakin Dijital sun taƙaice ta waɗannan Sharuɗɗa, dokar haƙƙin mallaka, da dokokin amfani da suke samuwa a https://go.microsoft.com/fwlink/p/?LinkId=723143. Ka yarda cewa ba za ka yi ƙoƙarin gyaggyara kowaɗane Kayayyakin Dijital da aka samu ta hanyar kowane daga Sabis-sabis ɗin don wani irin dalili ba, da ya haɗa don maƙasudin sakewa kama ko canzawa mallaka ko tushen Kayayyakin Dijital ɗin. Microosft ko masu mallaka Kayayyakin Dijital suna iya, daga lokaci zuwa lokaci, cire Kayayyakin Dijital daga Sabis-sabis ɗin ba tare da sanarwa ba.
Cikakken rubutu
OneDriveOneDrive14l_OneDrive
Taƙaitawa
 • l. OneDrive.
  • i. Kasafin Wurin adana. Idan kana da ƙarin ƙunshiya da aka ajiye a cikin asusun OneDrive ɗinka fiye yadda aka samar maka a ƙarƙashin sharuɗɗan sabis na rajista na kyauta ko na biyan kuɗi ɗinka don OneDrive kuma ba ka ba da amsa ga sanarwa daga Microsoft don gyara asusunka ta cirewa rarar ƙunshiya ko matsarwa zuwa wani sabon tsarin rajista mai ƙarin wurin adana ba, mun riƙe haƙƙin rufewa asusunka da kuma share ko naƙasa iso ga zuwa Ƙunshiyarka a kan OneDrive.
  • ii. Yin aiki na Sabis. Dangane da halaye kamar na'urarka, haɗin intanet da kuma ƙoƙarin Microsoft don kula da yin aiki da mutuncin sabis ɗinsa, kana iya lokaci-lokaci ɗanɗana jinkiri wajen yin lodi ko daidaitawa ƙunshiya a kan OneDrive.
Cikakken rubutu
Microsoft RewardsMicrosoft Rewards14m_MicrosoftRewards
Taƙaitawa
 • m. Microsoft Rewards.
  • i. Program. Sakayyar Microsoft ("Shirin") yana ba ka damar samun maki na karɓa don ayyuka, kamar su bincike da ya cancanta, samu, lokaci da aka kashe wajen burauzi da Microsoft edge, da kuma sauran taye-taye daga Microsoft. Tayin zai iya bambanta daga kasuwa zuwa kasuwa. Bincike wani aiki ne da ɗaiɗaikun masu amfani suke shigar da rubutu da niyya mai kyau don samun sakamakon binciken Bing na niyyar binciken mai amfani kuma bai haɗa da duk wasu tambayoyi da bot ya shigar ba, makro, ko sauran hanyoyi na zama masu aiki da kansu ko wasu iri ("Bincike"). Samu wata hanya ce ta sayen kayayyaki ko saukewa da kuma samun lasisi na ƙunshiyar dijital daga Microsoft, ko a kyauta ko kuwa ta biyan kuɗi ("Samu"). Ba a samar da makin Sakayya ga kowace sayayya daga Microsoft. Yin bincike da Microsoft Edge akai-akai yana nufin buraucer ake kallo a kan allon na’urarka (misali, buɗewa da kuma amfani kamar haskaka alamar Microsoft Egde a baa na aiki, da yake nuna cewa ana amfani da manhajar a yanzu), da kuma yin burauzi don duba shafukan yanar gizo, kallon bidiyoyi a cikin burauzar, bincika imel, da kuma sauran amfani waɗanda ake yi da burauza. Don samun ƙarin maki ta amfani da Microsoft Edge, dole ne a Saita Bing a zaman burauzar nema ta asali kuma dole ne a ƙyale ma’auni kunne a cikin saitunan Windows ɗinka. Microsoft za ta iya samar da ƙarin dama ta samun maka daga lokaci zuwa lokaci, kuma kowane tayi na samun-maki ba zai ci gaba da samuwa ba din-din-din. Za ka yi amfani da makin da ka samu don karɓar abubuwa ("Sakayya") a cikin shafin karɓa. Don ƙarin bayani ga sashen Sakayya a support.microsoft.com ("Tambayoyi da aka Fiya yi").
   • 1. Buƙatun Shirin. Kana buƙatar wani asusun Microosft mai aiki kuma dole na’urori su cim ma ƙarancin buƙatun na’ura. Shirin yana samuwa ga masu amfani waɗanda suke zaune a cikin kasuwanni da aka jera a ɓangare Tambayoyi da aka Fiya yi. Ɗaiɗaikun mutane ba za su mallaki sama da asusun Shiri ɗaya ba, ko da kuwa ɗaiɗaikun mutane suna da ninkin adiresoshin imel, kuma ba a wuce adadin asusu guda shida a gida. An samar da Shirin ne kawai don amfanin kai amma ba na kasuwanci ba.
   • 2. Maki. Sai dai kawai idan kana bayar da tallafin makinka ga wata ƙungiyar agaji da aka jera a cibiyar karɓa, ba za ka iya tura makinka. Makin ba mallakinka ba ne, kuma ba za ka iya samun tsabar kuɗi ko kuɗi ta hanyar musayarsu ba. Ana samar maka da makin sakayya ne ta hanyar bayarwa. Ba za ka iya sayen makin ba. Microsoft za ta iya taƙaita yawan makin ko Sakayya ga mutum ɗaya, gida, ko a wani wa’adin lokaci (misalai, a rana). Za ka iya karɓar fiye da maki 550,000 a shekara a cikin Shirin. Makin da aka samu a cikin Shirin ba sa aiki, kuma ƙila ba za a yi amfani da su da wasu tare da, ko ta wani shiri da Microsoft ko wasu suke samarwa ba. Makin da ba a karɓa suna lalacewa idan ba ka samu ko karɓi duk wasu maki cikin watanni 18 ba.
   • 3. Saka wa. Za ka iya karɓar makinka ta ziyartar cibiyar karɓa ko ka taimaka da maki zuwa wata ƙungiyar agaji da aka jera. Ta yiwu akwai wa’adi na adadin wata keɓaɓɓiyar Saka wa da take samuwa, kuma za a isar ga waɗannan Saka wa ga waɗanda suka fara zuwa, wato ta hanyar waɗanda suka fara zuwa. Ƙila a buƙaci ka samar da ƙarin bayani kamar adireshin wasiƙarka da kuma wata lambar tarho (ƙari ga lambar VOIP ko kira kyauta), kuma ƙila a umarce da ka shigar da lambar hana-zamba ko ƙarin takardun doka don karɓar maki na Sakayya. Da zarar ka yi odar wata Sakayya, ba za ka iya soke ta ko dawo da ita ba don ramuwar makin face sai idan samfurorin suna da matsala ko kamar yadda dokar da ta shafa ta samar. Idan ka yi odar wata Sakayya da babu ita a ƙasa ko ba ta samuwa bisa wasu dalilai ta ɓangaren Microsoft bisa ganin damarta, ƙila mu iya musanya Sakayyar da wata Sakayya mai daraja makamanciyar ta makin ramuwar. Microsoft za ta iya sabunta Sakayya da ta samar a cibiyar karɓa ko ƙin ci gaba da samar da wasu keɓaɓɓun Sakayya. Wasu Sakayyar ta yiwu suna da buƙatar cancanta ta shekaru. Za a saka waɗannan buƙatu a cikin tayin da suke da alaƙa. Kai ke da alhaki ga duk haraji na tarayya, jiha da kuma na gida da kuma sauran biyan kuɗi na karɓa da kuma amfani da Sakayya. Za a aika Saka wa ta hanyar adireshin imel da ka samar ba a yayin odar Saka wa, saboda haka sa imel ɗinka ya kasance yana aiki. Ba za a sake samar da Sakayya da ba a isar ba kuma za a ƙwace su. Ba a sake sayar da Sakayya
   • 4. Soke Shigarka Cikin Shirin. Za a soke asusun Shirinka idan ba ka shiga aƙalla sau ɗaya a cikin watanni 18 ba. Bugu da ƙari, Microsoft tana da iko na soke asusun Shirin na wani keɓaɓɓen mai amfani saboda ɓata shi, cin zarafinsa ko yi wa Shirin zamba, ko keta waɗannan Sharuɗɗa. Da zarar an soke Shirin (kai ko mu) ko idan an dakatar da Shirin, za ka sami kwanaki 90 na karɓar makinka; idan ba haka ba, za a ƙwace waɗannan maki. Duk wasu sokewa, hakkinka ne na amfani da Shirin da kuma samun maki na gaba zai ƙare.
   • 5. Sauran Sharuɗɗa. Microsoft tana da iko na fitar da kai; hana samun isonka ga Shiri ko asusun Saka wa ɗinka; kuma/ko riƙe mako, Sakayya da kuma tallafin taimako, idan Microsoft ta yi imani kana wasa ko keta dokar duk wani ɓangare na Shirin ko ta yiwu kana yin wasu ayyuka da suke keta waɗannan Sharuɗɗa.
Cikakken rubutu
Sauran abubuwaSauran abubuwa16_17_18_miscellaneous
Taƙaitawa

14. Sauran abubuwa. Wannan sashe, da kuma sassa na 1, 9 (ga kuɗi wanda ya shiga kafin ƙarewar waɗannan Sharuɗɗa), 10, 11, 12, 15, 17 da kuma waɗanda sharuɗɗansu aka sanya bayan waɗannan Sharuɗɗa sun ƙare, duk wata ƙarewa ko soke waɗannan Sharuɗɗa ba ta shafar su. Har iyakanci da dokar da take shafa take yarda da, ya yiwu mu sanya waɗannan Sharuɗɗa, yi wa wajibcinmu ƙaramar kwangila a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa, ko yi wa hakkinmu ƙaramin lasisi na waɗannan Sharuɗɗa, gaba ɗaya ko wani ɓangare, a kowane lokaci ba tare da sanar maka ba. Ƙila ba za mu saka waɗannan Sharuɗɗa ko tura su zuwa wasu hakkoki don amfani da Sabis-sabis ɗin ba. Wannan ce ɗaukacin yarjejeniya tsakaninka da Microosft don amfani da Sabis-sabis ɗin. Wannan ya soke duk wata yarjejeniya ta baya tsakaninka da Microsoft da suka shafi amfani da Sabis-sabis ɗin da kake yi. Wajen shiga waɗannan Sharuɗɗa, ba ka dogara kan duk wani jawali, wakilci, garanti, fahimta, aiwatarwa, alƙawari ko tabbbaci fiye da waɗanda aka bayyana a cikin waɗannan Sharuɗɗa ba. An sanya duk sassa na waɗannan Sharuɗɗa zuwa iyakar da dokar da ta shafa ta ƙyale. Idan kotu ko wani alƙali ya ce ba za mu tilasta wani sashe na waɗannan Sharuɗɗa kamar yadda aka rubuta ba, ƙila mu iya musanya waɗannan sharuɗɗa tare da wasu sharuɗɗa masu kama zuwa iyakar tilastawa a ƙarƙashin dakar da ta shafa, amma ba za a sauya ragowar waɗannan Sharuɗɗa ba. Waɗannan Sharuɗɗa ne dominka da kuma alfanunmu. Waɗannan Sharuɗɗa ba alfanun sauran mutane ba ne, sai ga magada da kuma waɗannan Microosft ta sa. Kanun sashe don ddubawa ne kawai amma ba su da sakamako na shari’a.

15. Dole ne a Miƙa Ƙorafe-Ƙorafe Cikin Shekara Ɗaya. Duk wani ƙorafi da ya shafi waɗannan Sharuɗɗa dole ne a miƙa shi a cikin kotu (ko alƙali idan an sanya sashe na 10(d)) cikin shekara guda daga ranar da za a fara miƙa ƙorafin, sai dai idan dokar ƙasarka ta buƙaci lokaci mai tsawo don miƙa ƙorafe-ƙorafe. Idan ba a miƙa cikin wannan lokaci ba, za a hana shi dindindin.

16. Dokokin Fitarwa. Dole ne ka bi duk dokokin gida da na waje na fitar kayayyaki ƙasashen waje da suka shafi manhajar da kuma/ko Sabis-sabis, wanda ya haɗa amma ba da iyakancewa ba da ƙasashe, masu amfani, da kuma nau’in amfani. Domin ƙarin bayani da kan taƙaitawa na wurare da kuma fitar da kaya, ziyarci https://go.microsoft.com/fwlink/?linkid=868968 and https://www.microsoft.com/exporting.

17. Keɓe Hakkoki da kuma Martani. Sai dai inda aka bayyana a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa, amma Microsoft ba ta baka wani lasisi ko duk wasu sauran hakkoki ko wasu iri a ƙarƙashin kowace lambar ƙira, yadda-ake, hakkin mallaka, sirrin kasuwanci, alamomin kasuwanci ko sauran hakkoki na ilimi mallakin Microsoft ko wanda take sarrafawa ko duk wani abu mai alaƙa, da ya haɗa amma ban da iyakancewa ga duk wani suna, alamar kasuwanci, tambari ko madadinsu. Idan ka ba wa Microsoft wata dabara, ƙuduri, shawara, ko wani martani, da ya haɗa, amma ban da iyakancewa ga dabaru na sababbin samfurori, kimiyya, talla, sunayen samfuri, martanin samfuri da kuma haɓaka samfuri ("Martani"), ka ba wa Microsoft, ba tare da wani biyan kuɗi ba, kuɗin shiga ko tilastawa gare ka ba, hakki na yi, samarwa, ayyukan kwaikwayon ƙirƙira, amfani, rabawa da kuma kasuwancin Martaninka ta kowace hanya da kuma kowane dalili. Ba za ka bayar da Martani da ya shafi wani lasisi da yake buƙatar Microsoft ta bayar da lasisin manhajarsa, fasaha ko daftarori ga wasu saboda Microsoft ta haɗa Martaninka a cikinsu.

Cikakken rubutu
SANARWASANARWANOTICES
Taƙaitawa

Sanarwa da hanyoyin ƙorafi kan keta hakkin mallakar ilimi. Microsoft tana mutunta hakkokin mallakar ilimi na wasu. Idan kana son aika sanarwa kan keta hakkin mallaka, da ya haɗa da koke-koke kan keta hakkin mallaka, yi amfani da hanyoyinmu na miƙa Sanarwar Keta Doka. AMSA KAWAI DA SHAFI WANNAN TAMBAYA ZA A SAMU.

Microsoft yana amfani da hanyoyi da aka gindaya a cikin Take na 17, United States Code, Sashe na 512 don bayar da amsa kan sanarwa game da keta hakkin mallaka. A lokuta da suka dace, ƙila Microsoft ta hana ko ƙare asusu-asusu na masu-aiki da ayyukan Microsoft waɗanda ƙila suka sake maimaita keta doka.

Sanarwa da kuma hanyoyi da suka shafi damuwa kan hakkin mallakar ilili a cikin talla. A yi bitar Jagororin Hakkin Mallakar Ilimi namu da suka shafin damuwa kan hakkin mallakar ilimi a kan hanyar sadarwarmu ta talla.

Sanarwar hakkin mallaka da alamar kasuwanci. Sabis-sabis ne masu hakkin mallaka © 2018 Microsoft Corporation and/or its suppliers, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. An tanadi duk hakkoki. Microsoft da sunayen, tambarori, da duk alamomin kayayyakin Microsoft, manhajoji, da kuma hidimomi za su iya kasancewa alamomin kasuwanci ko alamomin kasuwanci masu rajista na Microsoft a cikin ƙasar Amurka da kuma/ko sauran ƙasashe. Ainihin sunayen kamfanonin da kuma samfurori za su iya kasancewa su alamomin kasuwanci na masu su. Duk hakkoki da ba a bayyana a cikin waɗannan Sharuɗɗa ba an tanade su. Wani amfani da manhaja a cikin wasu sabobin yanar gizo na Moicrosoft ya dogara ne a cikin wani ɓangare na aikin Independent JPEG Group. Hakkin mallaka © 1991-1996 Thomas G. Lane. An tanadi duk hakkoki. Manhajar “gnuplot” da ake amfani da ita a wasu sabobin shafukan yanar gizon Microsoft© 1986‑1993 Thomas Williams, Colin Kelley. An tanadi duk hakkoki.

Sanarwa kan lafiya. Microsoft ba ya bayar da shawara kan lafiya, bincika lafiya ko samun magani. Nemi shawarar likita ko wani mai kula da lafiya ga duk wasu tambayoyi da suka shafi lafiya, abinci mai sa lafiya ko shiri mai ƙara lafiya. Kada a taɓa yin sakaci ko jinkiri da ƙwararriyar shawara kan lafiya wajen nemanta saboda bayanin da ka sami iso gare shi ko ta hanyar Sabis-sabis ɗin.

Ambaton haja da kuma bayanan fihirisa (da ya haɗa da darajojin fihirisa). © 2013 Morningstar, Inc. An tanadi duk hakkoki. Bayanin da yake ƙunshe a cikin nan: (1) mallakar Morningstar ne kuma/ko masu samar masa da ƙunshiya; (2) ƙila ba za a iya kwafi ko rarrabawa ba; kuma (3) kuma ba a bayar da tabbacin ya zama daidai ba, ko cikakke cikin lokaci ba. Morningstar ko masu samar masa da ƙunshiya ba su da alhaki na duk wata lalacewa ko asara da ta taso sanadiyyar amfani da wannan bayani. Ƙoƙari na baya ba ya bayar da tabbacin sakamako na gaba.

Ƙila ba za ka iya amfani da ɗaya daga cikin Fihirisoshin Dow Jones baSM, bayanan fihirisa, ko makin Dow Jones ba da suka shafi samarwa, ƙirƙiri, ɗaukar nauyi, kasuwanci, tallar wasu samfurorin sha’anin kuɗi ko samfurorin zuba jari (misali, sakamako, tsararrun samfurori, kuɗin zuba jari, kuɗin musayar kuɗi, wuraren zuba jari, da sauransu, inda farashi, riba da kuma /ko ƙarfin aikin hanyar ko zuba jarin ko tushen zuba hannun jarin, wanda ya shafi, ko niyyar bin-sawun wasu Fihirisoshi ko wakilci ga ɗaya daga cikin Fihirisoshin) ba tare da keɓaɓɓiyar rubutacciyar yarjejeniya tare da Dow Jones ba.

Sanarwar sha’anin kuɗi. Microsoft ba dillali ba ne/dila ko wani mai bayar da shawara kan hannun jari da aka yi wa rajista a ƙarƙashin dokokin kadarori na Amurka ko sauran dokoki kan kadarori, kuma ba ta ba ya ba wa ɗaiɗaikun mutane shawara kan zuba hannun jari, saye, ko sayar da kadarori ko sauran samfuroin sha’anin kuɗi ko sabis-sabis. Ba wani abu a cikin Sabis-sabis ɗin da yake tallata ko jan hankali kan sayen wata kadara ba. Microsoft ko masu samar da ambaton haja ko bayanan fihirisa ba su shawarta ko yabawa ga wani keɓaɓɓun samfurori na harkokin kuɗin ba. Ba wani abu a cikin Sabis-sabis ɗin da aka yi niyyar ya zama ƙwararriyar shawara, da ya haɗa ba tare da iyakancewa ba, zuba jari ko shawara kan haraji.

Sanarwa game da H.264/AVC, MPEG-4 Visual, da kuma VC-1 Video Standards. Ƙila manhajar ta haɗa da H.264/AVC, MPEG-4 Visual da kuma/ko kimiyyar VC-1 codec da ƙila MPEG LA, L.L.C. ta bayar da lasisi. Wannan kimiyya ce ta tsara matse bayanai na bayanin bidiyo. MPEG LA, L.L.C. yana buƙatar wannan sanarwa:

AN SAMAR DA WANNAN SAMFURI NE A ƘARƘASIN LASISI H.264/AVC, MPEG-4 VISUAL, DA KUMA VC-1 SHAIDAR LASISIN KAYA DON KEƁAƁƁEN AMFANI DA KUMA AMFANI DA BA NA KASUWANCI BA ZUWA (A) ENCODE VIDEO BISA DACEWA DA INGANCI ("VIDEO STANDARDS") DA KUMA/KO (B) DECODE H.264/AVC, MPEG-4 VISUAL, DA KUMA VC-1 VIDEO WANDA AKA JUYA GA MAI KEƁAƁƁEN AMFANI KO AMFANI WANDA BA NA KASUWANCI BA DA KUMA/KO AKA SAMU DAGA LASISIN MAI SAMAR DA BIDIYO DON SAMAR DA WANNAN BIDIYO. BABU ƊAYA DAGA CIKIN LASISAN DA ZA A FAƊAƊA ZUWA WANI SAMFURI KO DA AN HAƊA WANNAN SAMFURI TARE DA MANHAJAR A CIKIN WATA MAƘALA GUDA. BA LASISI DA ZA A BAYAR KO ZA A SANYA DON WANI AMFANI DABAN. ƘILA ZA A IYA SAMUN ƘARIN BAYANI DAGA MPEG LA, L.L.C. DUBA SHAFIN YANAR GIZON MPEG LA.

Don dalili na tabbatarwa kawai, wannan sanarwa ba ta taƙaita ko tilasta amfani da manhajar da aka samar a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa don amfanin kasuwanci na daidai da yake amfani da wannan da ya keɓanta gare shi wanda bai haɗa da (i) sake rarraba softwaya ɗin ga wasu ba, ko (ii) ƙirƙirar kayayyaki ta bin kimiyyyar VIDEO STANDARDS don rarrabawa ga wasu ba.

Cikakken rubutu
SHARUƊƊAN DAIDAITACCEN LASISIN MANHAJASHARUƊƊAN DAIDAITACCEN LASISIN MANHAJASTANDARDAPPLICATIONLICENSETERMS
Taƙaitawa

SHARUƊƊAN DAIDAITACCEN LASISIN MANHAJA

WURIN ADANA NA MICROSOFT, WURIN ADANA NA WINDOWS, DA KUMA WURIN ADANA NA XBOX

Waɗannan sharuɗɗan lasisi wata yarjejeniya ce tsakaninka da kuma mawallafin manhajar. Sun shafi manhajojin sofwaya da ka sauke daga Wurin Adana na Microsoft, Wurin Adana na Windows ko Wurin Adana na Xbos (wanda kowanne ake nuni da shi a cikin waɗannan sharuɗɗan lasisi a zaman "Wurin Adana"), da ya haɗa da duk wani sabuntawa ko ƙari ga wannan manhaja, sai dai idan manhajar ta zo da keɓaɓɓun sharuɗɗa, inda a wannan hali ake sanya waɗannan sharuɗɗa.

TA SAUKE KO AMFANI DA MANHAJAR, KO ƘOƘARIN YIN ƊAYA DAGA WAƊANNAN, KA AMINCE DA WAƊANNAN SHARUƊƊAN. IDAN BA KA AMINCE DA SU BA, BA KA DA WANI HAKKI KUMA DOLE NE BA ZA KA SAUKE KO AMFANI DA MANHAJAR BA.

Mawallafin manhajar yana nufin wanda yake baka manhajar lasisin, kamar yadda aka gano a Wurin Adana.

Idan ka bi waɗannan sharuɗɗan lasisi, kana hakkokin da suke ƙasa.

 • 1. HAKKOKIN SA WA DA KUMA AMFANI; LALACEWA. Za ka iya saka da kuma amfani da manhajar a kan na’urorin Windows ko Xbox consoles kamar yadda aka bayya a cikin Dokokin Amfani na Microsoft. Microsoft tana da iko na gyara Dokokin Amfani na Microsoft a kowane lokaci.
 • 2. AYYUKA DA SUKA SHAFI INTANET.
  • a. Amincewa da ayyuka da suka shafi Intanet ko haɗi ta hanyar iska. Idan manhajar tana haɗi da sistem na kwamfuta ta hanyar Intanet, wanda ƙila zai iya haɗawa ta hanyar sadarwar iska, ta amfani da manhajar yana aiki kamar yadda ka amince don watsa daidaitaccen bayanin na’ura (da ya haɗa amma ban da iyakancewa da bayani game da na’urarka, sistem da kuma softwayar manhajar, da kuma sauran kayan haɗi) ga sabis da suka shafi Intanet ko haɗin ta hanyar iska. Idan an gabatar da sauran sharuɗɗa da suka shafi amfani da sabis-sabis da ka sami iso gare su ta hanyar amfani da manhajar, haka nan an sanya waɗannan sharuɗɗa.
  • b. Rashin Amfani da Ayyuka Masu Aiki-da-Intanet Yadda ya Dace. Ƙila ba za ka yi amfani da sabis da ya shafi Intanet ba ta kowace hanya da za ta cutar da shi ko katse amfanin wani ko cibiyar sadarwar marar wayar. Ƙila ba za ka iya amfani da sabis ɗin ba wajen ƙoƙarin samun iso ga wani sabis, bayanai, asusu, ko hanyar sadarwa ta kowace hanya ba.
 • 3. FAƊIN LASISI. Aikace-aikacen yana da lasisi, ba a sayar ba. Wannan yarjejeniya kawai tana ba ka wasu hakkoki ne na amfani da aikace-aikacen. Idan Microsoft ta hana dama ta amfani da aikace-aikacen a kan na´urarka bisa yarjejeniya tare da Microsoft, duk wani lasisi da ya shafa zai ƙare. Mawallafin manhajar ke riƙe da duk iko. Sai dai idan dokar da ta shafa ta ba ka ƙarin hakkoki duk da wannan iyakancewa, ƙila ka iya amfani da manhaja kawai kamar yadda aka ƙyale a bayyane a cikin wannan yarjejeniya. A wajen aikata haka, dole ne ka bi duk wasu iyakoki na na´ura a cikin manhaja da kawai yake ƙyale ka ka yi amfani da shi cikin wasu hanyoyi. Ƙila ba za ka iya:
  • a. Aiki a kusa da duk inda aka yi wa taƙaitawar sana’a a cikin manhajar.
  • b. Juya kimiyya, sake haɗa manhajar, banda kawai yadda doka ta tanada a rubuce, duk da wannan iyakancewa.
  • c. Samar da kwafin manhajar sama da yadda aka ƙayyade a cikin wannan yarjejeniya ko da dokar da ta shafa ta ƙyale, duk da wannan iyakancewa.
  • d. Wallafa ko kuma samar da kwafin manhajar ga wasu mutane don yin kwafi.
  • e. Haya, ba da haya, ko aron manhajar.
  • f. Tura manhaja ko wannan yarjejeniya zuwa ga wasu.
 • 4. ADANA DAFTARI. Idan an samar da manhajar tare da daftari, ƙila za ka iya kwafi da kuma amfani da daftarin don dalilai na amfaninka.
 • 5. TAƘAITAWAR KIMIYYA DA KUMA FITARWA. Manhajar ƙila ta zama a ƙarƙashin Amurka ko kulawar kmiyyar ƙasar waje ta Amurka ko dokokin fitarwa. Dole ne ka bi duk dokoki da ƙa’idoji na gida da na waje da suka shafi kimiyya da aka yi amfani da ita ko manhajar take goyon baya. Waɗannan dokoki sun haɗa da taƙaitawa a kan wuraren kaiwa, masu amfani da kuma ƙarshen amfani. Domin ƙarin bayani kan sababbin samfurorin Microsoft, tafi zuwa shafin fitar da kayayyaki na Microsoft.
 • 6. AYYUKAN GOYON BAYA. Tuntuɓi mawallafin manhajar don ƙayyade ayyukan goyon baya da suke akwai. Microsoft, maƙerin hadwaya ɗinka da kuma mai samar maka da sadarwa ta hanyar isa (sai dai idan ɗayansu shi ne mawallafin manhajar) ba su da hakki na samar da goyon baya kan sabis-sabis na manhajar.
 • 7. ƊAUKACIN YARJEJENIYA. Wannan yarjejeniya, kowace dokar tsare sirri da take shafa, kowaɗane ƙarin sharuɗɗa da suka bi manahajar, da kuma sharuɗɗan don ƙari da sabuntawan cikakkiyar yarjejeniyar lasisi ce tsakanin kai da mawallafin manahajar don manahajar.
 • 8. DOKA DA AKA SA.
  • a. Amurka da Canada Idan ka samu manhajar a Amurka ko Canada, dokar jiha ko lardin da kake zaune (idan wani kasuwanci, inda cibiyar kasuwanci take) yake da alhakin fassara wannan yarjejeniya da kuma ya shafi ƙorafe-ƙorafe na keta shi, da kuma duk sauran koke-koke (da suka haɗa da kariyar mai amfani, gasa ta rashin adalici, da kuma ƙorafi na doka) ba bisa la’akari da saɓani na doka ba.
  • b. Wajen Amurka da kuma Canada. Idan ka sami manhajar ne a wata ƙasa, dokokin wannan ƙasa za a sanya.
 • 9. SAKAMAKON SHARI’A. Wannan yarjejeniya ta bayyana wasu hakkoki ne na doka. Ƙila kana da sauran hakkoki a ƙarƙashin dokokin jiharka ko ƙasarka. Wannan yarjejeniya ba ta sauya hakkokinka a ƙarƙashin dokokin jiharka ko ƙasarka idan dokokin jiharka ko ƙasarka ba su ba da damar aikata haka ba.
 • 10. KASHEDIN GARANTI. An samar da lasisin manhaja “kamar yadda yake”, “tare da duk lahanoni” kamar “yadda yake samuwa”. Duk haɗari na amfani da shi ya rataya a wuyanka. Mawallafin mahajar, a madadin kansa, Microsoft (idan Microsoft ba shi ne mawallafin manhajar ba), masu samar da sadarwa ta hanyar iska waɗanda aka samar da manhajar ta hanyar sadarwarsu, da kuma kowane rassanmu, masu sayarwa, jami’a da kuma sararwa (“Waɗanda abin ya Shafa”), ba su bayar da wata yarjejeniya, garanti ko sharuɗɗa da suka shafi manhajar ba. Ɗaukacin haɗari ga ingancin, tsaro, jin daɗi, da ƙarfin aiki na manahajar yana a hannunka. Idan an tabbatar da buƙatar ba daidai ba ce, kai ke da alhakin biyan duk kuɗin da ya shafi sabis ko gyara. Ƙila kana da wasu ƙarin hakkoki na mai amfani da kaya a ƙarƙashin dokokin ƙasarka da wannnan yarjejeniya ba za ta iya canzawa ba. Har iyakanci da dokoki na gida ɗinka suke yarda da, Kulallen Wasu sun ware kowane warantoci ko halaya da suke shafa, da suka haɗa waɗannan na kasuwanci, dacewa don wani takamaiman maƙasudi, taro, jin daɗi da kuma rashin keta doka.
 • 11. IYAKA A KAN DA KUMA WARIYA NA MAGANCEWA DA KUMA LALACEWA. Zuwa ga iyakar da doka ba ta haramta ba, idan kana da wata hujja ta rashin ɗaukar asara, za ka iya dawo da kuɗi daga mawallafin manhajar kawai kai tsaye har zuwa adadn kuɗin da ka biya na manhajar ko $1.00, duk wanda ya fi yawa. Ba za ka iya, ko goge duk wani hakki, da ya nemi dawo da duk wasu lalacewa, da suka haɗa da lalacewa babba, rasa riba, lalacewa musmman, ko a kaikaice, lalaewar da ba ta gangan ba daga mawallafin manahajar. Idan dokokin ƙasarka sun tilasta yarjejeniya, garanti ko sharaɗi ko da waɗanann sharuɗɗa ba su yi ba, tsawon lokacinsa shi ne kwanaki 90 daga rana da ka sauke manhajar.

Wannan iyakancewa ta shafi:

 • Duk wani abu da ya shafi manhajar ko ayyukan da aka samar ta hanyar manhajar; da kuma
 • Koke-koke na keta dokar kwangila, keta dokar garanti, tabbaci ko sharaɗi; bashi mai tsanani, sakaci, ko wani laifi; keta doka ko ƙa’ida; azurtawa bisa rashin adalci; ko a ƙarƙashin duk wani irin dalili, duk zuwa iyakar da dokar da aka sanya ta ƙyale.

Haka nan ya shafi idan:

 • Abin da ake bayarwa ba ya biyan diyyar gaba ɗaya asarark; ko
 • Mawallafin manhajar ya sani ko yakamata ya san yiwuwar lalacewar.
Cikakken rubutu
Sabis-Sabis da ya HaɗeSabis-Sabis da ya Haɗeserviceslist
Taƙaitawa

Samfurorin da suke tafe, manhajiji da kuma sabis-sabis suna ƙarƙashin kulawar Yarjejeniyar Sabis na Microsoft, amma ƙila bza su samu a cikin kasuwarka ba.

 • Abinci da Abin Sha na Bing
 • Account.microsoft.com
 • Advertising.microsoft.com
 • Asusun Microsoft
 • Bin a Cikin Aji
 • Bing App for Android
 • Bing Bots
 • Bing Business Bot
 • Bing for Business
 • Bing Image and News (iOS)
 • Bing Search APIs/SDKs
 • Bing Sportscaster
 • Bing Translator
 • Bing Webmaster
 • Bing.com
 • Bing
 • Bingplaces.com
 • Bugawa ta MSN
 • Burauzar Bing Wikipedia
 • Citizen Next
 • Cortana skills by Microsoft
 • Cortana
 • Default Homepage and New Tab Page on Microsoft Edge
 • Destof na Bing
 • Dev Center App
 • Dictate
 • Docs.com
 • education.minecraft.net
 • Face Swap
 • Feedback Intake Tool for Azure Maps (aka “Azure Maps Feedback”)
 • Finafinai da TV na Microsoft
 • Forms.microsoft.com
 • forzamotorsport.net
 • Galarin Hoto na Windows
 • Groove Music Pass
 • Groove
 • GroupMe
 • Hasashen Yanayi na Bing
 • HealthVault
 • Hoton Bango na Microsoft
 • Iyali na Microsoft
 • Jerin Kayan Aiki na Bing
 • Kulle Allo na Gaba
 • Kulle Allon Picturesque
 • Kuɗi na Bing
 • Labarai na Bing
 • Lafiya da Kuzari na Bing
 • Lafiya ta Microsoft
 • LineBack
 • Maitaimakon Goyon baya da Samuwa Microsoft ga Office 365
 • Manajan Skype
 • Manhajar Lafiyar Na’ura
 • Manhajar Nema ta Bing
 • Manhajar Taswirori
 • Manhajoji na Bing
 • Ma’adanar Office
 • Microsoft Academic
 • Microsoft Add-Ins for Skype
 • Microsoft Bots
 • Microsoft Educator Community
 • Microsoft Pay
 • Microsoft Research Interactive Science
 • Microsoft Research Open Data
 • Microsoft Soundscape
 • Microsoft Translator
 • Microsoft XiaoIce
 • Mixer
 • MSN Explorer
 • MSN Lambawan
 • MSN.com
 • Nema mai Dabara
 • Office 365 Consumer
 • Office 365 Home
 • Office 365 Personal
 • Office 365 Pro Plus optional connected experiences
 • Office 365 University
 • Office don yanar gizo (da ake kira Office Online a baya)
 • Office Sway
 • Office.com
 • OneDrive.com
 • OneDrive
 • OneNote.com
 • Outlook.com
 • Paint 3D
 • Presentation Translator
 • Remix 3D
 • Rinna
 • rise4fun
 • Ruuh
 • Seeing AI
 • Send
 • Skype in the Classroom
 • Skype Interviews
 • Skype Qik
 • Skype.com
 • Skype
 • Snip Insights
 • Spreadsheet Keyboard
 • Sprinkles
 • Sway.com
 • Tafiya ta Bing
 • Taswirori na Bing
 • to-do.microsoft.com
 • Translator for Microsoft Edge
 • Translator Live
 • UrWeather
 • Video Breakdown
 • Visio Online
 • Wasanni na Bing
 • Wasannin, manhajojin da kuma shafukan yanar gizon Windows da Microsoft ta wallafa
 • Wasannin, manhajojin da kuma shafukan yanar gizon Xbox Game Studios
 • Web Translator
 • Who’s In
 • Windows Live Mail
 • Windows Live Writer
 • Windows Movie Maker
 • Wurin Adana Windows
 • Wurin adana
 • Xbox Game Pass
 • Xbox Live Gold
 • Xbox Live
 • Xbox Music
 • Xbox Store
 • Ƙamusu na Bing
Cikakken rubutu
Maris 1, 20180