SHARUƊƊAN SAYARWA NA MICROSOFT

An Sabunta a Fabrairu 2017

Maraba ga Wurin Adana na kan layi da masu saye daidai na Microsoft. "Wurin Adana" yana nufin wurare kan layi da kuma wurin masu saye ɗaiɗai da yake ba ka damar burauzi, duba, samu, saye, da kuma kimanta da bitar kayayyaki da kuma sabis-sabis da suka haɗa da na’urori, na’urorin wasa, ƙunshiyar dijital, manhajoji, wasanni, sabis-sabis, da makamantansu. Waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa ("Sharuɗɗan Sayarwa") sun shafi amfani da Wurin Adana na Microsoft, Wurin Adana Xbox, Wurin Adana Windows, da kuma sauran sabis-sabsi na Microsoft da suka shafi waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa (a tattare "Wurin Adana"). Ta hanyar Wurin Adana, Microsoft tana samar da samun dama ga mabambantan albarkatu, da suka haɗa da yankunan saukewa, manhaja, kayayyaki, da kuma bayani game da manhaja, sabis-sabis da kuma sauran kayayyaki ( a tattare "Sabis-sabis" da kuma a tare tare da Wurin Adana, "Wurin Adana"). Mafi yawan kayayyaki, sabis-sabis da kuma ƙunshiya da aka samar a cikin Wurin Adana kayayyakin wasu ne waɗanda suka samar sama da Microsoft. Ta amfani da Wurin Adana, ko ta sayen samfurori da kuma sabis-sabis aga Wurin Adana, ka amince kuma ka yarda da waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa, Jumlar Asiri ta Microosft (duba sashen Sirri da Kariyar Keɓaɓɓen Bayani da suke ƙasa), da kuma sharuɗɗa da ƙa’idoji da aka gindaya, dokoki ko zare hannu da aka samu a cikin Wurin Adana ko nuna da waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa (a tattare "Dokokin Wurin Adana"). Muna shawartarka da ka karanta Dokokin Wurin Adana a tsanake. TA YIWU BA ZA KA IYA AMFANI DA WURIN ADANA BA KO SABIS-SABIS IDAN BA KA YARDA DA DOKOKIN WURIN ADANA BA.

Idan muna da wani Wurin Adana Microsoft na ɗaiɗaiku a ƙasarka ko yanki, ƙila yana da dokoki daban ko ƙarin dokoki. Micoroft ƙila za ta iya sabunta ko gyara duk wasu dokoki a kowane lokaci ba tare da sanarwa ba.

Sharuɗɗa da Suka Shafin Amfaninka da Wurin Adana

1. Asusun Mambobi. Idan Wurin Adana yana buƙatar ka buɗe wani asusu, dole ne ka kammala aiwatar da rajistar ta samar mana da sabon bayani, cikakke da fam ɗin ya buƙata. Haka nan ƙila a buƙaci ka yarda da wata yarjejeniya ko keɓaɓɓun sharuɗɗan amfani a zaman wata ƙa’ida ta buɗe asusun. Amfani da kake da asusun don samun iso ga Wurin Adana da kuma ƙunshiya da ka buƙata daga Wurin Adana yana ƙarƙashin duk sharuɗɗan da suke kan asusun Microsoft. Don ƙarin bayani, duba Yarjejeniyar Sabis na Microsoft. Ki ke da alhaki na ajiye bayanin asusunka da kalmar sirri a asirce kuma kai ke da alhaki na duk wani aiki da ya faru a cikin asusunka.

2. No Unlawful or Prohibited Use. A zaman wani sharaɗi na amfani da kake yi da Wurin Adana da Sabis-sabis, ka ba mu yarjejeniyar cewa ba za ka yi amfani da Wurin Adana ga kowane irin dalili da aka haramta ko waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa suka hana ba, dokokin Wurin Adana, ko duk wasu sauran sharuɗɗa da aka sanya ga amfani da Wurin Adana da kake yi. Ƙila ba za ka yi amfani da Wurin Adana a cikin wani yanayi da zai iya lalata, hana, aiki fiye da ƙima, ko ɓata duk wata sabar Microsoft, ko hanyar(hanyoyin) sadarwa da aka haɗa da sabar Microsoft, ko katsewa tare da amfanin wasu da kuma jin daɗin Wurin Adana ba. Ƙila ba za ka yi ƙoƙarin samun iso marar izini zuwa ga Wurin Adana, sauran asusu-asusu, na’urorin kwamfuta ko hanyoyin sadarwa da aka haɗa kowace sabar Microsoft ko Wurin Adana, ta hanyar satar bayanai, kwaiwayon kalmar sirri ko kuma ma ta kawace irin hanya ba. Ƙila ba za ka iya samu ko ƙoƙarin samun wasu kayayyaki ko bayani ta kowane irin hanya ba a samar da ita da niyya ba ta hanyar Wurin Adana ba. Ƙila ba za ka iya amfani da Wurin Adana ta kowane hanya da ta keta hakkokin wasu ba, da suka haɗa da cutar da wani ko wani abu da gangan, da ya haɗa da Microsoft ba. Ƙila ba za rarrabawa ta hanyar kasuwanci, wallafa, ko sayar da duk wasu kayayyaki, bayani ko sabis-sabis da ka samu daga Wurin Adaba ba.

3. Kayayyaki da ka Samar ga Microsoft ko ka Buga a Wurin Adana. Microsoft ba ta iƙirarin mallakar kayayyaki da ka samar ga Microsoft (da suka haɗa da martani, kimantawa, bitoci da kuma shawarwari) ko ka buga, loda, shigar ko miƙa zuwa Wurin Adana ko sabis-sabis da suka shafi Microsoft don bita daga wasu (kowane "Miƙawa" da kuma a tattare "Miƙawa"). Kodayake, ka ba wa Microsoft wani iko, marar ƙarewa, mara warwarewa, a duniya gaba ɗaya, wanda ba a raba da wasu ba kuma hakki wanda ba za a iya ƙaramin lasisi ba don amfani, kwaskwari,a, kwafi, sake samarwa, ƙirƙirar ta kwaikwayo, fassara, gyara, aiwatar, rarraba, da kuma nuna Miƙawarka da ta haɗa da sunanka a kowace kafar sadarwa. Idan ka wallafa Miƙawarka a yankunan Wurin Adana a inda yake samuwa da faɗi a kan layi ba tare da ƙayyadewa ba, ƙila Miƙawarka ta bayyana a cikin kayayyakin gwaji ko waɗanda suke ciyar da Wurin Adana gaba ko kuma/ko kayayyako, sabis-sabis da kuma ƙunshiya da aka samar a cikin Wurin Adana. Ka bayar da tabbaci da kuma wakilci cewa kana da (kuma za ka samu) duk hakkoki na wajibi don samar da kowace Miƙawa da ka samar kuma ka bayar da waɗannan hakkoki zuwa Microsoft.

Babu wata diyya da za a iya dangane da amfani da Miƙawarka. Ba wani wajibci da zai sa Microosft za ta buga da kuma amfani da duk wata Miƙawa kuma Microsoft za ta iya cire kowane Miƙawa a kowane lokaci bisa ganin damanta. Microsott ba ta ɗukar alhaki ko nauyi na Miƙawarka ko kayayyakin da wasu suka buga, loda, shigar ko miƙawa ta amfani da Wurin Adana.

Idan ka kimanta ko bitar wata manhaja a cikin Wurin Adana, ƙila ka sami wani imel daga Microsoft wanda ke ɗauke da ƙunshiya daga mawallafin manhajar.

4. Hanyoyi zuwa Shafukan Yanar Gizo na Wasu. Ƙila Wurin Adana ya haɗa da hanyoyin shafukan yanar gizo na wasu da su sa ka bar Wurin Adana. Waɗannan hanyoyi ba sa ƙarƙashin kulawar Microsofy kuma Microsoft ba ta da alhaki na duk wata ƙunshiya na duk wani shafi da aka haɗa ko duk wani abu da shafin da aka haɗa ya ƙunsa. Microsoft tana samar da waɗannan hanyoyi ne gare ka kawai don dacewa, kuma saka dik wata hanya ba yana nufin Microsoft tana goyon bayan shafin ba. Amfaninka da shafin yanar gizon na wasu ƙila ya zama a ƙarƙashin sharuɗɗa da ƙa’idoji na wasun.

Sharuɗɗa da Suka Shafi Sayar da Kayayyaki DA KUMA SABIS-SABIS gare ka

5. Samuwa Bisa La’akari da Wuri. Samuwar kayyayaki da sabis-sabis ƙila su bamabanta dangane da yankinka ko na’ura. Ƙari ga wannan, akwai wasu iyakoki a kan inda za mu kai kayayyakin kamar yadda aka bayyana a cikin dokokinmu na kai kaya. Don kammala sayayyarka, ƙila ka buƙaci wani adireshin kai kaya mai inganci kuma adireshin ya kasanci cikin ƙasar ko yankin da Wurin Adana da ka yi sayayyar yake.

6. Masu Amfani Kawai. Dole ne ka kasance wani mai amfani don sayen kayayyaki da kuma sabis-sabis daga Wurin Adana. Ba a ƙyale ‘yan sari su saya.

7. Iyakokin Fitarwa. Kayayyaki da sabis-sabis da aka saya daga Wurin Adana ƙila su kasance ƙarƙashin dokokin jami’an kwastan da kuma dokokin kula da fitarwa. Ka yarda ka bi duk wasu dokoki da ƙa’idojin ƙasa-da-ƙasa da kuma na ƙasa.

8. Biyan kuɗi. Ta samarwa da Microsoft wata hanyar biyan kuɗi, ka: (i) bayyana cewa ka ba da izini na amfani da hanyar biyan kuɗin da ka samar kuma cewa duk wani bayani na biyan kuɗin da ka samar gaskiya ne kuma daidai ne; (ii) ka ba wa Microsoft izini na cajin ayyuka, sabis-sabis ko ƙunshiya mai samuwa ta amfani da hanyar biyan kuɗinka; kuma (iii) ka ba wa Microsoft izini na cajin duk wata siffar Wurin Adana ɗin ta biya da ka zaɓa ka yi rajista ko amfani. Ka yarda ka riƙa sabunta asusunka da kuma sauran bayanai akai-akai, da suka haɗa da adireshin imel ɗinka da kuma lambobin katin bashi da lokacin ƙarewa, saboda mu iya kammala hadahadar da kuma tuntuɓarka idan da buƙatar hakan dagane da hadahadar. Ƙila mu iya cajinka (a) tun kafin lokaci; (b) a lokacin sayayya; (c) jim kaɗan bayan sayayya; ko (d) a wasu lokuta na sake aukuwar rajistoci. Haka nan, ƙila mu caje ka har zuwa iyakar kuɗin da ka amince, kuma za mu sanar da kai kafin lokacin bisa la’akari da sharuɗɗan rajistarka na kowane sauyi a cikin adadin kuɗin da za a caje na rajistoci masu sake aukuwa. Ƙila mu caje ba a lokaci guda na sama da ɗaya daga cikin lokutanka da ka fi so na biyan kuɗi na adadin kuɗin ba a riga an aiwatar a baya ba. Ga bayanin Maimaita Biyan Kuɗi da ka da yake ƙasa.

Idan ana damawa da kai cikin wata garaɓasa ta gwaji, dole ne ka soke sabis ɗin a ƙarshen wa’adin gasar don gujewa sabon cajin kuɗi mai sake aukuwa, in ba haka ba, sai dai idan mun sanar da kai a’a. Idan ba ka soke sabis ɗin gwajin ba a ƙarashen wa’adin gwajin, ka ba mu damar cajinka hanyar biyan kuɗi ɗinka don samfurin ko sabis ɗin.

9. Maimaita Biyan Kuɗi. Idan ka sayi wani ayyuka, sabis-sabis ko ƙunshiya ta hanyar rajista (misali mako-mako, wata-wata, kowane watanni 3 ko shekara-shekara (yadda ya shafa)), ka amince kuma ka yarda cewa kana bayar ga izini da maimaita biyan kuɗi, da kuma biyan kuɗi za a yi ne ga Microsoft ta hanyar da ka zaɓa a tazarar maimaitawar da ka yarda da ita, har sai ka karar ko Microsoft ta ƙarar da rajistar ko idan ba haka ba bisa la’akari da sharuɗɗansa. Ta bayar da izinin maimaita biyan kuɗi, ka ba wa Microsoft izini na aiwatar da wannan biyan kuɗi ko ta hanyar ɗebewar lantarki ko tiransifar kuɗi, ko a zaman biyan kuɗi ta hanyar lantarki daga asusunka (misali kamar Automated Clearing House ko biyan kuɗi mai kama da haka), ko caje-caje ga asusunka (misali idan katin bashi ne ko biyan kuɗi mai kama da haka) (a tare gaba ɗaya, "Biyan Kuɗi ta Hanyar Lantarki"). Ana lissafta kuɗin rajista ne ko caji tun kafin lokacin biyan rajistar da ya shafa ya kewayo. Idan aka dawo da kuɗi da ba a biya ba ko idan aka ƙi karɓar ko ƙin yarda da wani katin bashi ko hada-hada mai kama da haka, Micrsoft ko mai samar masa da sabis yana da hakki na karɓar duk wani abu da aka dawo da shi, ƙin karɓa ko wani kuɗi da dokar da ta samar ta shafa.

10. Samuwar Samfuri da Yawa da Kuma Iyakar Oda. Farashin samfuri da samuwa za su iya sauyawa a kowane lokaci ba tare da sanarwa ba. Microsoft za ta iya saka wani wa’adi da yawan kayayyakin da za a saya a kowace oda, a asusu, a katin bashi, mutum ɗaya, ko a gida ɗaya. Idan kayayyakin ko sabis-sabis ɗin da ka yi oda babu su a ƙasa, za mu iya tuntuɓarka don samar maka da wani makamancin samfuri. Idan ba ka zaɓi sayen makamancin samfurin ba, za mu soke odarka.

Microsoft ƙila ta iya ƙin yarda ko ƙin amince da duk wata oda a kowane lokaci, dawo maka da kuɗinka da ka biya na odar, bisa dalilai kamar, amma ba da iyakancewa ba, idan ba ka cim ma sharuɗɗa da aka gindaya a lokacin odar ba, idan ba za a iya aiwatar da biyan kuɗinka, ko kayayyakin da aka yi odar ba sa samuwa, ko don wasu kurakurai na farashi ko wasu daban. A yayin da aka samu wani yanayi kuskuren farashi ko wasu daban, muna riƙe da dama, bisa zaɓinmu, ko dai (a) mu soke odar ko sayayyar ko (b) tuntuɓe ko don umartarka. A yayin da aka samu sokewa, za a hana ka samun dama ga kayayyakin da suka shafi ƙunshiyar.

Haka na ƙila mu hana ka samun dama ga ƙunshiya da ta shafi asusunka bisa kowane irin dalili. Haka nan za mu iya cire ko hana wasanni, manhajoji, ƙunshiya, ko sabis-sabis a kan na’uarka don kare Wurin Adanar ko wasu da abin zai iya shafa. Ta yiwu wasu ƙunshiya da manhajoji su ƙi samuwa daga lokaci zuwa lokaci ko a samar da su na wani ƙayyadadden lokaci. Yanki ma zai iya shafar samuwa. Saboda haka, idan ka sauya asusunka ko na’ura zuwa wani yanki, ƙila ba za ka sami damar sake sauke ƙunshiya ko manhajoji ko sake kallon wasu ƙunshiya da ka saya ba; ƙila ka buƙaci sake sayen ƙunshiyar ko manhajojin da ka riga ka biya a yankinka na baya. Ban da kawai zuwa iyakacin yadda dokar aka sa ta buƙata, ba mu da wajibci na samar da wani sake-sauke ko musanya na duk wata ƙunshiya ko manhajoji da ka saya ba.

11. Sabuntawa. Idan ya shafa, Microsoft za ta bincika kai tsaye don dubawa da sauke sabuntawa zuwa manhajojinka, ko da ba ka shiga cikin Wurin Adana ba. Za ka iya sauya saitunanka idan ka fi son kada ka karɓi sabuntawa ta kai tsaye daga manhajojin Wurin Adana. Kodayake, ƙila a sabunta wasu manhajojin Office Store da ake samunsu gaba ɗaya ko wani ɓangarensu a kan layi a kowane lokaci daga maƙerin manhajar kuma ƙila a buƙaci izininka don sabuntawa.

12. Lasisan Manhaja da kuma Hakkokin Amfani. Manhaja da sauran ƙunshiyar dijital da aka samar ta hanyar Wurin Adana masu lasisi ne, ba sayar maka aka yi ba. Manhajoji da aka sauke kai tsaye daga Wurin Adana sun dogara ne da Sharuɗɗan Lasisin Daidaitacciyar Manhaja ("SALT") da yake samuwa a [https://go.microsoft.com/fwlink/p/?linkid=838610&clcid=0x0468], sai dai idan sharuɗɗan lasisi daban aka samar tare da manhajar. (Manhajoji da aka sauke daga Office Store ba sa ƙarƙashin kulawar SALT suna da keɓaɓɓun sharuɗɗan lasisi.) Manhajoji, wasanni da kuma sauran ƙunshiyar dijital da aka samu ta hanyar Wurin Adana suna ƙarƙashin dokokin amfani da suke samuwa a https://go.microsoft.com/fwlink/p/?LinkId=723143. Ka fahimta kuma ka nuna ka yarda da hakkokinka dangane da waɗannan kayayyakin dijital suna Sharuɗɗan Sayarwa sun iyakance su, dokar hakkin mallaka da kuma dokokin amfani da aka zayyana a sama. Lasisan manhaja da aka saya a Wurin Adana Microsoft na ɗaiɗaiku suna ƙarƙashin yarjejeniyar lasisi da suka biyo manhajar, kuma za a buƙaci ka yarda da yarjejeniyar lasisin a yayin saka manhajar. Duk wani saka samarwa ko sake raba manhaja ko kasuwanci da bai dace da sharuɗɗan lasisi mai alaƙa ba, dokokin amfani, da kuma dokar da ta shafa da aka bayyana ta haramta kuma zai iya haifar da hukunci mai tsanani. Masu keta dokar suna da haɗarin shiga shari’a har iya wa’adin da doka ta ƙyale.

A TUNTUƁI WURIN ADANA MICROSOFT NA ƊAIƊAIKU (KAMAR YADDA AKA BAYYANA A CIKIN SANARWOWI DA KUMA SASHEN TUNTUƁA DA YAKE ƘASA) IDAN KANA SON WANI KWAFI NA YARJEJENIYAR LASISI DA AKA SAKA NA MANHAJA TA CIKIN KWALI, BA TARE DA BIYAN KUƊI BA, KAFINKA BUƊE DUK WANI KWALIN DA YAKE ƊAUKE DA DUK WATA MANHAJA.

SAURAN SHARUƊƊA DA ƘA’IDOJI. Ƙari ga manhaja da kuma sauran kayayyaki da ake saukewa, sauran samfurori da kuma sabis-sabis da suke samuwa don saye ko gwaji a cikin Wurin Adana ƙila a samar maka da su a tare da keɓɓiyar yarjejeniyar lasisi ta mai amfani, sharuɗɗan amfani, sharuɗɗan sabis da sauran sharuɗɗa da ƙa’idoji. Idan ka sayi ko ka yi amfani da waɗannan kayayyaki, ƙila ka buƙaci amincewa da waɗannan sharuɗɗa a zaman wani sharaɗi na saye, sawa, ko amfani.

DON JIN DAƊINKA, MICROSOFT ƘILA TA IYA SAMARWA A WANI ƁANGARE NA WURIN ADANA KO SABIS-SABIS KO A CIKIN MANHAJARTA KO KASUWANCI, KAYAYYAKIN AMFANI DA KAYA NA AMFANI DA KUMA/KOSAUKEWA DA BA ƁANGARE NE NA SAMFURIN KO SABIS-SABIS ƊIN DA AKA SAYAR BA NE. ZUWA IYAKAR DA DOKAR DA AKA SANYA TA ƘYALE, MICROSOFT YIN WANI WAKILCI, GARANTI KO BAYAR DA TABBACI DANGANE DA ABIN DA YA SHAFI DAIDAITO NA SAKAMAKO KO ABIN FITARWA DAGA KOWANE IRIN KAYAYYAKI KO ABUBUWAN AMFANI.

A mutunta dik hakkokin mallakin ilimi na wasu a yayin amfani da kayan aiki da kayayyaki da aka samar ta hanyar Wurin Adana, ko a cikin manhaja ko kasuwanci.

13. Sassauke lambobin Manhaja da Ƙunshiya. Ana isar maka da wasu manhajoji da kuma ƙunshiya ta samar da wata hanyar saukewa da take samuwa a cikin asusun Microsoft ɗinka da ya shafi sayayyarka. La’akari da sakin layin da yake ƙasa, mukan adana hanya saukewa da kuma lambobin dijital masu alaƙa da sayayyar da aka yi a cikin asusun Microsoft ɗinka tsawon shekaru 3 daga ranar sayayyar, amma ba ma alƙawarin adana su ga wani keɓaɓɓen lokaci mai tsawo. Ga kayayyaki masu rajistar da aka isar maka ta samar maka da wata hanyar saukrewa, ƙila a sanya wasu sharuɗɗa da hakkokin adanawa daban, wanda zai ba ka damar bita da kuma yarda gare su a lokacin rajistarka.

Ka yarda cewa za mu iya soke ko gyara shirin adana lambar dijital ɗinka a kowane lokaci. Haka nan ka yarda za mu iya dakatar da tallafin adana lambobi na samfuri ɗaya ko fiye a kowane lokaci kuma bisa kowane dalili, da ya haɗa da, alal misali, a ƙarshen wa’adin tallafin samfurin, wanda bayan nan za ka daina samun iso ga hanyar saukewa ko lambar dijital. Idan muka soke ko gyara shirinmu misali irin wanda ka daina samun damar iso ga hanyar saukewa ko lambar dijital a cikin asusunka, za mu samar maka sanarwar kwanaki 90 kafin nan ta amfani da bayanin tuntuɓa da ya shafi asusun Microsoft.

14. Farashi. Idan muna da wani Wurin Adana Microsoft na ɗaiɗaiku a ƙasarka ko yanki, farshin, zaɓin samfuri da gasa da aka samar a nan ƙila ta bambanta da waɗanda suke samuwa a Wurin Adana na kan layi. Zuwa iyakar da dokar da aka sanya ta ƙyale, Microsoft ba ta bayar da tabbaci na wani farashi, samfuri ko gasa da aka samar a kan a kan layi da kuma samuwa ko girmama wani Wurin Adana Microsoft na ɗaiɗaiku ko akasin haka.

Wurin Adan ba shi da tabbacin daidaiton farashi. Ba za mu daidaita farashin talla tare da sauran gasar wuraren sayarwa ɗaiɗaiku ga abubuwa iri ɗaya ba.

Ƙila mu samar da wani zaɓi na kafin-odar samfurori kafin lokacin samuwarsu. Don ƙarin koyo game da dokokin kafin-oda ɗinmu, ga shafin Kafin-oda ɗinmu https://go.microsoft.com/fwlink/p/?linkid=834935&clcid=0x0468.

Sai dai idan an ambata a wani wuri, farashin da aka nuna a cikin Wurin Adana ba su haɗa da haraji ko cajje-caje ("Haraji") da ƙila za a sa ga sayayyar ba. Farashin da aka nuna a Wurin Adana ba su haɗa da kuɗin kawowa ba. Haraji da kuɗin kowowa (da aka saka) za a ƙara su ga adadin kuɗin sayayyarka kuma a nuna a shafin biyan kuɗin. Kai ke da alhaki na biyan wannan Haraji da kuɗin kawowa.

Dangane da wurinka, mai yiwuwa wasu cinikayya su buƙata musayar kuɗin ƙasasshe waje ko a sarrafa a cikin wata ƙasa dabam. Ƙila bankinka ya yi ƙarin cajin kuɗi na waɗannan ayyuka idan ka yi amfani da wani katin bashi ko katin ɗebewa. Don Allah tuntuɓi bankinka don cikakkun bayanai.

15. Zaɓin Sabuntawa da Ka. Matuƙar ana samar da sabuntawa da ka a ƙasarka, yanki, gunduma, ko jiha, ƙila ka iya zaɓar kayayyaki ko sabis-sabis don sake sabunta su da ka a ƙarshen wani ƙayyadedden wa’adin sabis. Idan ka zaɓi sabunta samfurinka ko sabis da ka, ƙila mu sabunta samfurin ko sabis ɗin da ka a ƙarshin wa’adin samfurin da kuma cajarka farashi na yanzu na sabuntawar, sai dai idan ka zaɓi soke samfurin ko sabis ɗin kamar yadda aka bayyana a ƙasa. Za mu caji hanyar biyan kuɗinka don sabuntawar, ko yana kan fayil ne a ranar sabuntawar ko a samar daga baya. Ƙila ka iya soke samfurorin ko sabis-sabis kafin ranar sabuntawar. Dole ne ka soke kafin ranar sabuntawar don gujewa cajinka don sabuntawar.

16. Dokar Dawo da Kaya. Za mu karɓi dawo da kaya da musanye ga kayayyaki da suka cancanta tsawon kwanaki 14 daga ranar sayayya ko saukewa, kamar yadda yake. Kawai ka dawo da samfuri da ya cancanta kamar yadda yake sabo kum a cikin kwalinsa na asali, tare da duk wasu sassa, kayan haɗi, jagororin masu amfani da takardunsa da aka haɗa da su tun farko. Wannan dokar Dawo da Kaya ba ta shafar hakkinka na doka da ƙila za a iya aiwatarwa ga sayayyarka.

Dole ne a dawo da kwalin manhaja da kuma wasanni ɗauke da tambarin kariya kamar yadda suke kuma dole ne a haɗa da duk wasu kayayyakinsa da kuma lambobin samfuri. A wani yanayi mai iyaka, ana iya dawo da kwalaye na manhaja ko wasanni da aka buɗe a cikin wa’adin dawowar idan ba ka yarda da yarjejeniyar lasisin ba, amma kawai idan ba ka yi amfani ko amfani da duk wani kwafi ba.

Wasu abubuwa ba sa cancantar dawo da su; sai dai idan doka ta tanadi haka ko wata garaɓasa ce ta wani keɓaɓɓen samfuri, duk sayayya na waɗannan nau’o’in samfurori an yi ne a ƙarshe ba a dawo da su:

Manhajojin dijital, ƙunshiyar da rajistocin cikin manhaja, waƙa, finafinai, shirye-shiryen talabijin, da kuma ƙunshiya masu alaƙa;

Katinan kyauta da kuma katinan sabis/rajista (misali, Skype, Xbox Live, Groove Music Pass);

Samfurori da aka shirya bisa zaɓin mutum ko aka keɓance;

odojin samfurori na musamman, idan ba wani ɓangaren wani Wurin Adana ba ne da ake samarwa;

samfurorin ("RAM");

sabis-sabis da aka aiwatar ko amfani da su; da kuma

ko abubuwa da aka yi fitarwa ko abubuwan da aka yi wa alama kamar "Sayarwar Ƙarshe" ko "Ba a dawo da shi".

Idan ka cancanji dawowa da abu, za mu dawo maka da cikakken adadin kuɗi, ƙasa da asalin kuɗin kawowa da kuma caje-cajen isarwa (idan har akwai), kuma za ka sami ramuwar aƙalla cikin kwanakin aiki 3-5. Bayan an sanya duk wata ramuwa zuwa asusu ɗaya, da kuma amfani da hanya irin ɗaya da ta biyan kuɗi, wadda aka yi amfani da ita wajen saka oda (sai dai idan ka zaɓi wani bashin Wurin Adana a cikin adadin ramuwar).

Don cikakkun bayanai kan yadda za ka dawo da kayayyaki da suka cancanya, duba shafin Dawowa da kuma Ramuwa ɗinmu https://go.microsoft.com/fwlink/p/?linkid=723276&clcid=0x0468.

Idan kana da zama a Taiwan, don Allah lura cewa gwargwadon Dokar Kariyar Mai amfani na Taiwan da muhimman ƙa'idojinsa, dukan saye-saye da suka shafa ƙunshiyar dijital da aka samar da ta hanyar tsari maras taɓawa da kuma/ko sabis-sabis na kan layi ƙarshe ne da kuma maras-mayarwa idan aka samar da irin wannan ƙunshiya ko sabis a kan layi. Ba ka da damar neman wani lokacin shan iska ko wata mayarwa kuɗi ba.

17. Biyan kuɗi Gare ka. Idan kana binmu wani kuɗi, ka yarda ka sanar da mu cikin lokaci da kuma samar mana duk wani bayani da muke buƙata wajen biyanka wannan kuɗin. Kai ke da alhaki na duk wasu harajoji da kuma caje-caje da zai iya faruwa a sakamakon wannan biyan kuɗi gare ka. Kai ke da alhaki na duk wani haraji da caje-cajen da zai iya aukuwa a sanadiyyar yi maka wannan biyan kuɗi. Idan ka sami wani biyan kuɗi bisa kuskure, ƙila mu iya warware ko mu buƙaci dawo da biyan kuɗin. Ka yarda ka bayar da haɗin gai gare mu wajen ƙoƙarin mu na aikata wannan. Zuwa iyakar da dokar da aka sanya ta ƙyale, dole ne ka bayar da goyon baya ga sauran sharuɗɗa da muka gindaya a kan hakkinka na duk wani biyan kuɗi.

18. Katinan Kyauta. Katin kyauta da aka saya cikin wani Wurin Adana Microsoft na ɗaiɗaiku suna ƙarƙashin Yarjejeniyar Katin Kyauta na Ɗaiɗaiku da yake samuwa a https://www.microsoftstore.com/store/msusa/html/pbPage.Help_Retail_Stores#GiftCards.

Bayani game da katinan kyauta na Skype suna samuwa a kan shafin Taimako na Skype (https://support.skype.com/en/faq/FA12197/what-is-a-skype-gift-card-and-where-can-i-buy-one).

Karɓa da amfani da katinan kyauta na Microsoft suna ƙarƙashin Sharuɗɗa da Ƙa’idoji na Katin Kyauta na Microsoft (https://commerce.microsoft.com/PaymentHub/Help/Show/toc_link_no_62).

19. Sashen Kula da Abokan Ciniki. Ziyarci shafin Sayarwa da Tallafi namu https://go.microsoft.com/fwlink/p/?linkid=824761&clcid=0x0468 don ƙarin bayani game da zaɓuɓɓukan sashen kula da abokan ciniki.

SHARUƊƊA NA GABA ƊAYA

20. Sauya Sharuɗɗa. Microsoft za ta iya sauya Sharuɗɗan Sayarwar a kowane lokaci kuma ba tare da sanar da kai ba. Sharuɗɗan Sayarwa da ake tilastawa a yayin da ka sanya oda za su kasance ƙarƙashin sayayyarka kuma za su yi amfani a matsayin kwangila tsakaninmu. Kafin ka yi siyayya ta gaba, ƙila Microsoft ta sauya Sharuɗɗan Sayarwar ba tare da sanar da kai ba. Yi bitar Sharuɗɗan Sayarwa a duk lokacin da ka ziyarci Wurin Adana. Mun shawarta cewa ka adana ko yi ɗab’in wani kwafi na Sharuɗɗan Sayarwa don gaba a yayin da ka yi wata sayayya.

21. Iyakoki na Shekaru. Ƙila a saka iyakokin shekaru ga amfani da Wurin Adana da kake yi, da suka haɗa da sayayya.

22. Sirri da Kariyar Keɓaɓɓen Bayani. Sirrinka yana da muhimmanci a gare mu. Muna amfani da wasu bayanai da muka tattara daga wajenka don sarrafa da kuma samarwa Wurin Adana. A karanta Jumlar Sirri ta Microsoft saboda sun bayyana nau’o’ in bayanai da muke karɓa daga gareka da kuma na’urorinka ("Bayanai") da kuma yadda muke amfani da Bayananka. Haka nan Jumlar Sirrin ta wassafa yadda Microsoft take amfani da sadarwarka tare da wasu; bugawa ko miƙa martani da ka yi zuwa Microsoft ta hanyar Wurin Adana; da kuma fayiloli, hotuna, daftaran aiki, sauti, ayyuka na dijital, da kuma bidiyoyi da ka loda, adana ko raba ta hanyar Wurin Adana ɗin ("Ƙunshiyarka"). Ta amfani da Wurin Adana, ka bayyana amincewarka ga tarin Microst, su yi amfani da kuma bayyana Ƙunshiyarka da Bayanai kamar yadda aka bayyana a cikin Jumlar Sirri.

23. Allo da Launin Samfuri. Microsoft tana ƙoƙarin nuna launukan samfuri da kuma hotuna daidai amma ba za mu iya bayar da tabbaci na cewa launin da ka gani a kan na’urarka ko allo zai dace da launin samfurin ba.

24. Kurakura Wajen Gabatar da Wurin Adana. Muna ƙoƙari tuƙuru wajen wallafa bayanai daidai, sabunta Wurin Adana akai-akai, da kuma gyara kurakurai idan an gano su. Kodayake, duk wasu ƙunshiya a cikin Wurin Adana za su iya zama ba daidai ba ko su zama ba na yayi ba a kowane lokaci. Muna riƙe da iko na yin sauye-sauye zuwa Wurin Adana a kowane lokaci, da ya haɗa da farashin samfuri, ƙayyade-ƙayade, garaɓasoshi da kuma samuwa.

25. Ƙare Amfani ko Samun Iso. Microsoft za ta iya ƙare asusunka ba tare da amfani da Wurin Adana ba a kowane lokaci bisa kowane dalili, da ya haɗa, ban da iyakancewa da, idan ka keta waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa ko Dokokin Wurin Adana, ko idan Microsoft ta daina sarrafa Wurin Adana. Ta amfani da Wurin Adana, ka yarda da ɗaukar nauyi (bisa bin waɗannan sharuɗɗa) ga duk wasu odoji da ka yi ko sauye-sauye da suka gudana kafin wannan ƙarewar. Microsft za ta iya sauta, daina, ko kuma dakatar da Wurin Adana a kowane lokaci, bisa kowane dalili, kuma ba tare da sanarwa ba gabani.

26. Garantoci da Iyakokin Magancewa. ZUWA GA ƘUREWAR DA DOKAR ƘASARKA TA BAYAR, MICROSOFT DA KUMA MAI SAMAR MASA DA KAYA, MASU RARRABAWA, MASU SARI, DA KUMA MASU SAMAR ƘUNSHIYA BA SU BAYYANA BA KO WASU GARANTOCI KAI TSAYE, GARANTOCI, KO SHARUƊƊA, DA SUKA HAƊA DA NA KASUWANCI, GAMSUWA, INGANCI, DACEWA DA WATA BUƘATA, JAJIRCEWAR AIKI, DA KUMA RASHIN-KETA DOKA. KAYAYYAKI KO SABIS-SABIS DA AKA SAYA KO SUKE SAMUWA A CIKIN WURIN ADANA SUNA DA GARANTI, IDAN GABA ƊAYA, KAWAI A ƘARƘASHIN DUK WASU YARJEJENIYOYIN LASISI KO GARANTOCIN MAƘERI DA SUKA ZO DA SU. BAN DA KAMAR YADDA AKA SAMAR A ƘARƘASHIN YARJEJENIYAR LASISIN WANI KAMFANI KO GARANTIN MAƘERI DA KUMA LA’AKARI DA HAKKOKINKA NA DOKA:

SAYAYYARKA DA KUMA AMFANI HAƊARIN KANKA NE;

MUN SAMAR DA SAMFUIN DA SABIS-SABIS "KAMAR YADDA SUKE" "TARE DA DUK LAHANONI" DA KUMA "KAMAR YADDA YAKE SAMUWA."

KAI KE DA ALHAKI NA HAƊARI NA INGANCINSU DA ƘARFIN AIKI, DA KUMA

KAI KE DA ALHAKIN BIYAN DUK KUƊIN DA YA SHAFI SABIS KO GYARA.

MICROSOFT BA TA DA TABBACI NA DAIDAITO KO DAIDAITUWAR BAYANI DA YAKE SAMUWA DAGA WURIN ADANA KO SABIS-SABIS ƊIN. KA AMINCE CEWA KWAMFUTA DA SISTEM NA SADARWA BA WAI BA SA SAMUN MATSALA BA, A WASU LOKUTA SUKAN SAMU MATSALA. BA MA BAYAR DA TABBACIN CEWA SAMUN ISO GA WURIN ADANA KO SABIS-SABIS ƊIN BA ZA SU KATSE BA, CIKIN LOKACI, TSARO, KO BA ZA SU SAMU MATSALA BA KO BA ZA A IYA ASARAR ƘUNSHIYA BA.

Idan, duk da waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa, kana da wasu hujjoji na karɓar lalacewar da ta taso dangane da ABIN DA YA SHAFI Wurin Adana, Sabis-sabis, ko duk samfuri ko aiki da aka samar, ZUWA GA IYAKAR DA DOKAR DA TA SHAFA TA SAMAR, ramuwar da za ka samu daga Microosft ko masu samar mata da ITS, dillalai, masu rarrabawa, da kuma masu samar da ƙunshiya jumlar diyyar KAI TSAYE har zuwa (1) farashin ko kuɗi na wata ɗaya na kowane sabis, rajista, ko kuɗi mai kama da wannan (ban da farashin sayen hadwaya, manhaja, tallafi, ko garantoci da aka faɗaɗa), ko (2) Dalar Amurka $100.00 idan babu sabis, rajista, ko kuɗi mai kama da haka.

ƘILA KANA DA WASU HAKKOKI A ƘARƘASHIN DOKAR ƘASARKA. BA WANI ABU A CIKIN WAƊANNAN SHARUƊƊA DA YAKE NUFIN SHAFAR WAƊANNAN HAKKOKI, IDAN AKWAI SU.

Ga masu amfani da suke zaune a New Zealand, ƙila kana da hakkoki na shari’a a ƙarƙashin Dokar Garanti ta Masu Amfani da Kayayyaki ta, kuma babu wani abu a cikin waɗannan Sharuɗɗa da zai shafi waɗannan hakkoki.

27. Iyakacin Ɗaukar Nauyi. ZUWA GA IYAKAR DA DOKAR DA TA SHAFA TA SAMAR, KA YARDA CEWA BA ZA KA IYA DAWO DA DUK SAURAN LALACEWA KO ASARORI, DA SUKA HAƊA DA BABBAR LALACEA, TA MUSAMMAN, A KAIKACE, HAƊARI, KO LALACEWAR GANAGN, RASA RIBA. Iyakoki da wariya ɗin A CIKIN SASSAN 26 DA 27 sun shafi ma idan haɗar da lalacewa da ma idan mun san ko za mu san yiwuwar lalacewar. WASU JIHOHI KO GUNDUMONI/yankuna BA SA ƘYALE WARE KO IYAKANCEWAR LALACEWA NA HAƊARI KO NA GANGAN, SABODA HAKA IYAKANCEWAR SAMA KO WARIYA BA ZA TA IYA SHAFARKA BA.

zuwa iyakar wa’adin da dokar da ta sanya ta shafa, waɗannan iyakoki da wariya da sun shafi Duk wasu KOKE-KOKE, A ƘARƘASHIN KOWACE IRIN SHARI’A, da suka shafi Wurin Adana, Sabis-sabis ɗin, waɗannan sharuɗɗan sayarwa, ko duk wani samfuri ko sabis da aka samar, da ya haɗa da rasa abun ciki, duk wata ƙwayar cuta KO MALWAYA da ya shafin amfani da kake da Wurin Adana ko Sabis KO DUK WANI SAMFURI KO SABIS DA AKA SAMU DAGA WURIN ADANA; DA KUMA jinkiri ko kasawa wajen fara ko kammala watsawar ko hada-hadar.

28. Fashin baƙin Waɗannan Sharuɗɗa. Duk sassan waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa an sanya su zuwa iyakar wa’adin da dokar da ta sanya ta shafa; ƙila kana da hakkoki manya a cikin yankin da kake zaune (ko, idan kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana wajen). Idan ya nuna ba za mu iya tilasta wani ɓangare na waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa kamar yadda aka rubuta ba, ƙila mu iya musanya waɗannan sharuɗɗa tare da wasu sharuɗɗa masu kama zuwa iyakar tilastawa a ƙarƙashin dakar da ta shafa, amma ragowar waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa ba za su canza ba. Waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa dominka da kuma alfanunmu; ba alfanun wani mutum daban ba ne, sai ga magada da kuma waɗanda Microosft ta sa. Za a iya saka sauran sharuɗɗa idan ka sayi kayayyaki ko sabis-sabis daga sauran shafukan yanar gizo na Microsoft.

29. Yarjejeniya. Zuwa iyakar da dokar da aka sanya ta ƙyale, ƙila mu iya sanya, sauya wuri ko kuma watsar da hakkokinmu da wajibci a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa, gaba ɗaya ko wane ɓangare, a kowane lokaci ba tare da sanar da kai ba. Ƙila ba za ka saka waɗannan Sharuɗɗa ko tura su zuwa wasu a ƙarƙashin Waɗannan Saharuuɗan Sayarwa ba.

30. Sanarwowi da Tuntuɓa. Don tallafin tambayoyin abokan ciniki, duba shafin Sayarwa da Tallafi a cikin Wurin Adana. Don saɓani, bi hanyar sanarwa da ke cikin wannan sashe.

31. Abin da ake Kwangila kansa, Zaɓin Shari’a, da kuma Wuri na Warware Saɓani.

a. Amurka ta Arewa ko Kudu wajen Amurka da Canada. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Amurka ta Arewa ko Kudu wajen Amurka da Canada, kana yin kwangila ne tare da Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. Dokar Jihar Washington ce ke kula da fashin-baƙi na waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa da kuma ƙorafe-ƙorafe kan keta su, duk kuwa da zaɓin dokoki. Dokokin ƙasarda miƙa Wurin Adana da Sabis-Sabis su ke kula da duk sauran ƙorafe-ƙorafe (da suka haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci da kuma koke-koke kan lahani).

b. Gabas ta Tsakiya ko Afirka. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Gabas ta Tsakiya ko Afirka, kana yin kwangila ne tare da Microsoft Ireland Operations Limited, The Atrium Building, Block B, Carmanhall Road, Sandyford Industrial Estate, Dublin 18, Ireland. Dokokin Jihar Ireland ne ke kula da fashin-baƙi na waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa da kuma ƙorafe-ƙorafe kan keta su, duk kuwa da zaɓin dokoki. Dokokin ƙasar da miƙa Wurin Adana da Sabis-Sabis su ke kula da duk sauran ƙorafe-ƙorafe (da suka haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci da kuma koke-koke kan lahani). Kai da mu duk mun amince da kotunan Ireland su zama wajen shari’a da kuma warware duk wasu saɓani da suka taso dangane da ko suka shafi waɗannan Sharuɗɗa na Sayarwa ko Wurin Adana.

c. Asiya ko South Pacific, ban da ƙasashen da aka bayyana a ƙasa. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Asiya (ban da Sin, Japan, the Jamhuriyar Korea ko Taiwan), kana yin kwangila ne tare da Microsoft Regional Sales Corporation, wani kamfani da aka tsara a ƙarƙashin dokokin Jihar Nevada, U.S.A., wanda yake da rassa a Singapore da Hong Kong, yake da babban ofishinsa na kasuwanci a 438B Alexandra Road, #04-09/12, Block B, Alexandra Technopark, Singapore, 119968. Dokokin Jihar Washington ce ke kula da fashin-baƙi na waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa da kuma ƙorafe-ƙorafe kan keta su, duk kuwa da zaɓin dokoki. Dokokin ƙasar da miƙa Wurin Adana su ke kula da duk sauran ƙorafe-ƙorafe (da suka haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci da kuma koke-koke kan lahani). Duk wani saɓani da ya taso ko da ya shafi waɗannan Sharuɗɗan Sayarwa ko Wurin Adana, da ya haɗa da duk wata tambaya da ta shafi samuwarsu, inganci, ko ƙarewa, za a tura shi ne zuwa da kuma warwarewa daga ƙarshe a Singapore ta hanyar sauraren ƙara tare da Dokokin Sauraron Ƙara na Singapore International Arbitration Center (SIAC), wanda aka haɗe wasu dokokinta ta nuni da wannan yankin jumla. Kotun Sauraron Ƙarar za ta ƙunshi alƙali ɗaya da Shugaban SIAC zai naɗa. Harshen saurarn ƙarar zai kasance Ingilishi. Hukuncin da alƙalin ya yanke shi zai zama na ƙarshe, yankewa, da kuma ba za a daɗa tayar da ita ba, kuma ƙila a yi amfani da ita a matsayin samfuri na yanke hukunci a kowace ƙasa ko yanki.

d. Japan. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Japan, kana yin kwangila ne tare da Microsoft Japan Co., Ltd (MSKK), Shinagawa Grand Central Tower, 2-16-3 Konan Minato-ku, Tokyo 108-0075. Dokokin ƙasar Japan su ke kula da waɗannan Sharuɗɗa na Sayarwa da kuma duk wasu batutuwa da za su taso dangane da su ko Wurin Adana.

e. Jamhuriyar Korea. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Jamhuriyar Korea, kana yin kwangila ne tare da Microsoft Korea, Inc., 11th Floor, Tower A, K-Twin Tower, Jongro 1 gil 50, Jongro-gu, Seoul, Republic of Korea, 110-150. Dokokin Jamhuriyar Korea su ke kula da waɗannan Sharuɗɗa na Sayarwa da kuma duk wasu batutuwa da za su taso dangane da su ko Wurin Adana.

f. Taiwan. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Taiwan, kana yin kwangila ne tare da Microsoft Taiwan Corporation, 18F, No. 68, Sec. 5, Zhongxiao E. Rd., Xinyi District, Taipei 11065, Taiwan. Dokokin ƙasar Taiwan su ke kula da waɗannan Sharuɗɗa na Sayarwa da kuma duk wasu batutuwa da za su taso dangane da su ko Wurin Adana. Domin ƙarin bayani game da Microsoft Taiwan Corporation, duna shafin yanar gizo da Ma’aikatar Sha’anin Tattalin Arziki R.O.C. ta samar. (https://gcis.nat.gov.tw/main/index.jsp). Kai da mu duk mun amince da Kotun Gunduma ta Taiwan Taipei ta zama kotun farko wajen yanke hukunci a kan warware duk wasu saɓani da suka taso dangane da ko suka shafi waɗannan Sharuɗɗa ko Wurin Adana, zuwa iyakar yadda dokokin Taiwan suka bada dama.

32. Sanarwowi.

a. Sanarwa da hanyoyin ƙorafi kan keta hakkin mallakar ilimi. Microsoft tana mutunta hakkokin mallakar ilimi na wasu. Idan ka yi niyyar aika wata sanarwa ta keta hakkin ilimi, da suka haɗa da ƙorafe-ƙorafen keta dokar hakkin mallaka, yi amfani da hanyoyinmu na miƙa Sanarwar keta doka (https://www.microsoft.com/info/cpyrtInfrg.aspx). DUK TAMBAYOYI DA BA SU DA ALAƘA GA WANNAN HANYA BA ZA SU KARƁI AMSA BA.

Microsoft yana amfani da hanyoyi da aka gindaya a cikin Take na 17, United States Code, Sashe na 512 don bayar da amsa kan sanarwa game da keta hakkin mallaka. A lokuta da suka dace, ƙila Microsoft ta hana ko ƙare asusu-asusu na masu-aiki da ayyukan Microsoft waɗanda ƙila suka sake maimaita keta doka.

b. Sanarwar hakkin mallaka da alamar kasuwanci.

Duk ƙunshiya ta Wurin Adana da Sabis-sabis masu Hakkin mallaka ne © 2016 Microsoft Corporation da kuma/ko masu samar masa kayayyaki da kuma wasu masu samarwa daban, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. An tanadi duk hakkoki. An tanadi duk hakkoki. Mu ko masu samar mana da kayayyaki da kuma wasu masu samarwa daban sun mallaki take, hakkin mallaka, da kuma sauran hakkoki mallakar ilimi a cikin Wurin Adana, Sabis-sabis da kuma ƙunshiya. Microsoft da sunayen, tambarori, da duk alamomin kayayyakin Microsoft da kuma hidimomi za su iya kasancewa alamomin kasuwanci ko alamomin kasuwanci masu rajista na Microsoft a cikin ƙasar Amurka, Canada da kuma/ko sauran ƙasashe.

Za a iya samun jerin alamomin kasuwanci na Microsoft a: https://www.microsoft.com/trademarks. Ainihin sunayen kamfanonin da kuma samfurori za su kasancewa su alamomin kasuwanci na masu su. Duk hakkoki da ba a bayyana a cikin waɗannan Sharuɗɗa na Sayarwa ba an tanade su.

33. Gargaɗin Kariya. Don gujewa rauni, rashin jin daɗi, ko matsalar ido da yake yiwuwa, ya kamata ka ɗauki hutu lokaci-lokaci daga yin amfani da wasanni da sauran manahajoji, musamman idan kana jin wani ciwo ko kasala a sanadiyyar amfanin. Idan ka ɗanɗana rashin jin daɗi, ɗauki hutu. Rashin jin daɗi yana iya haɗa jiwa na tashin zuciya, ciwon motsi, hajijiya, yamutsi, ciwon kai, gajiya, matsalar ido, ko ƙeƙasattun idanu. Yin amfani da manahajoji yana iya ɗauka maka hankali da kuma tsare muhallanka. A kauce haɗarorin tuntuɓe, matakala, silin da ya yi ƙasa, abubuwan aras ko masu kima da suke iya lalace. Wani kason mutane ƙasan ƙila su iya fuskantar kamuwa a yayin kallon wasu hotuna kamar wuta mai walƙiya ko samfurorin da ƙila za su bayyana a cikin manhajojin. Ko da mutane waɗanda ba su da tarihin kamuwa ƙila su sami wani hali da ba a bincika ba da zai haddasa waɗannan kamuwa. Alamomi da suka haɗa da jiri, matsalar gani, kumburi, kakarewa ko motsa laɓɓa, ruɗewa da kuma rasa nutsuwa, ko farfaɗiya. Dakatar da amfani nan-da-nan ka kuma tuntuɓi likita idan ka fuskanci ɗaya daga cikin waɗannan alamomi, ko ka tuntuɓi likita kafin amfani da manhajar idan ka taɓa fuskantar alamomi da aka dangata su da kamuwa. Iyaye za su kula da amfani da ƴaƴansu suke yi da manhajojin don alamomi na kamuwa.

 Martani kan shafi