DAIDAITATTUN SHARUƊƊAN LASISIN MANAHAJA
WURIN ADANA MICROSOFT, WURIN ADANA WINDOWS, DA WURIN ADANA XBOX
An sabunta Oktoba 2017
Waɗannan sharuɗɗan lasisi wata yarjejeniyar ne tsakanin ka da mawallafin manahajar. Sai a karanta su. Suna sanya ga manahajojin sofwaya da ka zazzage daga Wurin Adana Microsoft, Wurin Adana Windows, ko Wurin Adana Xbox (kowanne da aka yi magana game da su a cikin waɗannan sharuɗɗan lasisi a zaman "Wurin adana"), da suka haɗa kowane sabuntawa ko ƙari na manahajar, sai da manahajar ta zo tare da sharuɗɗa dabam, a halin da waɗancan sharuɗɗa za su sanya.
IDAN AKA ZAZZAGE KO YI AMFANI DA MANAHAHAR, KO YIN ƘOƘARIN YI KOWANE A CIKIN WAƊANNAN, KA YARDA DA WAƊANNAN SHARUƊƊA. IDAN BA KA YARDA DA SU BA, BA KA DA HAƘƘIN ZAZZAGE KUMA WAJIBI NE KADA KA ZAZZAGE KO YI AMFANI DA MANAHAJAR.
Mawallafin manahajar yana nufi entitin mai ba ka manahajar, yanda aka shaida a cikin Wurin Adana.
Idan ka bi waɗannan sharuɗɗan lasisi, kana da haƙƙoƙin a ƙasa.
1. GIRKAWA DA AMFANIN HAƘƘOƘI; ƘAREWA. Kana iya girka da kuma yi amfani da manahajar a kan na'urorin Windows ko konsololin Xbox yanda aka kwatance a cikin namu Dokokin Amfani. Microsoft yana mallaka haƙƙin gyaggyara namu Dokokin Amfani a kowane lokaci.
2. AYYUKA DANGANE DA INTANET.
a. Yarda ta ayyuka dangane da Intanet ko mara waya. Idan manahajar tana haɗa da tsare-tsaren kwamfuta bisa Intanet, wanda yake iya haɗa ta wata hanyar sadarwa mara waya, yin amfani da manahajar tana yin aiki a zaman yarda da watsawar daidaitaccen bayanin na'ura (da suka haɗa amma ba su taƙaice ga bayanin fasaha game da na'urarka, sistem ɗinka, da kuma sofwaya na manahajar, da kuma kayan haɗi) don ayyuka dangane da Intanet ko mara waya. Idan aka gabatar da wasu sharuɗɗa haɗe da amfaninka da ayyuka da aka iso ga ta yin amfani da manahajar, waɗancan sharuɗɗa za su sanya kuma.
b. Amfani mara daidai da ayyuka dangane da Intanet. Ba za ka iya yi amfani da kowane aiki dangane da Intanet a wata hanyar da take iya lahanta shi ko hana wani dabam daga yin amfani da shi ko hanyar sadarwa mara waya. Ba za ka iya yi amfani da aikin ko yi ƙoƙarin samu iso ga mara izini zuwa kowane aiki, bayanai, asusu, ko hanyar sadarwa ta wata hanya ba.
3. RANJIN LASISI. An ba da lasisin manahajar, ba a sayar da ita ba. Wannan yarjejeniya tana ba ka kawai wasu haƙƙoƙi yin amfani da manahajar. Idan Microsoft ya naƙasa iyawar yin amfani da manahajoji a kan na'urorinka bisa ga yarjejenniyarka da Microsoft, za a ƙare kowaɗane haƙƙoƙin lasisi da suka danganta. Mawallafin manahajar yana riƙe dukkan sauran haƙƙoƙi. Sai da dokar da take shafa suka ba ka ƙarin haƙƙoƙi duk da wannan taƙaitawa, kana iya yi amfani da manahajar kawai yanda aka yarda da musamman a cikin wannan yarjejeniya. Haka nan, dole ne ka bi kowane taƙaitawar fasaha a cikin manahajar da suke bari ka yi amfani da ita kawai a cikin wasu hanyoyi. Ba sai ka:
a. Nemi hanyar shawo kan kowace taƙaitawar fasaha a cikin manahajar ba.
b. Juya injin, cire sirrin, ko kwance manahajar, sai dai da kuma kawai har iyakar da dokar da take sanya take yarda da duk da wannan taƙaitawa.
c. Yi ƙarin kwafe-kwafi na manahajar fiye yanda aka bayyana a cikin wannan yarjejeniyar ko yanda ake bari ta dokar da take shafa, duk da wannan taƙaitawa.
d. Wallafa ko idan ba haka ba yiwa manahajar ta samu ga wasu domin su yi kwafi.
e. Yi haya, ba da haya don wani lokaci, ko ara wa manahajar.
f. Gusar da manahajar ko wannan yarjejeniyar ga wasu.
4. SANARWA DON YIN AMFANI. Idan aka samar da sanarwa don yin amfani tare da manahajar, kana iya kwafa da kuma yi amfani da sanarwa don yin amfani ɗin don keɓaɓɓen manufan mahangi.
5. FASAHA DA KUMA ƘAYYADEWAR FITAR DA. Manahajar tana iya gana wa sarrafawar fasaha ta Hadaddiyar Daula ko ƙasasshen duniya ko dokoki da kuma ƙa'idojin fitar da. Dole ne ke bi dukan dokoki da kuma ƙa'idoji na gida da kuma na ƙasasshen duniya da suka shafa fasahar da aka yi amfani da ita ko da aka goyi bayanta ta wajen manahajar. Waɗannan dokoki sun haɗa ƙayyadewa a kan wuraren zuwa, masu amfani na ainihi, da kuma amfani na ainihi. Don ƙarin bayani a kan abubuwan sayarwa masu alama na Microsoft, je ka shafin yanar-gizo na fitar waje na Microsoft (http://go.microsoft.com/fwlink/?LinkId=242130).
6. AYYUKAN GOYON BAYA. Tuntuɓi mawallafin manahajar don ƙudurci idan wasu ayyukan goyon baya suke samuwa. Microsoft, kamfanin ƙera na hadwaya ɗinka da kuma kamfanin sadarwa mara waya ɗinka (sai dai ɗaya daga cikinsu mawallafin manahajar ne) ba su a ɗauka nauyin samar da ayyukan goyon baya don manahajar.
7. CIKAKKIYAR YARJEJENIYA. Wannan yarjejeniya, kowace dokar tsare sirri da take shafa, kowaɗane ƙarin sharuɗɗa da suka bi manahajar, da kuma sharuɗɗa don ƙarin da kuma sabuntawa su ne cikakkiyar yarjejeniyar lasisi tsakanin ka da mawallafin manahajar don manahajar.
8. DOKA DA TAKE SHAFA.
a. Hadaddiyar Daula da Ƙasar Canada. Idan ka samu manahajar a Hadaddiyar Daula ko Ƙasar Canada, dokokin jihar ko lardi inda kake da zama (ko, idan wani kasuwanci ne, inda muhimmin wurin kasuwanci yake) suke sarrafa ma'anar waɗannan sharuɗɗa, diyyar ƙeta su, da kuma dukkan sauran ɗiyya (da suka haɗa kariyar mai amfani da kaya, gasa maras adalci, da kuma diyyar ƙetar haƙƙi), ko da saɓanin ƙa'idojin doka.
b. A waje da Hadaddiyar Daula da Ƙasar Canada. Idan ka samu manahajar a wata ƙasa dabam, dokokin waccan ƙasar za su shafa.
9. TASIRIN SHARI'A. Wannan yarjejeniyar yana kwatance wasu haƙƙoƙin shari'a. Ya yiwu kana da wasu haƙƙoƙi a ƙarƙashin dokokin jiharka ko ƙasarka. Wannan yarjejeniyar ba ta canza haƙƙoƙinka a ƙarƙashin dokokin jiharka ko ƙasarka ba idan dokokin jiharka ko ƙasarka ba su yarda a yai ta haka ba.
10. TSAME HANNU NA WARANTI. An ba da lasisin manahajar "yanda-yake", "tare da dukan laifuffuka" da kuma "yanda yake samuwa". Kai ne mai ɗauka nauyin dukan kasadar yin amfani da ita. Mawallafin manahajar, a madadin kansa, Microsoft (idan Microsoft ba mawallafin manahajar ba), kamfanonin sadarwa mara waya waɗanda aka samar da manahajar bisa hanyar sadarwa tasu, da kuma kowane a cikin namu takaimaman dangantawa, masu talla, wakiloli da kuma masu samarwa ("Masu Ɗauka Nauyi"), ba ya ba da warantoci, garantoci, ko ƙa'idoji dangane da manahajar. Cikakken haɗarin game da ingancin, tsaro, nima, da kuma aikin manahajar suna a hannunka. Idan manahajar ta fito da lahani, kai ne mai ɗauka nauyin cikakken kuɗin dukan kular da aiki ko gyara. Wataƙila ka samu ƙarin haƙƙoƙin mai amfani a ƙarƙashin dokoki na gida ɗinda waɗanda wannan yarjejeniya ba za ta iya canza ba. Har iyaka da ake yarda da a ƙarƙashin dokoki na gida ɗinka, Masu Ɗauka Nauyi ba su haɗa wasu warantoci ko ƙa'idoji da suka shafa ba, da suka haɗa waɗanda ake iya sayar da su, kuzari don wani taimaiman manufa, tsaro, nima, da kuma mara-ƙetawa.
11. TAƘAITAWA A KAN DA KUMA WARIYAR AMSOSHI DA KUMA DIYYA. Har iyakar da ba a hana ta wajen doka, idan kana da wata makamar dawo da diyya, kana iya dawo da kawai diyya kai tsaye daga mawallafin manahajar har yawan da ka biya don manahajar ko $1.00 dalar Amurka, kowane mafi babba. Ba za ka nemi, kuma ka watsar da kowane haƙƙin nemi ganewa kowace sauran diyya, da suka haɗa muhimman riba da aka rasa, diyya mara kai tsaye ko mai iya aukuwa na musamman, da ga mawallafin manahaja ba. Idan dokoki na gida ɗinka suka tilasta wani waranti, garanti ko ƙa'idoji ko ma waɗannan sharuɗɗa ba su tilasta ba, an iyakance tsarin lokacinsa zuwa kwanaki 90 daga lokacin da ka zazzage manahajar.
Wannan taƙaitawa yana shafa ga:
• Kome da ya danganta da manahajar ko ayyukan da aka samar da ta hanyar manahajar; da kuma
• Diyya don saɓa yarjejeniya, waranti, garanti, ko ƙa'ida; basusuka masu tsanani, sakaci, ko sauran ƙeta; ƙetawar wata doka ko ƙa'ida; arzuta maras adalci; ko ƙarƙashin sauran nazariyyar dabam; har iyakar da aka yarda ta wajen doka ta take shafa.
Haka kuma yana shafa ko ma idan:
• Wannan amsa ba ta cikakke biya ka diyyar kowace hasara ba; ko
• Mawallafin manahajar ya sani ko ya kamata ya sani game da iyawar diyyar.