Sauye-sauyen da aka samar ga Yarjejeniyar Sabis na Microsoft a taƙaice – 30 ga watan Satumba na shekarar 2026
Muna sabunta Yarjejeniyar Sabis na Microsoft, wanda ya shafi amfaninka na kayayyakin da ayyukan mabuƙacin Microsoft a kan layi. Wannan shafin na ɗauke da muhimman sauye-sauyen da aka yi wa Yarjejeniyar Sabis na Microsoft a taƙaice.
Domin kallon dukkannin sauye-sauyen, to a daure a duba kammalallen Yarjejeniyar Sabis na Microsoft a nan.
- A sama, mun sabunta ranar wallafawa zuwa 30 ga watan Yulin shekarar 2026, sannan mun sabunta ranar fara aiki zuwa 30 ga watan Satumbar shekarar 2026.
- A sashen gabatarwa, mun ƙara bayani domin haɗa da kayayyakin, gidajen yanar gizon da ayyukan mabuƙacin waɗanda suke nufin Yarjejeniyar Sabis na Microsoft ƙarƙashin ¨Ayyuka¨ waɗanda suke ƙarƙashin sharuɗɗan.
- A sashen ¨Samuwar Sabis¨, mun ƙara bayani waɗanda suka shafi musamman dokokin da ƙa’idojin ƙasar Brazil.
- A sashen ¨Ƙungiyar Yarjejeniyar Kwangila, Zaɓin Doka, & Wuri na Warware Saɓani¨, mun sabunta ƙungiyar yarjejeniyar kwangila ga wasu ƙasashe a Amurka ta Arewa, Amurka ta Kudu da kuma South Pacific.
- A sashen ¨Yarjejeniyoyi¨, mun ƙara bayani waɗanda suka shafi musamman dokokin da ƙa’idojin ƙasar Brazil.
- A sashen ¨Sharuɗɗan Keɓaɓɓen-Sabis¨, mun yi ƙare-ƙare da sauye-sauyen da aka zayyana a ƙasa:
- A sashen ¨Wurin Adana¨, mun sabunta bayani game da sabuntawar otomatik, wanda ke ba masu amfani damar dakatawar sabuntawar otomatik, kuma mun bayyana illolin idan wasu manhajoji suka kasa sabuntawa.
- Karkashin sashen ¨Cortana¨, mun yi bayani cewa Microsoft ba ya ƙara tallafawa Cortana tun daga shekarar 2024, kuma mun cire sassan da suka shafi ayyukan Cortana da ba za a iya amfani da su ba yanzu.
- A sashen ¨Manhajoji da Sabis-sabis na Microsoft 365¨, mun sabunta sunayen jerin kayayyakin Microsoft 365 kuma mun fayyace cewa amfani da manhajoji da sabis-sabis da aka ambata suna ƙarƙashin sharuddan lasisin.
- A sashen ¨Kayayyakin Dijital¨, mun goge ambaton Microsoft Groove, wanda ba ya samuwa yanzu.
- A sashen ¨Microsoft Rewards¨, mun sabunta hanyoyin haɗi zuwa shafukan tallafi da suka dace kuma mun sabunta adadin maki da za a iya fansa a shekara domin ya nuna matakai biyu na iyaka.
- An sake canza sunan sashen ¨Copilot¨ kuma an fayyace nau’ikan Copilot da Yarjejeniyar Sabis na Microsoft ya shafa.
- Cikin dukanin Sharuɗɗan, mun yi canje-canje domin inganta fahimta da kuma magance nahawu, kuskuren bugawa, da kuma irin al'amurran da suka shafi. Kuma mun sabunta sanyawar suna da kuma kalmomin haɗi.