Tsarin Sirrinka
1. Tsarin Sirrinka. Tsarin sirrinka yana da muhimmanci a gare mu. Daure ka karanta Bayanan Tsarin Sirri na Microsoft (https://go.microsoft.com/fwlink/?LinkId=521839) ("Bayanan Tsarin Sirri" ɗin) yadda ya bayyana nau'o'in bayanan da muke tara daga gare ka da kuma na'urorinka ("Bayanai"), yadda muke yin amfani da Bayananka, da kuma dalilolin shari'a da muke da shi don sarrafa Bayananka. Haka kuma Bayanan Tsarin Sirrin ɗin yana bayyana yadda Microsoft ke yin amfani da ƙunshiyarka, wanda yake sadarwarka tare da wasu; abubuwan da ka aika zuwa ga Microsoft ta hanyar Sabis-sabis ɗin; da kuma fayiloli, hotuna, daftarori, sauti, ayyuka na dijital, watsawa ta kai tsaye da kuma bidiyoyi da ka ɗora, ajiye, yaɗa, ƙirƙira, fito da, ko raba ta hanyar Sabis-sabis ɗin, ko shigarwar da ka miƙa domin fito da ƙunshiya ("Ƙunshiyarka"). A inda sarrafawa ya dogara da ƙunshiyar da kuma har iyakar da aka yarda ta doka, idan ka yarda da waɗannan Sharuɗɗa, ka amince Microsoft ya tara, yi amfani da kuma bayyana Ƙunsiyarka da kuma Bayananka yadda aka bayyana a cikin Bayanan Tsare Sirri ɗin. A wasu halaye, za mu samar da keɓaɓɓiyar sanarwa da kuma buƙatar yardarka kamar yadda yake a cikin Bayanan Tsare Sirri.
Ƙunshin bayanin ka
2. Ƙunshin bayanin ka. Mafi yawan Sabis-sabis ɗinmu suna ba ka damar ƙirƙira, adana ko raba Ƙunshiyarka ko karɓar kayayyaki daga wasu. Ba mu a iƙirarin mallakar Taka Ƙunshiyar. Taka Ƙunshiyar zai kasance taka kuma kai ne kake ɗauka nauyinsa.
- a. Idan ka raba Taka Ƙunshiyar tare da sauran mutane, ka fahimci cewa ƙila za su iya samun damar, ta gama-gari, yi amfani, adana, naɗa, sake sarrafa, watsawa, yaɗa, raba da kuma nuna Taka Ƙunshiyar don dalilin da ka sa a samu Taka ƙunshiyar a kan Sabis-sabis, ban tare da biyanka diyya ba. Idan ba ka son wasu su sami dama ba, kada ka yi amfani da Sabis-sabis ɗin don raba Taka Ƙunshiyar. Kana wakilta da kuma yarda cewa a tsawon lokaci na waɗannan Sharuɗɗa, kana da (kuma za ka sami) duk haƙƙoƙi da suke da wajibi don Taka Ƙunshiyar da aka ɗora, ajiye, ko raba a kan ko ta hanyar Sabis-sabis ɗin da kuma cewa tarawa, amfani, da kuma riƙewa Taka Ƙunshiyar ba zai keta kowace doka ko haƙƙi na wasu. Microsoft ba da mallaka, sarrafa, tabbatar, biya, ko shawarta ko kuma ɗaukar duk wani nauyi bisa Ƙunshiyarka kuma ba za a riƙe ta da alhaki na Ƙunshiyarka ko sauran kayayyaki da aka loda, adana ko rana ta amfani da Sabis-sabis ɗin.
- b. Zuwa iya iyakar wajibci na samar maka da Sabis-sabis da kuma wasu, don kare ka da kuma Sabis-sabis ɗin, da kuma inganta samfurori da Sabis-sabis ɗin Microsoft, ka ba wa Micorosft hakki ga hanyar kayanka na intanet da kuma amfani da lasisin hakkin mallakar ilimi ga Ƙunshiyarka, misali, samar da kwafi, riƙewa, watsawa, sake tsarawa, nunawa, da kuma rarrabawa ta hanyar kayayyakin sadarwa da Ƙunshiyarka a kan Sabis-sabis ɗin. Idan ka wallafa Ƙunshiyarka a cikin yankuna na Sabis-sabis in da yake samuwa a kan layi ba tare da taƙaitawa ba, ƙila Ƙunshiyarka ta bayyana a cikin misali ko kayayyaki da suke tallata Sabis ɗin. Wasu Sabis-sabis da talla yake goyon baya. Bayani kan yadda Microsoft take keɓance talla yana samuwa a https://choice.live.com. Ba ma amfani da abin da ka ce a cikin imel, taɗi, kiran bidiyo na saƙon murya, ko daftaranka, hotuna ko sauran keɓaɓɓun fayiloli don turo maka talla. Ana kula da dokokin talla namu a cikakken bayani a cikin Jumlar Sirri ɗin.
- c. Microsoft yana samar maka da ikon samun dama ga bayanan ka da za a iya fitarwa ta Allon gudanarwar sirri na Microsoft (https://account.microsoft.com/privacy) ko yanayin mai amfani da samfur, lokacin da aka tabbatar da ingancin tare da asusun Microsoft ɗinka. Za a iya amfani da bayanan da za a iya fitarwa wajen sauyawa zuwa wani mai tanadar da sabis. Microsoft na da hakkin ƙayyade fitarwar bayanai wanda zai iya sassauta tsaron sabis ɗin ko kadarorin ilimi na Microsoft. Idan ka kasa fitar da bayanan ka ta waɗannan injinan, tuntuɓi Microsoft a adireshin cikin Yadda za a tuntuɓe mu sashi (https://privacy.microsoft.com/privacystatement#mainhowtocontactusmodule) ko ta amfani da fom na intanet ɗinmu (https://go.microsoft.com/fwlink/?linkid=2126612).
Ƙa'idar Aiki
3. Ƙa'idar Aiki. Kai ne kake ɗauka nauyin ɗa'arka da kuma ƙunshiyarka a lokacin da kake yin amfani da Sabis-sabis ɗin.
- a. Ta amincewa da waɗannan Sharuɗɗan, kana amincewa da shi, lokacin amfani da Sabis ɗin, ciki har da sabis na AI wanda ke yanke shawara, ko ɗaukan shawara, mai zaman kansa tare da matakai daban-daban na shiga tsakani na mutum, za ka bi waɗannan dokokin:
- i. Kada ka yi wani haramtaccen abu, ko yi ƙoƙarin fitar da ko raba ƙunshiyar da ta kasance haram.
- ii. Kada ka saka kanka cikin wani aiki da yake lalata, cutar, ko barazanar cutar da ƙananan yara.
- iii. Kada ka aika sifam ko jingarta cikin saƙon masu sata bayanan mutum, ko yi ƙoƙari da fitar da ko raba malwaya. Saƙon bogi wani imel ne da ba a so kuma wani tarin imel ne da ba a so, turawa, buƙatun tuntuɓa, SMS (rubutattun saƙonni), ko saƙonnin nan-take, ko sadarwar na'urar lantarki makamani. Hanyar damfara a yanar-gizo shi ne aikawa saƙonnin imel ko wasu sadarwar lantarki don zuga masu karɓa su bayyana keɓaɓɓen bayaninsu ko bayani masu kara ta hanyar zamba ko ta haram, kamar kalmomin sirri, ranakun haihuwa, lambobin Tsaron Jama'a, lambobin fasfo, bayanin katin bashi, bayanin sha'anin kuɗi, ko sauran bayani mai kara, ko don samun iso ga zuwa asusu-asusu ko naɗe-naɗe, sata bayanai daga daftarorin aiki ko sauran bayani na kara, biyan kuɗi da kuma/ko fa'idar sha'anin kuɗi. Malwaya yana haɗa da kowane aiki da aka zana don jawo lahani na fasaha, kamar su isar da maƙetacin abu da ake iya zarta, tsarawa hana farmakin sabis ko gudanar da umarni da kuma uwannin garke na sarrafawa.
- iv. Kada ka nuna a bainar jama’a ko amfani da Sabis-sabis don fito da ko raba ƙunshiya ko kayayyaki da ba su dace ba (da suka haɗa misali tsiraici, fasiƙanci tsakanin ɗan’adam da dabba, finafinai na fasiƙanci, kalaman ɓatanci, zane na tashin hankali, kisan kai, ko aikata laifi) ko Ƙunshiyarka ko kayayyako da ba su bin dokoki da ƙa’idoji na gida.
- v. Kada ka jingata cikin aikin da suke kasance zamba, ƙarya ko mai ruɗewa (alal misali, neman kuɗi da bisa yaudara, yin sojan gona wani mutum dabam, ƙirƙirar asusu na jabu, aiki mara tabbaci na kai tsae, fito da ko raba ƙunshiyar da aka yi niyya ta ruɗa, juya Sabis-sabis don ƙara adadin yin wasa, ko shafi makami, kimantawa, ko sharhohi) ko na rainuwa ko na ɓatanci.
- vi. Kada ka guje kowaɗane iyakoki a kan samun dama, amfani, ko samuwa Sabis-sabis (alal misali yin ƙoƙarin "gujewa kurkuku" wani tsarin AI ko tsamewa bayanai mara izini).
- vii. Kada ka jingata cikin aikin da suke da lahani gare ka, Sabis-sabis ɗin, ko sauran (alal misali watsar da sankarorin kwamfuta, lekawa, yin ƙoƙarin fito da ko raba ƙunshiyar da suke takura, tsangwama ko yi barazana wasu, aikawa ƙunshiya ta ta'adanci ko mai tashin hankali sosai, sadar da magana ta tsana, ko ciyar da tashin hankali ga wasu).
- viii. Kada ka keta ko saɓa haƙƙoƙi na wasu (alal misali rabawa kiɗa masu haƙƙin mallaka ko sauran kaya mai haƙƙin mallaka ba tare da izini ba, sake sayar da ko sauran rabawa da taswirorin Bing, ko ɗauka hotuna ko naɗe-naɗen bidiyo/sauti na wasu ban da yardarsu don sarrafa masu ganowa/bayanin surar mutum ko wani sauran dalili ta yin amfani da kowane daga cikin Sabis-sabis ɗin).
- ix. Kada ka sa kanka cikin wani aiki da ya keta sirri ko kariyar hakkin mallaka ta wasu.
- x. Kada ka taimakawa wasu karya waɗannan dokoki.
- Ƙarin bayani game da dokokinmu, hanyoyin kima da tilastawa da sharuɗɗa takamaimai ga sabis yana samuwa a aka.ms/trustandsafety.
Amfani da Sabis & Tallafi
4. Amfani da Sabis-sabi da Tallafi.
- a. Asusu Microsoft. Za ka buƙaci wani asusu Microsoft don samun dama ga yawa daga cikin Sabis-sabi. Asusu Microsoft ɗinka yana ba ka damar shiga samfurori, shafukan yanar gizo da kuma ayyuka da Microsoft da wasu abokan hulɗar Microsoft suke samarwa.
- i. Ƙirƙirar Asusu. Za ka iya ƙirƙirar asusu Microsoft ta yin rajistar a kan layi. Ka amince ba za ka yi amfani da duk wani bayani na ƙarya ko mara daidai ko mai ruɗewa a yayin yin rajistar don asusunka na Microsoft. A wasu lokuta, wani daban, kamar mai samar maka da sabis na Intanet, ƙila ya sanya maka wani asusun Microsoft. Idan ka karɓi asusu Microsoft ɗinka daga wani daban, ƙila wannan wani daban ɗin yana da ƙarin haƙƙi a kan asusunka, kamar damar samun iso ko share asusunka na Microsoft. Daure a yi bitar ƙarin sharuɗɗa da wani dabam ya samar maka, don Microsoft ba ta da nauyi da ya shafi waɗannan ƙarin sharuɗɗa. Idan ka ƙirƙiri wani asusun Microsoft a madanin wani abu, kamar kasuwancinka ko ma’aikaci, ka wakilta cewa kana da haƙƙi na shari'a don ɗaure wancan abu da waɗannan sharuɗɗa. Ba za ka iya miƙa bayananka na asusun Microsoft ga wani mai amfani ko wani abu ba. Domin kare asusunka, ajiye muhimman bayanan asusunka da kuma kalmar sirri a asirtacce. Kai ne da alhaki na duk wani aiki da ya faru a ƙarƙashin asusun Microsoft ɗinka.
- ii. Amfani da Asusu. Dole ne ka yi amfani da asusu Microsoft don barin sa a cikin aiki. Wannan na nufin dole ne ka shiga ciki aƙalla sau ɗaya a tsawon lokacin shekara biyu don ajiye asusun Microsoft ɗinka, da Sabis masu alaƙa (sa dai idan an bayyana ba haka bane), ,mai aiki, sai dai idan an samar da mafi tsawon lokaci a cikin aikin dokar asusun Microsoft a https://go.microsoft.com/fwlink/p/?linkid=2086738 ko a cikin tayi na kashi da aka biya na Sabis ɗin. Idan ba ka shiga a cikin wannan lokacin ba, za mu ɗauka asusunka na Microsoft ba ya cikin aiki kuma za mu rufe maka shi. Daure a duba sashe na 4.a.iv.2 don sakamako na asusun Microsoft da aka rufe. Dole ne ka shiga akwatin saƙon Outlook.com ɗinka da kuma OneDrive (a ware) aƙalla sau ɗaya a shekara, idan ba haka ba za a rufe maka akwatin saƙonka na Outlook.com da kuma OneDrive ɗinka. Idan bisa gaskiya mun yi zaton asusun Microsoft ɗinka yana cikin haɗari na yiwuwar wani ya yi amfani da shi ta hanyar zamba (alal misali, a sakamakon wani fallasar asusun), Microsoft za ta iya dakatar da asusunka har sai ka yi iƙirarin mallakarsa. Dogara da halin sulhu, muna iya buƙara a naƙasa iso ga zuwa wasu ko dukan Ƙunshiyarka. Idan kana fuskantar matsala wajen samun iso ga asusun Microsoft ɗinka, daure ka ziyarci wannan shafin yanar gizo: https://go.microsoft.com/fwlink/?LinkId=238656.
- iii. Yara da Asusu. Idan ka ƙirƙira wani asusun Microsoft ko kana yin amfani da Sabis-sabis, ka yarda kuma ka amince a ɗaure ka da waɗannan Sharuɗɗa kuma ka nuna cewa ka kai shekarun “balaga” ko “na ɗaukar nauyi bisa shari’a” a inda kake da zama ko iyayenka ko mai riƙonka yana amince a ɗaure su da waɗannan Sharuɗɗa a madadinka. Idan ba ka sani ko ka kai shekara na "balaga" ko “ɗaukar nauyi bisa shari'a” a inda kake da zama ba, ko ba ka fahimci wannan sashe ba, daure ka nemi taimako wajen iyayenka ko mai riƙonka bisa shari'a. Idan kai wani iyaye ko mai riƙo na wani yaro ne, kai da yaron kun yarda kuma kun amince a ɗaure ku da waɗannan Sharuɗɗa kuma kuna ɗauka nauyin dukkan amfani da asusu ko Ayyuka na Microsoft, da suka haɗa sayayya, ko an buɗe asusun yaron yanzu ko an ƙirƙira daga baya.
- iv. Rufewa Asusunka.
- 1. Za ka iya soke wasu keɓaɓɓun Ayyuka ko rufe asusun Microsoft a kowane lokaci bisa kowane dalili. Domin a rufe asusun Microsoft ɗinka, ziyarci https://go.microsoft.com/fwlink/p/?linkid=618278. Idan ka umarce mu mu rufe asusunka na Microsoft, za ka iya zaɓa a saka shi a yanayin dakartacce don ko kwanaki 30 ko 60 kawai idan za ka sake yanke shawara. Bayan wancan tsawon lokaci na kwana 30 ko 60, za a rufe asusun Microsoft ɗinka. Daure a duba sashe na 4.a.iv.2 da ke ƙasa domin cikakken bayani kan abin da yake faruwa idan an rufe asusun Microsoft ɗinka. Sake shigarwa yayin tsawon lokacin dakatar da zai sake aikatar da asusun Microsoft ɗinka.
- 2. Idan an rufe asusun Microsoft ɗinka (kai da kanka ko mu), wasu abubuwa kaɗan suna faruwa. Da farko, damarka ta amfani da asusun Microsoft ɗin don samun iso ga Ayyukan tana tsayawa nan-da-nan. Na biyu, za mu share Bayananka ko Ƙunshiyarka dangane da asusun Microsoft ɗinka ko kuma mu raba ta da kai da kuma asusunka na Microsoft (sai dai idan doka ta buƙaci mu ajiye ta, dawo da ita, ko miƙa ta gare ka ko wasu da ka amince). Za ka sami wani tsarin wararriyar ajiya koyaushe saboda Microsoft ba zai iya dawo da Ƙunshiyarka ko Bayanai da zarar an rufe asusunka ba. Na uku, za ka iya rasa samun iso ga samfurorin da ka samu.
- b. Kima da Zartarwa. Yawan Sabis-sabis ɗinmu da suke ba ka damar yin hulɗa, ƙirƙira, fito da, da kuma raba ƙunshiya tare da wasu suna cin amfanin tsare-tsare masu tsaro don kare Sabis-sabis ɗinmu da kuma sauran masu amfani.
- i. Dokoki. Namu Dokar Ɗa'ar Ma'aikata yana gano abin da ake haramta a lokacin da ake amfani da Sabis-sabis ɗinmu. Ana iya samun ƙunshiyarmu da dokokin tsare sirrinmu a nan (https://www.microsoft.com/DigitalSafety/policies). Takamaiman Sabis-sabis suna da ƙarin dokoki da ƙa'idojin al'umma da suke sanya ga masu amfani ɗinsu, waɗanda suke samuwa a nan (https://aka.ms/trustandsafety).
- ii. Yin Rahoto wata Damuwa. Za ka iya yi rahoto damuwa game da ƙunshiya da kuma tsarin hali da suke keta namu Dokar Ɗa'ar Ma'aikata a nan (https://aka.ms/reportconcerns).
- iii. Yi bita. A inda yake sanya, mai yiwuwa mu yi amfani da tsare-tsare na kai tsaye da kuma mutane don yi bitar ƙunshiya don gane sifam da aka yi zargi, sankarorin kwamfuta, zamba, saƙo mai sata bayanan mutane, malwaya, gujewa kurkuku, ko sauran ƙunshiya ko tsarin hali masu haram ko masu lahani.
- iv. Tilastawa. Muna mallaka haƙƙin ƙi ƙunshiya idan ta wuce iyakokin a kan ma'ajiya ko girman fayil da ake yarda da ta wajen Sabis ɗin. Muna iya toshe, cire ko ƙi nuna ƙunshiya idan yana nuna cewa ta keta Dokar Ɗa'ar Ma'aikata ɗinmu ko wata dokar Sabis dabam ko inda Doka take buƙata. Idan ka keta waɗannan sharuɗɗa ko Dokoki (https://aka.ms/trustandsafety), mai yiwuwa mu ɗauki mataki kan asusunka. Wannan yakan haɗa da iyakanci samun dama ga wasu siffofi ko Sabis-sabis, tsayar da samar da Sabis-sabis, rufewa asusunka na Microsoft nan da nan ko toshewa isar da sadarwa (kamar su imel, rabawa fayil ko saƙon nan take) zuwa ga ko daga Sabis-sabis ɗin. Rufewa damar da kake samu ga wani Sabis ko asusunka yakan iya jawo rasawar lasisocin ƙunshiya, ƙunshiya masu alaƙa, zaman mamba, da kuma ragowar asusun Microsoft mai alaƙa da asusun. A yayin yin bitar tuhumar keta waɗannan Sharuɗɗa, Microsoft yana mallaka haƙƙin yin bitar ƙunshiyar don warware matsalar. Ko da yake, ba za mu iya ƙura ido a cikakkun Sabis-sabis ba kuma ba mu yi ƙoƙarin yin haka ba. Don ƙarin bayani game da hanyoyin kiyayewa da zartarwa (https://www.microsoft.com/DigitalSafety/moderation-and-enforcement), Sharuɗɗa takamaimai ga Sabis, Ƙarin dokoki da ƙa'idoji (https://www.microsoft.com/DigitalSafety/policies/additional-guidelines), da ƙara (https://www.microsoft.com/DigitalSafety/moderation-and-enforcement/appeals), duba https://aka.ms/trustandsafety. Ana iya samun bayani game da dokarmu dangane da diyyar keta haƙƙin mallaka ƙirar mutum a SANARWA.
- c. Asusu na Aiki ko Makaranta. Za ka iya shiga wasu sabis-sabis na Microsoft ta amfani da wani adireshin imel na aiki ko makaranta. Idan ka yi, kana yarda da cewa za a iya sanar da mamallakin bagiren hurumin mai alaƙa da adireshin imel ɗinka da kasanscewar asusun Microsoft ɗinka da kuma rajistocinsa masu alaƙa, sarrafa da kuma gudanar da asusunka, da kuma iso ga da sarrafa Bayananka, da suka haɗa da ƙunshiyoyi ta sadarwarka da kuma fayilolinka, da kuma cewa ƙila Microsoft ta sanar da mamallakin bagiren hurumin idan an fallasa asusun ko Bayanan. Ka ƙara yarda da cewa amfaninka da sabis-sabis na Microsoft yana iya gana wa yarjejeniyoyin da Microsoft yake da su tare da kai ko ƙungiyarka kuma waɗannan Sharuɗɗa ba su shafa ba. Idan ka riga kana da wani asusun Microsoft kuma kana yin amfani da wani adireshin imel na aiki ko makaranta dabam don iso ga Sabis-sabis da ake kula da su a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa, ta yiwu a faɗakar da kai ka sabunta adireshin imel da aka danganta da asusun Microsoft ɗinka domin a ci gaba da iso ga irin waɗannan Sabis-sabis.
- d. Ƙarin Na'urori/Shirye-shiryen Bayanai. Don yin amfani da yawanci daga cikin Ayyukan, za ka buƙaci wani haɗin intanet da kuma/ko tsarin bayanai/salula. Haka nan ƙila za ka buƙaci ƙarin na’urori, kamar wata na'urar kai, kyamara ko makarufo. Kai ne da alhaki na samar da duk haɗe-haɗe, tsare-tsare, da kuma na’urori da ake buƙata don amfani da Ayyukan da kuma biyan kuɗin da mai samar da haɗe-haɗenka, tsare-tsare, da kuma na’ura ya yi caji. Waɗannan kuɗaɗe ƙari ne ga duk kuɗaɗe da ka biya mu don Ayyukan kuma ba za mu dawo maka da waɗannan kuɗi ba. Duba wajen mai samarwarka don ƙudurta idan akwai irin waɗannan kuɗi da za a iya sanya maka.
- e. Sanarwar Sabis. Idan akwai wani abu da muke buƙatar gaya maka game da wani Aiki da kake amfani da shi, za mu aika maka sanarwar Aiki. Idan ka ba mu adireshin imel ɗinka ko lambar waya dangane da asusun Microsoft ɗinka, sannan za mu iya aika maka sanarwar Aiki ta hanyar imel ko ta hanyar SMS (rubutaccen saƙo), da ya haɗa don tabbatar da shaidarka kafin yin rajistar lambar wayarka ta hannu da kuma tabbatar da saye-sayenka. Haka nan kuma ƙila mu aika maka da sanarwar Aiki ta sauran hanyoyi (misali ta hanyar saƙonin cikin-samfuri). Za a iya biyan kuɗin bayanai ko yin saƙo lokacin karɓar sanarwa ta SMS.
- f. Tallafi. Tallafi don wasu Sabis yana samuwa a https://support.microsoft.com kuma ana gudanar da shi ta waɗannan sharuɗɗan, kuma wasu Sabis na iya bayar da ƙarin tallafin abokin ciniki ko daban, bisa ga ƙarin sharuɗɗa. Ta yiwu tallafi ba zai samu ga sigogi na fara duba ko gwaji ba na siffofi ko Ayyuka. Samuwar Tallafi na iya bambanta dangane da matakin rayuwar samfurin kuma dole Ka samu Sabis(s) na lasisi bisa inganci da cancanta wanda ya cika mafi ƙarancin buƙatun nema don tallafi da aka yi bayani a cikin Rayuwar Microsoft (https://learn.microsoft.com/lifecycle). Ba lallai Sabis ɗin ya dace ba tare da manhaja ko sabis da wasu suka bayar, kuma kana da alhakin sanin kanka tare da baƙatun dacewa.
- g. Ƙare Sabis-sabis ɗinka. Idan an soke Sabis ɗinka (ko da kai ne ko mu), da farko damar isa ga Sabis ɗin zai tsaye nan take kuma lasisin ka ga manhajar da ke da alaƙa ga Sabis ɗin ya zo karshe. Na biyu, za mu share Bayanai ko Ƙunshiyarka masu alaƙa da Aikinka ko kuma mu raba ta da kai da asusun Microsoft ɗinka (sai dai idan doka ta buƙaci mu ajiye ta, dawo da ita, ko miƙa ta gare ka ko wasu da ka amince). A sakamakon haka, ta yiwu ka daina samun iso ga kowane daga cikin Ayyukan (ko Ƙunshiyarka da ka adana a kan waɗancan Ayyukan). Ya kamata kana da wani shirin tsimi na akai-akai. Na uku, za ka iya rasa samun iso ga samfurorin da ka samu. Idan ka soke asusun Microsoft ɗinka kuma ba ka da wani asusun da zai samu iso ga Sabis-sabis ba, ta yiwu za a soke Sabis-sabis ɗinka nan-da-nan.
Amfani da Manhajoji da Sabis-Sabis na Wasu
5. Amfani da Manhajoji da Sabis-Sabis na Wasu. Sabis-sabis ɗin ƙila su ba ka damar samun iso ko mallakar samfurori, sabis-sabis, shafukan yanar gizo, hanyoyi, kayayyaki, wasanni, dabaru, haɗewa, bots ko manhajoji daga wasu mutane masu zaman kansu (kamfanoni ko mutane waɗanda ba Microsoft ba) ("Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu"). Mafi yawan Sabis-sabis ɗinmu haka nan suna taimaka maka samu, yin buƙatu ga, ko hulɗa da Manhajoji da kuma Sabis-sabis na Wasu kuma na iya ƙyale ko buƙata ka yaɗa Ƙunshiyarka ko Bayananka tare da irin waɗannan Manhajoji da kuma Sabis-sabis na Wasu, kuma ka fahimci cewa ta amfani da Sabis-sabis ɗinmu kana umartarsu da su samar maka Manhajoji da kuma Sabis-sabis na Wasu. Haka nan ƙila waɗannan Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu za su iya ƙyale ka ko buƙata ka adana Ƙunshiyarka ko Bayanai ba tare da mawallafin ba, mai samarwa, ko mai sarrafa Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu ɗin. Manhajoji da Sabis-sabis na wasun ƙila su gabatar maka da wata manufar tsare sirri ko su buƙace ka ka yarda da sharuɗɗa kafin ka iya saka ko amfani da Manhaja ko Sabis na Wasu. Duba sashe na 13.b don ƙarin sharuɗɗa don manhajoji da aka samu ta hanyar wasu Wuraren Adana da Microsoft ko rassansa ya mallaka kuma yake sarrafawa (da suka haɗa, amma, ba su taƙaita ga, Wurin Adana na Office, Microsoft Store a kan Xbox da kuma Microsoft Store a kan Windows. Za ka yi bitar sharuɗɗa da manufofin tsare sirri na wasu kafin samu, amfani, buƙata, ko haɗa Asusun Microsoft ɗinka ga duk wasu Manhajoji ko kuma Sabis-sabis na Wasu. Duk wasu sharuɗɗan wasu ba sa gyara waɗannan Sharuɗɗa. Microsoft ba ta bayar da lasisin duk wani hakkin mallaka na ilimi gare ka a zaman duk wasu Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu. Ka yarda ka ɗauki duk wani nauyi da ya taso daga amfani da waɗannan Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu da kuma cewa Microsoft ba ta da alhaki na duk wata matsala da ta taso ta amfani da su. Microsoft ba ta da alhaki gare ka ko wasu na bayani ko sabis-sabis da duk Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu suka samar.
Samuwar Sabis
6. Samuwar Sabis.
- a. Sabis-sabis ɗin, Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu, ko kaya ko samfurori da aka samar ta hanyar Sabis-sabis ɗin ƙila za su iya ƙin samuwa daga lokaci zuwa lokaci, ƙila a samar da su a taƙaice, ko ƙila su bambanta ta la’akari da yankinka ko na’ura. Idan ka sauya wuri da ya shafin asusun Microsoft ɗinka, ƙila ka buƙaci sake samun kaya ko manhajoji da aka samar maka ta hanyar biya da ka yi a yankinka na da. Ka yarda ba za ka sami iso ga ko amfani da kaya ko Sabis-sabis waɗanda suke haramtattu ba ko da ba bayar da lasisi don amfani a ƙasarka wadda daga ciki ka sami iso ko amfani da waɗannan kaya ko Sabis-sabi, ko don soke ko rashin wakiltar wurinka ko shaida don samun iso ko amfani da waɗannan kaya ko Sabis-sabis.
- b. Muna jajircewa wajen sa Sabis-sabis aiki; amma, duk sabis-sabis na kan layi suna samun katsewa da dakatarwa lokaci-lokaci, kuma Microosft ba shi ne da alhaki na duk wata katsewa ko asara da za a iya fuskanta a sakamakon haka ba. A hali na dakatarwa, ƙila ba za ka iya samun damar dawo da Ƙunshiyarka ko Bayanai da ka adana ba. Muna shawartarka da ka riƙa adani akai-akai na Ƙunshiyarka da kuma Bayanai da ka adana kan Sabis-sabis ko wurin adana ta amfani da Sabis-sabis da Manhajoji na Wasu.
Sabuntawa ga Ayyuka ko Sofwaya ɗin, da kuma Canje-canje ga Waɗannan Sharuɗɗa
7. Sabuntawa ga Ayyuka ko Sofwaya ɗin, da kuma Canje-canje ga Waɗannan Sharuɗɗa.
- a. Ƙila za mu iya canza waɗannan Sharuɗɗa a kowane lokaci, kuma za mu sanar da kai idan mun yi hakan. Yin amfani da Ayyukan bayan canje-canjen su fara aiki yana nufin ka yarda da sababbin sharuɗɗan. Idan ba ka yarda da sababbin sharuɗɗan ba, dole ne ka dakatar da amfani da Ayyukan, rufe asusun Microsoft ɗinka, sannan, idan kai mahaifi ne ko mai riƙon, ka taimaki ƙaramin yaronka rufe asusun Micorosft ɗinsa ko ɗinta.
- b. Wani lokaci za ka buƙatar sabuntawan sofwaya domin ka ci gaba da yin amfani da Ayyukan. Muna iya bincika sigarka ta sofwaya ɗin ta otomatik da kuma zazzage sabuntawan sofwaya ko canje-canjen tsarin. Haka kuma wataƙila akwai buƙatar ka sabunta sofwaya ɗin domin ka ci gaba da yin amfani da Ayyukan. Waɗannan sabuntawa suna gana wa waɗannan Sharuɗɗa sai dai idan wasu sharuɗɗa sun zo da sabuntawa, a wannan hali, za a sanya waɗancan sharuɗɗan. Ba a tilastawa Microsoft ya samar da kowaɗane sabuntawa ba kuma ba ta bayar da tabbaci na cewa za mu tallafa sigar ta tsarin don wanda ka sayi ko samun lasisi na sofwaya, manhajoji, ƙunshiya ko sauran samfurori ba. Mai yiwuwa irin waɗannan sabuntawa ba za su dace da sofwaya ko ayyuka da wasu dabam suka samar ba. Za ka iya janya yardarka ga sabuntawan sofwaya na gaba a kowane lokaci ta hanyar fasa girka sofwaya ɗin.
- c. Bugu da ƙari, akwai wasu lokuta da muke buƙatar cire ko canza siffofi ko aiki na Aikin ko dakatar da samar da wani Aiki ko samun iso ga Manhajoji da Ayyuka na Wasu a tare. Sai dai har iyakar da dokar da ta shafi take buƙata, ba mu da wajibi na samar da wani sake-zazzage ko mayewa na kowane kaya, Kayayyakin Dijital (da aka bayyana a sashe na 13.i), ko manhajoji da aka saya a baya. Mai yiwuwa mu saki Ayyukan ko siffofinsu a cikin wata sigar fara duba ko gwaji, wanda ƙila ba zai yi aiki daidai ba ko a cikin wata hanya irin da sigar ta ƙarshe za ta iya aiki.
- d. Domin ka iya amfani da kaya da aka kare da gudanarwar haƙƙin dijital (DRM), kamar wasu waƙoƙi, wasanni, finafinai, littattafai da sauransu. sofwaya na DRM zai iya tuntuɓi sabar haƙƙin mallaka ta kan layi da kuma zazzage da girka sabuntawan DRM ta otomatik.
Lasisin Sofwaya
8. Lasisin Sofwaya. Sai dai idan ya zo da wata wararriyar yarjejeniyar lasisin Microosft (misali, idan kana amfani da wata manhajar Microsoft da ta haɗa da wani ɓangare na Windows, a kokacin Sharuɗɗan Lasisin Manhajar Microsoft na Windows Operating System yake kula da wannan sofwaya), duk wata sofwaya da muka samar gare ka a zaman wani ɓangare na Sabis-sabis ɗin ya shafi waɗanann Sharuɗɗa. Manhajoji da aka samu ta hanyar wasu Wuraren Adana da Microsoft ko rassansa ya mallaka kuma yake sarrafawa (da suka haɗa, amma ba su taƙaita ga, Wurin Adana na Office, Microsoft Store a kan Windows da Microsoft Store a kan Xbox) suna ƙarƙashin sashi na 13.b.i da yake ƙasa.
- a. Idan ka bi waɗannan Sharuɗɗa, mun ba ka dama ta saka da kuma amfani da kwafi ɗaya na manhajar a na’ura ɗaya ta la’akari da faɗin-duniya don amfani kawai ga mutum ɗaya a zaman wani ɓangare na amfani da Sabis-sabis da kake yi. Ga wasu na’urori, akan fara saka wanann manhaja don amfanin kanaka, amma ba amfani da Sabis-sabis ɗin ba don kasuwanci. Manhajar ko shafin yanar gizon wani ɓangare ne na Sabis-sabis ƙila ya haɗa da lambar sirrin wasu. Duk wani rubutu na wasu ko lambar sirri, da aka haɗa aka nuna daga manhajar ko shafin yanar gizon, masu wannan lambar sirrin ne suka baka lasisin, amma ba Microsofy ba. Sanarwa, idan akwai, ta lambar sirrin wasu ana sa maka ita ne kawai don bayani.
- b. Manhajar mai lasisi ce, ba sayarwa ba, kuma Microsoft ita ke da duk hakkoki ga manhajar da ba a bayyana ko bayarwa daga Microsoft ba, ko a kaikaice, da shaida, ko akasin haka. Wannan lasisi bai ba ka wani hakkki don yin, kuma ƙila ba za ka iya:
- i. dabara ko kaucewa duk wasu hanyoyin kariyar kimiyya a ciki ko da suka shafi manhajar ko Sabis-sabis ɗin;
- ii. sake haɗawa, buɗewa, shiga, kwafi, ci-da-gumi, ko juya kimiyya ta duk wata manhaja ko wani ɓangare na Sabis-sabis da aka saka a ciki ko ake iso ta hanyar Sabis-sabis ɗin, ban da kawai zuwa wa’adin da dokar hakkin mallakar da ta shafa ta ƙyale aikata hakan;
- iii. ware kayan manhajar ko Sabis-sabis don amfani a kan wasu na’urori daban;
- iv. wallafa, kwafi, haya, bayar da haya, sayarwa, fitarwa, shigarwa, rarrabawa, ko bayar da aron manhajar ko Sabis-sabis ɗin, sai dai idan Microsoft ta ba da izinin haka a rubuce;
- v. mayar da manhaja ko wani lasisin manhaja zuwa wani, ko duk wani hakki na samun iso ko amfani da Sabis-sabis ɗin;
- vi. yin amfani da Sabis-sabis ta duk wata hanya da ba a bayar da izini ba za ta iya katse amfani da wani yake yi da su ko samun iso ga duk wani sabis, bayani, asusu, ko hanyar sadarwa;
- vii. ƙyale iso ga Sabis-sabis ko gyara wani na’ura mai izinin-Microsoft (misali, konsololin Xbox, Microsoft Surface, da sauransu) daga wasu manhajojin wasu marasa izini.
Sharuɗɗan Biyan Kuɗi
9. Sharuɗɗan Biyan Kuɗi. Idan ka sayi wani Sabis, ana sanya waɗannan sharuɗɗan biyan kuɗi ga sayayyarka kuma ka yarda da su.
- a. Cajin kuɗi. Idan akwai wani caji da ya shafi wani ɓangare na Sabis-sabis ɗin, ka amince ka biya wannan caji a cikin kuɗin da aka fayyace. Farashin da aka bayyana a cikin Sabis-sabis bai haɗa da kuɗaɗen haraji da na canjin kuɗi ba, sai dai idan an bayyana akasin haka. Duka farashin samfurorin Skype da aka biya sun haɗa da haraji da aka saka, sai dai idan an bayyana akasin haka. Kai ke da alhaki na biyan waɗannan haraji ko sauran caji. Skype yana lissafta haraji ne ta la’akari da adireshin wurin da kake da ya shafi bayanin biyan kuɗinka. Kai ke da alhaki na tabbatar da cewa wannan adireshi yana aiki kuma daidai ne. Ban da kawai samfurorin Skype, ana lissafta haraji ne ta la’akari da wurin da kake a lokacin da aka yi rajistar asusun Microsoft ɗinka sai dai idan dokar ƙasa ta buƙaci wani dalili daban na lissafin. Ƙila mu dakatar ko soke Ayyukan idan ba mu sami wani cikakken biyan kuɗi daga gare ka a kan loaci ba. Dakatar ko soke Ayyuka a sanadiyyar rashin biyan kuɗi zai iya haifar da rasa samun dama da kuma amfani da asusunka da kuma abun ciki nasa. Haɗi da Intanet ta hanyar kamfani ko sauran keɓaɓɓun hanyar sadarwa wanda yake toshe wajenka ƙila ya haifar da caji ya zama daban daga waɗanda ake nunawa ga ainihin wajenka. Dangane da wurinka, mai yiwuwa wasu cinikayya su buƙata musayar kuɗin ƙasasshe waje ko a sarrafa a cikin wata ƙasa dabam. Mai yiwuwa bankinka ya caje ka ƙarin kuɗi don waɗannan sabis-sabis idan ka yi amfani da wani katin deɓe kuɗi ko amsar kuɗi. Don Allah tuntuɓi bankinka don cikakkun bayanai.
- b. Asusunka na Biyn Kuɗi. Don biyan caji na wani Sabis, za a buƙace ka da ka samar da wata hanyar biyan kuɗi a lokacin da ka yi rajistar wannan Sabis. Don dukkan Sabis-sabis ban da Skype, za ka iya samu dama zuwa da kuma canza bayanin lissafin kuɗi da kuma hanyar biyan kuɗi naka a kan shafin yanar-gizo na gudanarwar da asusun Microsoft (https://go.microsoft.com/fwlink/p/?linkid=618281) kuma don sofwaya da kuma kayayyaki na Skype ta shigarwa cikin ƙofar asusunka a https://skype.com/go/myaccount. Ƙari ga wannan, ka yarda ka ƙyale Microsoft ya yi amfani da duk wani bayanin sabunta asusu da ya shafi hanyar biyan kuɗi da aka zaɓa da bankinka ya samar ko hanyar biyan kuɗi da aka sa. Ka yarda a sabunta asusunka da sauran bayaninka nan da nan, da suka haɗa adireshin imel da cikakkun bayanan hanyar biyan kuɗi ɗinka, domin mu iya kammala cinikayyarka da kuma tuntuɓe ka yadda ake buƙata dangane da cinikayyarka. Sauye-sauye da aka yi ga asusun biyan kuɗinka ba zai shafi sauye-sauyen da muka miƙa zuwa asusun biyan kuɗinka kafin mu iya tsayawa a madadinka a kan sauye-sauye ga asusun biyan kuɗinka ba.
- c. Byan kuɗi. Ta samarwa da Microsoft wata hanyar biyan kuɗi, ka (i) bayyana cewa ka kana da izini na amfani da hanyar biyan kuɗin da ka samar kuma cewa duk wani bayani na biyan kuɗin da ka samar gaskiya ne kuma daidai ne; (ii) ka ba wa Microsoft izini na cajin Sabis-sabis ɗinka ko ƙunshiya mai samuwa ta amfani da hanyar biyan kuɗinka; kuma (iii) ka ba wa Microsoft izini na cajin duk wata siffar Sabis-sabis ɗin ta biya da ka zaɓa don rajista ko amfani yayin tilasta waɗannan Sharuɗɗa. Ƙila mu iya cajinka (a) tun kafin lokaci; (b) a lokacin sayayya; (c) jim kaɗan bayan sayayya; ko (d) a wasu lokuta na sake aukuwar rajistar Ayyuka. Hakanan za mu iya cajin ka har zuwa adadin da ka amince da shi, kuma za mu sanar da kai kafin duk wani canji a cikin adadin da za a caji don Ayyukan biyan kuɗi da ke maimaituwa. Ƙila mu caje ba a lokaci guda na sama da ɗaya daga cikin lokutanka da ka fi so na biyan kuɗi na adadin kuɗin ba a riga an aiwatar a baya ba.
- d. Maimaita Biyan Kuɗi. Idan ka sayi wani Sabis-sabis ta hanyar rajista (misali wata-wata, kowane watanni 3 ko shekara-shekara), ka amince kuma ka yarda cewa bayar ga izini da maimaita biyan kuɗi, da kuma biyan kuɗi za a yi ne ga Microsoft ta hanyar da ka zaɓa a tazarar maimaitawar da ka yarda da ita, har sai ka ƙarar ko Microsoft ta ƙarar da rajistar wannan Sabis. Dole ka soke Sabis-sabis ɗinka kafin ranar lissafi ta gaba don dakatar da yiwuwar cajin kuɗi don ci gaba da Sabis-sabis ɗinka. Za mu samar maka da umarni a kan yadda za ka soke Sabis-sabis ɗin. Ta bayar da izini maimaita biyan kuɗi, ka ba wa Microsoft izini na aiwatar da wannan biyan kuɗi ko ta hanyar ɗebewar lantarki ko tiransifar kuɗi, ko a zaman biyan kuɗi ta hanyar lantarki daga asusunka (misali kamar Automated Clearing House ko biyan kuɗi mai kama da haka), ko caje-caje ga asusunka (misali idan katin bashi ne ko biyan kuɗi mai kama da haka) (a tare gaba ɗaya, "Biyan Kuɗi ta Hanyar Lantarki"). Ana lissafta kuɗin rajista ne ko caji tun kafin lokacin biyan rajistar ya shafa ya kewayo. I dan aka dawo da kuɗi da ba a biya ba ko idan aka ƙi karɓar ko ƙin yarda da wani katin bashi ko hada-hada mai kama da haka, Micrsoft ko mai samar masa da sabis yana da hakki na karɓar duk wani abu da aka dawo da shi, ƙin karɓa ko kuɗi da ba su cika ba don aiwatar da wannan biyan kuɗi a zaman Biyan Kuɗi ta Hanyar Lantarki.
- e. Jawabin kan intanet da kuma Kurakura. Don dukkan Sabis-sabis ban da Skype, Microsoft zai samar maka da wani bayanin lissafin kuɗi na kan layi a kan shafin yanar-gizo na gudanarwar da asusun Microsoft (https://go.microsoft.com/fwlink/p/?linkid=618282), inda za ka iya duba da kuma yi ɗab'i bayaninka. Don Skype, za ka iya samu dama ga bayani na kan layi ɗinka ta shigarwa cikin asusunka a www.skype.com (https://www.skype.com). Wannan ne kawai bayanin ajiya da muke samarwa. Idan mun yi wani kuskure wajen cajinka, dole ne ka sanar da mu cikin kwanaki 90 da bayyanar wannan kuskure a kan cajinka. Sannan za mu fara binciken cajin. Idan ba ka sanar da mu ba cikin wannan lokaci, ka sake mu daga duk nauyi da ƙorafe-ƙorafe na rashi da ya samu daga kuskuren kuma ba za a buƙata mu gyara kuskuren ko samar da mayarwa kuɗi ba, sai dai idan doka ta buƙata haka. Idan Microsoft ta gano wani kuskuren cajin kuɗi, za mu gyara wannan kuskure cikin kwanaki 90. Wannan dokar ba ta shafi duk wasu hakkoki na shari’a ba da za a iya sanyawa.
- f. Dokar Ramuwa. Sai dai an samar da shi ta hanyar doka ko sharuɗɗan na wata takamaimiyar tayar Sabis ta wata hanya, an karasa dukkan saye-saye kuma ba a mayar da kuɗin. Idan ka yi imani Microsoft ta caje ka bisa kuskure, dole ne ka tuntuɓe mu cikin kwanaki 90 da yin wannan caji. Babu mayarwa kuɗi da za a bayar da don kowaɗane caje-caje sama da kwanaki 90, sai dai idan doka ta buƙata haka. Muna da haƙƙi na samar da ramuwa ko basusuka bisa ganin damarmu sai dai idan ba haka ake buƙata ta wajen doka ba. Idan mun bayar da ramuwa ko bashi, ba ma ƙarƙashin wani wajibci na samar da ramuwa ɗaya ko mai kama ga matsala ta gaba. Wannan dokar ramuwa ba ta shafi duk wasu hakkoki na shari’a ba da za a iya sanyawa. Don ƙarin bayanin mayar da kuɗi, sai a ziyarci namu batun taimako (https://go.microsoft.com/fwlink/p/?linkid=618283). Idan kana da zama a Taiwan ko Isra'ila, don Allah lura cewa gwargwadon Dokar Kariyar Mai amfani ɗin da kuma muhimman ƙa'idojinsa, dukan saye-saye da suka shafa ƙunshiyar dijital da aka samar da ta hanyar tsari maras taɓawa da kuma/ko sabis-sabis na kan layi ƙarshe ne da kuma maras-mayarwa idan aka samar da irin wannan ƙunshiya ko sabis a kan layi. Ba ka da damar neman wani lokacin shan iska ko wata mayarwa kuɗi ba.
- g. Soke Sabis-sabis ɗin. Za ka iya soke wani Sabis a kowane lokaci, tare ko ba tare da dalili ba. Soke Sabis-sabis na biyan kuɗi yana dakatar da cajin kuɗi don ci gaba da Sabis. Don a soke wani Sabis da kuma buƙata wata mayarwa kuɗi, idan kana da damar samu wata, ziyarci Shafin yanar=gizo na gudanarwar da asusun Microsoft. Don Skype, sai kammala Fom na Janye ta yin amfani da bayanin da aka samar da shi nan (https://go.microsoft.com/fwlink/p/?linkid=618286). Ya kamata ka sake duba tayin da ke bayyana Sabis-sabis ɗin a zaman (i) ƙila ba za ka karɓi wata ramuwa a lokacin sokewar ba; (ii) ƙila a wajabta maka biyan kuɗin sokewa; (iii) ƙila a wajabta maka biyan duk caje-cajen ga asusunka na biyan kuɗi na Ayyukan kafin ranar sokewar; ko (iv) ƙila ka rasa samun dama ga asusunka idan ka soke Sabis-sabis ɗin; ko, idan kana da zama a Taiwan ko Isra'ila, (v) kana iya ka karɓi wata mayarwa kuɗin a yawan da ya yi daidai da kuɗin da ka biya don wani Sabis da ba a yi amfani da su ba wanda ake lissafawa a lokacin sokewa ɗin. Idan kana zama a Isra'ila ya yiwu ka soke ta kowace a cikin waɗannan hanyoyi da aka jera a https://support.microsoft.com/help/4027815. Sai a tuntuɓi wani wakilin Microsoft ta hanyar tarho don samun wata ramuwa idan ka cancanta don haka. Za mu aiwatar da Bayananka kamar yadda aka bayyana a sashe na 4. Idan ka soke, samun isonka ga wannan Sabis zai ƙare daga lokacinka na ƙarshe na Sabis ko, idan muna cajin asusunka ta lokaci ne, a ƙarshen lokacin da ka soke. Idan ka tayar da wani sake yin caji ko juyawa tare da bankinka don biyanka na Sabis-sabis, za mu ɗauka ka soke daga ranar da aka yi biyan kuɗi na ainihi, kuma ka ba mu izinin soke sabis ɗinka nan da nan da kuma/ko ɗanyata kowace ƙunshiyar da aka samar maka a musayan irin wannan biyan kuɗi.
- h. Tayi na Lokacin-Gwaji. Idan kana cikin wani tayin gwaji, ƙila a buƙaci ka soke Sabis na gwajin cikin wani wa’adin lokaci da aka sanar da kai a yayin yarda da tayin domin kauce wa cajin kuɗi don ci gaba da Sabis a ƙarshen wa’adin gwajin. Don wasu tayi na lokacin gwaji, muna iya buƙatar a kunna sabuntawa kai tsaye.
- i. Tayi na Garaɓasoshi. Daga lokaci-zuwa-lokaci, Microsoft ƙila za ta iya samar da Sabis-sabis a kyauta a yayin lokacin gwaji. Microsoft tana da alhaki na cajinka ga waɗannan Sabis-sabis (a farashi na daidai) a yayin da Microsoft ya gano (bisa zaɓin kansa) cewa kana cin zarafin sharuɗɗan wannan gasa.
- j. Sauyawar Farashi. Ƙila mu sauya farashin Sabis-sabis ɗin a kowane lokaci kuma idan kana da wata sayayya mai sake aukuwa, za mu sanar da kai ta hanyar imel aƙalla kwanaki 15 kafin sauya farashin. Idan ba ka yarda da canza farashin ba, dole ne ka soke da kuma dakatar da amfani da Ayyukan kafin canza farashin ya fara aiki. Idan akwai wani sharaɗi da aka saka wa’adi da kuma farashi na Sabis ɗin da aka samar maka, wannan farashin zai kasance cikin tilastawa zuwa wa’adin da aka saka.
- k. Biyan Kuɗi Gare ka. Idan kana bin mu kuɗi, ka yarda ka samar mana da duk wani bayani da muke buƙata don yi maka biyan cikin lokaci da kuma daidaito. Gana wa dokar da ta shafa, kai ne mai ɗauka nauyin wasu harajoji da kuma caje-caje da zai iya faruwa a sakamakon wannan biyan kuɗi gare ka. Haka nan dole ka bi duk wasu sauran sharuɗɗa da muka sa a kan hakkinka na duk wani biyan kuɗi. Idan ka sami wani biyan kuɗi bisa kuskure, ƙila mu iya warware ko mu buƙaci dawo da biyan kuɗin. Ka yarda ka bayar da haɗin gai gare mu wajen ƙoƙarin mu na aikata wannan. Ƙila kuma za mu iya rage biyan kuɗi gare ka ba tare da sanarwa don daidaita duk wani biyan kuɗi fiye da ƙima na baya ba.
- l. Katinan Kyauta. Ana gudanar da fansawa da kuma amfani da katunan kyauta (ban da katunan kyauta na Skype) ta Sharuɗɗa da Ƙa'idoji na Katin Kyauta na Microsoft (https://support.microsoft.com/help/10562/microsoft-account-gift-card-terms-and-conditions). Bayani kan katunan kyauta na Skype yana samuwa a Shafin taimako (https://go.microsoft.com/fwlink/?LinkId=615383) na Skype.
- m. Hanyar Biyan Kuɗi ta Asusun Banki. Za ka iya rajistar wani asusun banki da ya cancanta tare da asusun Microsoft ɗinka don amfani da shi a matsayin wata hanyar biyan kuɗi. Asusu-asusun da suka cancanta sun haɗa da asusu-asusu da ake da su a cibiyoyin hada-hadar kuɗi da suke iya karɓar ɗebe kuɗi na kai tsaye (misali wata cibiyar sha’anin kuɗi na Amurka da take goyon bayan automated clearing house ("ACH"), wani cibiyar hada-hadar sha’anin kuɗi da take goyon bayan Single Euro Payments Area ("SEPA") ko "iDEAL" a ƙasar Netherlands). Ana sanya sharuɗɗan da ka yarda da su wajen ƙara asusun bankinka a matsayin wata hanyar biyan kuɗi a cikin asusun Microsoft ɗinka (misali, “dokar” dangane da abin da ya shafi SEPA). Ka amince ka bayar da tabbacin cewa asusun bankinka cikin sunanka yake kuma an ba ka izinin yin rajista da kuma amfani da wannan asusun banki a matsayin wata hanyar biyan kuɗi. Ta yin rajista ko zaɓar asusun bankinka a matsayin hanyar biyan kuɗinka, ka ba wa Microsoft (ko jami’anta) izini na fara ɗiba ɗaya ko fiye da haka daga jumullar sayayyarka ko kuɗin rajista (bisa dacewa da sharuɗɗan sabis na rajista) daga bankinka (kuma, idan ya zama wajibi, fara ɗaukar kuɗi daga asusunka don gyara kurakurai, bayar da ramuwa ko wani dalili mai kama da haka), kuma ka ba wa cibiyar hada-hadar sha’anin kuɗi izini na riƙe asusun bankinka don ɗebe wannan kuɗi ko karɓar wannan kuɗi. Ka fahimci cewa izinin zai kasance cikin amfani da kuma aiki har sai ka cire bayanin bankinka daga asusun Microsoft. Tuntuɓi cibiyar tallafin abokin ciniki kamar yadda aka ambata a sama a sashen 4.e cikin gaggawa idan kana da yaƙinin an caje ka bisa kuskure. Dokoki da suka shafi ƙasarka haka nan suna taƙaita nauyinka kan duk wata zamba, kuskure ko hulɗa marar izini daga asusun bankinka. Ta yin rajista da kuma zaɓar wani asusun banki a matsayin hanyarka ta biyan kuɗi, ka amince ka karanta, fahimci da kuma yarda da waɗannan Sharuɗɗa.
Ƙungiyar Yarjejeniyar Kwangila, Zaɓin Doka, & Wuri na Warware Saɓani
10. Ƙungiyar Yarjejeniyar Kwangila, Zaɓin Doka, & Wuri na Warware Saɓani. Domin amfani da kake yi da Ayyukan masu alama-Skype na abokin ciniki na kyauta da kuma biyan kuɗi, idan kana da zama a waje da Turai, Gabas ta Tsakiya da kuma Afirka, waɗanda kake kwangila da su, kuma duk mahangi ga “Microsoft” a cikin waɗannan Sharuɗɗa suna nufin, Skype Communications S.à.r.l, 23 – 29 Rives de Clausen, L-2165 Luxembourg sai dai idan an bayyana dabam a ƙasa. Domin Ayyuka masu alamar-Skype na kyauta ko biyan kuɗi, idan kana da zama a waje da Turai, Gabas ta Tsakiya da Afrika, dokar Luzamburg ne take gudanar da fassarar waɗannan Sharuɗɗa da kuma diyyar ketarsu, ko me ne saɓanin aƙidun doka. Dokokin yardin ko ƙasar da kake da zama sune suke gudanar da duk sauran diyya (da suka haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci, da kuma diyya kan lahani). Idan kana da zama ne a waje da Turai, Gabas ta Tsakiya da kuma Afirka, kai da mu mun yarda da dokar ta musamman mara canzawa da kuma wuri na kotunan Luzamburg domin duk saɓani da yake taso daga ko dangane da Ayyukan masu alamar-Skype. Domin duk sauran Ayyuka, abun da kake yi wa kwangila, dokar mai sarrafa, da kuma wurin da za a warware saɓanin za su bayyana a ƙasa:
- a. Kanada. Idan kana da zama a (ko, idan wani kasuwanci ne, ainihin wurin kasuwancinka yana a) Kanada, kuma kana yin amfani da Ayyuka masu alamar-Skype na biyan kuɗi, ko idan kana yin amfani da ɓangarori na kyauta na Microsoft Teams, kana yin kwangila tare da Skype Communications US Corporation, 2215-B Renaissance Drive, Las Vegas, NV 89119, Ƙasar Amurka. Don duk sauran Sabis-sabis na abokin ciniki na kyauta ko na biyan kuɗi, kana ba wa Microsoft Corportation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052 Ƙasar Amurka kwagila. Dokoki na lardin da kake da zama (ko, idan wani kasuwa ne, ainihin wurin kasuwanka) suke gudanar da fassarar waɗannan Sharuɗɗa, diyya don ketarsu, da kuma duk sauran diyya (da suke haɗa da kariyar abokin ciniki, gasa mara adalci, da kuma diyyar tsallake abu mai muhimmanci), ba tare da la'akari da saɓani ga ƙa'dojin doka ba. Kai da mu mun yarda da dokar ta musamman mara canzawa da kuma wuri na kotunan a Ontario domin duk saɓani da yake taso daga ko dangane da waɗannan Sharuɗɗa ko Ayyukan.
- b. Amurka ta Arewa ko Kudu wajen Amurka da kuma Canada. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Amurka ta Arewa ko Kudu wajen Amurka da kuma Canada, kana yin kwangila ne tare da Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. Dokar Jihar Washington ce ke kula da fashin-baƙi na waɗannan Sharuɗɗa da kuma ƙorafe-ƙorafe kan keta su, koda kuwa wace irin babbar doka ce ta saɓanin. Dokokin ƙasar inda muka tura Ayyukanka ne suke gudanar da duk sauran diyya (da suke haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci, da kuma diyya kan lahani).
- c. Gabas ta Tsakiya, Afirka ko Turai. Idan kana da zama ne a (ko, idan wani kasuwanci ne, ainihin wurin kasuwancinka yana a) Gabas ta Tsakiya, Afirka, ko a Turai ban da Tarayyar Turai (EU) Ƙasar Aislan, Lichtenstein, Norwe, Switzerland, da kuma Birtaniya, kuma kana yin amfani da ɓangarori na kyauta na Ayyukan (kamar Bing da MSN), kana yin kwangila ne da Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, Ƙasar Amurka, sai dai idan kana yin amfani da ɓangarori na kyauta na Skype, kana yin kwangila ne da Microsoft Ireland Operations Limited, One Microsoft Place, South County Business Park, Leopardstown, Dublin 18, Ireland. Idan ka biya kuɗi don yin amfani da wani ɓangare na Ayyukan, kana yin kwangila ne da Microsoft Ireland Operations Limited, One Microsoft Place, South County Business Park, Leopardstown, Dublin 18, Ireland. Domin Ayyuka na kyauta da kuma na biyan kuɗi, dokokin Ireland ne suke gudanar da fassarar waɗannan Sharuɗɗa da kuma diyyar ketarsu, ko me ne saɓani na aƙidun dokoki. Dokokin ƙasar inda muka tura Ayyukanka ne suke gudanar da duk sauran diyya (da suke haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci, da kuma diyya kan lahani). Kai da mu mun yarda da dokar ta musamman mara canzawa da kuma wuri na kotunan Ireland domin duk saɓani da yake taso daga ko dangane da waɗannan Sharuɗɗa ko Ayyukan.
- d. Asiya ko South Pacific, sai dai idan an cire ƙasarka musamman a ƙasa. Idan kana zama a (ko, idan kasuwanci, babban wurin kasuwancin ka yana cikin) Asiya (ban da China, Japan, Jamhuriyar Koriya, ko Taiwan) ko kuma Kudancin Pasifik, kuma kana amfani da kaso kyauta na Sabis ɗin (kamar Bing da MSN), kana yarjejeniyar kwangila tare da Kamfanin Microsoft, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. Idan ka biya don amfani da kaso na Sabis ɗin, ko kana amfani da sabis na Outlook.com kyauta a Singapore ko Hong Kong, kana yarjejeniyar kwangila tare da Microsoft Regional Sales Pte Ltd., kamfani da aka tsara ƙarƙashin dokokin Singapore, tare da adireshin sa mai rajista a 182 Cecil Street, #13-01 Frasers Tower, Singapore 069547; da aka bayar, cewa idan kana zama a (ko, idan kasuwanci, babban wurin kasuwancin ka yana cikin) Australia, kana yarjejeniyar kwangila tare da Microsoft Pty Ltd, 1 Denison St, North Sydney, NSW 2060, Australia kuma idan kana zama a (ko, idan kasuwanci, babban wurin kasuwancin ka yana a) New Zealand, kana yarjejeniyar kwangila tare da Microsoft New Zealand Limited, Level 5, 22 Viaduct Harbour Avenue, PO Box 8070 Symonds Street, Auckland, 1150 New Zealand. Domin Ayyuka na kyauta da kuma na biyan kuɗi, dokokin Jihar Washington ne suke gudanar da fassarar waɗannan Sharuɗɗa da kuma diyyar ketarsu, ko me ne saɓani na aƙidun dokoki. Dokokin ƙasar inda muka tura Ayyukanka ne suke gudanar da duk sauran diyya (da suke haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci, da kuma diyya kan lahani). Kowane saɓani da yake taso ko da ya shafi waɗannan Sharuɗɗan Ayyukan bayan ga Skype, da ya haɗa da duk wata tambaya dangane da kasancewarsu, inganci, ko ƙarewa, za a tura shi ne zuwa kuma a warware daga ƙarshe ta wajen sulhu a Singapore gwargwadon Dokokin Sulhu na Cibiyar Sulhun Ƙasashen Waje ta Singafor (SIAC), wanda ake ɗauka na haɗe dokokinta ta mahangi a cikin wannan yankin jumla. Kotun Sauraron Ƙarar za ta ƙunshi alƙali ɗaya da Shugaban SIAC zai naɗa. Harshen sulhun zai zama Ingilishi. Hukuncin da alƙalin ya yanke shi zai zama na ƙarshe, abun ɗaurewa, da kuma ba za a daɗa tayar da ita ba, kuma ƙila a yi amfani da ita a matsayin samfuri na yanke hukunci a kowace ƙasa ko yanki.
- e. Japan. Idan kana zaune a cikin (ko, ko kasuwanci, ko cibiyar kasuwancinka tana cikin) Japan kuma kana amfani da wasu ɓangarori na Sabis-sabis (kamar Bing da MSN), kana yin kwangila ne tare da Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. Idan ka biya don amfani da wani ɓangare na Sabis-sabis ɗin, kana kwangila ne tare da Microsoft Japan Co., Ltd (MSKK), Shinagawa Grand Central Tower, 2-16-3 Konan Minato-ku, Tokyo 108-0075. Don Ayyuka na kyauta da na biyan kuɗi, dokokin Jafan ne suke gudanar da waɗannan Sharuɗɗa da kuma kowaɗane matsaloli da suke taso daga ko dangane da su ko Ayyukan. Kai da mu mun yarda da dokar ta musamman mara canzawa da kuma wuri na Kotun Gundumar Tokiyo domin duk saɓani da yake taso daga ko dangane da waɗannan Sharuɗɗa ko Ayyukan.
- f. Jamhuriyar Korea.
- i. Idan kana da zama a (ko, idan wani kasuwanci ne, ainihin wuirnka na kasuwanci yana a) Jamhurriyar Koriya, kuma kana yin amfani da kashe-kashe na kyauta na Sabis-sabis (kamar su Bing da MSN) kana yin kwangila da Microsoft Corporation, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052 Ƙasar Amurka. Idan ka biya kuɗi don yin amfani da wani kashi na Sabis-sabis, kana yin kwangila da Microsoft Korea, Inc., 12th Floor, Tower A, The K-Twin Tower, Jongro 1 gil 50, Jongro-gu, Seoul, Jamhurriyar Koriya, 03142. Don Sabis-sabis na kyauta da na biyan kuɗi, dokokin Jamhurriyar Koriya ne suke gudanar da waɗannan Sharuɗɗa da kuma kowane batu da ke tasowa daga ko dangane da su ko Sabis-sabis ɗin. Kai da mu mun yarda da dokar ta mara-musamman mara canzawa da kuma wuri na Kotun Gundumar ta Tsakiya ta Seoul domin duk saɓani da yake taso daga ko dangane da waɗannan Sharuɗɗa ko Ayyukan.
- ii. Idan kana da zama a Jamhurriyar Koriya, ta doka, ƙila kana da wasu haƙƙoƙin da ba za a iyakance ta wani kwangila kamar waɗannan Sharuɗɗa. Ba a yi niyyar waɗannan Sharuɗɗa su ƙayyade waɗancan haƙƙoƙi ba ko don ƙayyade basusukan Microsoft da aka kafa ta doka. Duk da koma da yake saɓa da yake ƙunshi a nan, za a zartar da waɗannan Sharuɗɗa har iyakar da doka ta ba da izinin. Za a yi kowane canji ga waɗannan Sharuɗɗa (da kuma kowane canji a cikin kuɗin da za a caji don Ayyukan rajista masu maimaitawa, idan ya shafa) gwargwadon buƙatun doka.
- g. Taiwan. Idan kana zama a (ko, idan kasuwanci, babban wurin kasuwan ka yana a) Taiwan, kuma kana amfani da Sabis na kaso kyauta (kamar Bing da MSN), kana yarjejeniyar kwangila tare da Kamfanin Microsoft, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. idan ka biya don amfani da Sabis na kaso, kana yarjejeniyar kwangila tare da Microsoft Taiwan Corp., 18F, No. 68, Sec. 5, Zhongxiao E. Rd., Xinyi District, Taipei 11065, Taiwan. Domin Ayyuka na kyauta da na biyan kuɗi, dokokin Taiwan ne suke gudanar da waɗannan Sharuɗɗa da kuma kowaɗane matsaloli da suke taso daga ko dangane da su ko Ayyukan. Don ƙarin bayani dangane da Microsoft Taiwan Corp., daure a duba shafin yanar-gizo da aka samar da shi ta wajen Ma'aikatan Harkokin Tattalin Arziki R.O.C. (https://gcis.nat.gov.tw/mainNew/). Kai da mu mun naɗa mara canzawa Kotun Gundumar Taipei a matsayin kotun na farkon misalin samun hukunci bisa kowane saɓani da yake taso daga ko dangane da waɗannan Sharuɗɗa ko Ayyukan, har iyakar mafi iyakance da dokokin Taiwan suke ba da izinin.
Wataƙila dokokin mai amfani na gida ɗinka za su buƙatar wasu dokoki na gida su gudanar da ko su ba ka damar warware saɓani a wani taro dabam duk da waɗannan Sharuɗɗa. Idan haka ne, zaɓen doka da kuma samarwar taro a cikin sashe na 10 za su sanya har yadda dokokin mai amfani na gida suka bari.
Yarjejeniyoyi
11. Yarjejeniyoyi.
- a. MICROSOFT, DA KUMA RASSANMU, MASU SAYARWA, MASU RARRABAWA, DA KUMA MASU SAYARWA, MAKE NO WARRANTIES, EXPRESS OR IMPLIED, GUARANTEES OR CONDITIONS WITH RESPECT TO YOUR USE OF THE SERVICES. KA FAHIMCI CEWA AMFANI DA SABIS-SABIS ƊIN ZAƁINKA NE KUMA CEWA MUN SAMAR DA SABIS-SABIS ƊIN NE “KAMAR YADDA SUKE” TARE DA DUK LAHANONI” DA KUMA “KAMAR YADDA YAKE SAMUWA.” MICROSOFT BA TA BAYAR DA TABBACI KO DAIDAITO KO AIKI CIKIN LOKACI NA SABIS-SABIS ƊIN BA. ƘILA KANA DA WASU HAKKOKI A ƘARƘASHIN DOKAR ƘASARKA. BA WANI ABU A CIKIN WAƊANNAN SHARUƊƊA DA YAKE NUFIN SHAFAR WAƊANNAN HAKKOKI, IDAN AKWAI SU. KA AMINCE CEWA KWAMFUTA DA SISTEM NA SADARWA BA WAI BA SA SAMUN MATSALA BA, A WASU LOKUTA SUKAN SAMU MATSALA. BA MA BAYAR DA TABBACIN CEWA DUK SABIS-SABIS ƊIN BA ZA SU KATSE BA, CIKIN LOKACI, TSARO, KO BA ZA SU SAMU MATSALA BA KO BA ZA A IYA ASARAR ƘUNSHIYA BA, HAKA NAN BA MA KUMA BAYAR DA TABBACIN DUK WANI HAƊI ZUWA KO WATSAWA DAGA KWAMFUTAR.
- b. ZUWA GA ƘUREWAR DA DOKAR ƘASARKA TA BAYAR, BA MA CIRE DUK WASU YARJEJENIYOYI DA AKA SANYA, DA SUKA HAƊA DA NA KASUWANCI, GAMSUWA, INGANCI, DACEWA DA WATA BUƘATA, JAJIRCEWAR AIKI, DA KUMA RASHIN-KETA DOKA.
- c. Ga masu amfani da suke zaune a Australia: Kayyakinmu da kuma sabis suna zuwa ne da tabbatoci na cewa ba za a cire su a ƙarƙashin Dokar Masu Amfani da Kaya ta Autiraliya. Don manyan kasawa tare da sabis ɗin, ka cancanci:
- soke kwangilar sabis ɗin tare da mu; da kuma
- don nemn ramuwa ga wani ɓangare da ba a yi amfani da shi ba, ko don biyan diyya saboda raguwar darajarta.
Haja nan ka cancanji zaɓar wata ramuwa ko musanye na manyan kayayyaki nda suka kasa. Idan wata kasawa ta auku da kayayykin ko wani sabis ba ya haifar da wata babbar kasashi, ka cancanci samun gyara matsalar cikin lokaci. Idan bai gama ba ka cancanci ramuwa na kayayyakin da kuma soke kwangilar don sabis ɗin da kuma samun ramuwa don duk wani ɓangare da ba a gani ba. Haka nan ka cancanci ramuwar kuɗi da za a ba ka ga duk wata asara da ba a hange ta ba zuwa lalacewa daga kasawa a cikin kayan da kuma sabis-sabis.
- d. Ga masu amfani da suke zaune a New Zealand, ƙila kana da hakkoki na shari’a a ƙarƙashin Dokar Garanti ta Masu Amfani da Kayayyaki ta, kuma babu wani abu a cikin waɗannan Sharuɗɗa da zai shafi waɗannan hakkoki.
Iyakacin Ɗaukar Nauyi
12. Iyakacin Ɗaukar Nauyi.
- a. Idan kana da wata hujja na karɓar diyya (da ya haɗa da keta waɗannan Sharuɗɗa), zuwa iyakar da dokar da ta shafa ta ƙyale, ka yarda cewa magancewar ita ce maidowa, daga Maicrosoft duk ko duk rassansa, masu sake sayarya, masu rarrabawa, Aikace-aikacen Wasu da kuma masu samar da Sabis-sabis, da dillalai, diyya ta kai tsaye wanda yake daidai da kuɗin Sabis-sabis ɗinka na watan da asarar ko keta dokar ta auku (ko har zuwa Dalar Amurka $10.00 idan Sabis-sabis ɗin kyauta suke).
- b. Har iyakanci da dokar da take shafa take yarda da, ba za ka iya dawo duk wata (i) babbar lalacewa ko asara ba; (ii) asarar anihin riba ko wadda ake sa-rai (kai tsaye ko kaikaice); (iii) asarar ainihin kuɗin shiga ko wanda ake sa-rai (kai tsaye ko kaikaice); (iv) rasa kwangila ko kasuwanci ko sauran asarori ko lalacewa da suka taso sanadiyyar amfani da Sabis-sabis da kake yi a matsayi wanda ba keɓaɓɓe ba; (v) lalacewar musamman, ko a kaikaice, lalacewa ko asarar da ba ta gangan ba; kuma (vi) zuwa wa’adin da doka ta ƙyale, asarori ko lalacewa na kai tsaye fiye da wanda aka bayyana a sashe na 12.a. da ke sama. Waɗannan iyakoki da kuma wariya sun shafi idan ba a biya ka cikakkiyar diyar wannan warwarewa ba na duk wata asara ko kasa ainihin dalilinsa ko idan mun sani ko ba mu sani ba game da yiwuwar lalacewar. Zuwa wa’adin da doka ta ƙyale, waɗannan iyakoki da wariya da aka sa ga komai ko duk wasu koke-koke da suka shafi waɗannan Sharuɗɗa, Sabis-sabis ɗin, ko manhaja da ta shafi Sabis-sabis ɗin.
- c. Microsoft ba ta da alhaki ko ɗaukar nauyi ga duk wata kasawa ta aiki ko jinkiri wajen aiwatar da wajibcinsa a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa zuwa iyakar kasawa ko jinkiri da ya auku da ya fi ƙarfin hakkin Microsoft (misali taƙaddama kan biyan lada, dalilai daga Ubangiji, yaƙi ko aikin ƴan ta’adda, lalacewa mai cutarwa, haɗari ko bin duk wata doka ko dokar gwamnati da aka saka). Microsoft za yi ƙoƙarin taƙaita sakamako na ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan aukuwa don aiwatar da wajibcinsa da ba a shafe su ba.
Sharuɗɗan Keɓaɓɓen-Sabis
13. Sharuɗɗan Keɓaɓɓen-Sabis. Sharuɗɗan kafin da kuma bayan sashe na 13 an sanya su gaba ɗaya ga duk Sabis-sabis. Wannan sashe ya ƙunshi sharuɗɗan keɓɓɓen-sabis da suke ƙari ne ga sharuɗɗa na gaba ɗayan. Waɗannan sharuɗɗa suna aiki ne idan akwai wasu saɓani ga sharuɗɗa na gaba ɗayan.
Xbox
- a. Xbox.
- i. Amfani na kai da ba na Kasuwanci ba. Sabis na kan intanet na Xbox ("Hanyar Sadarwar Xbox"), Wasannin Xbox Game Studios (ciki har da Mojang Games) (https://www.xbox.com/xbox-game-studios), manhajoji biyan kuɗi (misali, tayin sabis na biyan kuɗi na Xbox Game Pass), sabis (misali, Xbox Cloud Gaming), da ƙunshin bayani da Microsoft da bayar (a haɗe, "Sabis na Xbox") na keɓaɓɓen amfanin ka ne da wanda ba na kasuwanci ba.
- ii. Ayyuka na Xbox. Idan ka shiga cikin Xbox don karɓar Sabis na Xbox, bayani game da wasan ka, za a bi sawun ayyuka da amfani da wasanni da Sabis na Xbox kuma a raba tare da wasu masu amfani, ciki har da masu haɓaka wasanni da masu wallfa, don Microsoft ya iya isar da Sabis na Xbox da kuma don wasu su yi aiwatarwar sabis da wasanni wanda ba Microsoft ba. Bugu da ƙari, Idan aka samu damar shiga Xbox ta na'urorin wasu ko dandamali, ana iya bin sawun bayani game da wasan ka, ayyuka da amfani da wasanni da Sabis na Xbox kuma a raba ta na'urar wasu da dandamali, bisa ga sharuɗɗan kowane wasu kamfani da tsarin tsare sirri. Idan ka shiga cikin wani dandamali ko na'ura tare da asusun ka na Microsoft ko haɗa asusun Microsoft ɗinka da waɗannan dandamalim ko na'urori don samun dama ga Sabis na wanda ba Microsoft ba (alal misali, mai wallafa wasa wanda ba Microsoft ba ko Manhajojin Wasu Kamfani da Sabis), ka amince cewa: (a) Microsoft na iya raba asusu mai iyaka da bayani da ke da alaƙa da amfani (ciki har da ba tare da iyakancewa na gamertag, gamerscore, tarihin wasa, bayanan amfa da jerin abokai) tare da wannan kamar yadda aka bayyana cikin Bayanin Sirri na Microsoft, da (b) Idan saitunan sirri na Xbox ɗinka ya bayar da dama, wannan zai iya samun dama ga Ƙunshin bayanin ka daga sadarwar wasa na ciki ko wasu manhajoji da ka yi amfani da su da ka shiga cikin asusun ka tare da wannan ɗin. Haka nan, idan saitunan tsare sirri na Xbox ɗinka ya ƙyale, Microsoft za ta iya wallafa sunaka, tambarin wasa, hoton ɗan wasa, take, abata, gajeren bidiyon ɗan-wasa da kuma wasanni da ka buga cikin sadarwa da mutanen da ka ƙyale. Idan ka kunna saitunan tsaro na takamammen Iyali na Xbox, waɗannan saitunan sanye a na'urar Xbox, Wasan Gajimare na Xbox, da manhajar Xbox akan PC ko na'urar tafi da gidanka, amma ba lallai a sanya ga wasannin Xbox Game Studios ba ko sabis da aka samu dama ko aka kunna akan wasu na'urori ko dandamali. Don tabbatar da kwarewar wasa mai tsaro don iyalinka, daure ka duba saitunan iyaye akan waɗannan sauran na'urori da dandamali.
- iii. Ƙunshin bayanin ka. A zaman wani ɓangare na gina al’ummar Sabis-sabis ɗin Xbox, kana ba wa Microsoft, rassanta da kuma ƙananan masu lasisi haƙƙi na kyauta da kuma na gamegari, don yin amfani da, gyara, sake sarrafa, rarraba, da kuma nuna Ƙunshiyarka ko sunanka, tambarin mai wasa, take, ko avatar da ka aika don wasu Sabis-sabis ɗin Xbox.
- iv. Manajojin Wasa. Wasu wasanni suna iya yi amfani da manajojin, jakadu, ko masu saukar da wasa. Manajojin wasa da kuma masu shirya wasa ba su ne masu magana da yawun Microsoft da suke da izini ba. Ba lallai ra'ayoyinsu ya fayyace waɗannan na Mcrosoft ba.
- v. Yara da Xbox. Idan kai ƙaramin yaro ne mai yin amfani da Ayyuka na Xbox ɗin, iyayenka ko mai riƙonka zai iya samun dama a kan abubuwa da dama na asusunka kuma ƙila ya sami rahotanni game da yadda kake amfani da Ayyuka na Xbox. Waɗannan siffofin na musamman ne ga Sabis na Xbox kuma ba lallai ya tura zuwa wasu na'urori ko dandamali ba.
- vi. Kuɗin Wasa ko Abubuwan Gani. Ayyuka na Xbox suna iya haɗa da kuɗin wasa, mara ainihi (kamar zinare, tsabar kuɗi, ko makuna) wanda za a iya saye daga ko a madadin Microsoft ta yin amfani da ainihin kuɗi idan ka kai shekarun “balaga” a inda kake zaune. Haka kuma Ayyuka na Xbox suna iya haɗa da abubuwa ko kayayyaki na dijital mara ainihi wadda za a iya saye daga ko a madadin Microsoft ta yin amfani da ainihin kuɗi ko ta yin amfani da kuɗin wasa. Kuɗin wasa ko kayayyaki mara ainihi ba za a iya fanshe su don ainihin kuɗi ba, kayayyaki da kuma sauran abubuwa na darajar kuɗi daga Microsoft ko wani daban. Fiye da taƙaitacce, keɓaɓɓe, wanda za a iya sokewa, wanda ba za a iya turawa ba, lasisi wanda ba za a iya sake bayar da ɗan lasisi ba na yin amfani da kuɗin wasa da kuma kayayyaki mara ainihi a cikin Ayyuka na Xbox kawai, ba ka da haƙƙi ko take a cikin ko zuwa ga irin wannan kuɗin wasa ko kayayyaki mara ainihi da suke bayyana ko fitowa a cikin Ayyuka na Xbox, ko wasu sauran halaye da suka danganta da amfani da Ayyukan ko da aka ajiye a cikin Ayyuka na Xbox. Wataƙila Microsoft ya iya a kowane lokaci daidaita, sarrafa, gyara da kuma/ko fitar da kuɗin wasa da kuma ko kayayyaki mara ainihi da aka danganta da kowane wasan ko manhajar Xbox ɗaya ko fiye da haka yadda ta gan dama a cikin ra'ayinsa kaɗai ga iyaka mafi iyakace da ake yarda da shi ta wajen dokokinka na gida.
- vii. Sabuntawan Sofwaya. Don kowace na'ura da take iya yi haɗi da Ayyuka na Xbox, ta yiwu mu bincika sigar sofwaya na masarrafin Xbox ɗinka kai tsaye ko sofwaya na manhajar Xbox sanna kuma a sauke masarrafin Xbox ko sabuntawan sofwaya na manhajar Xbox ko canje-canjen tsari, da suka haɗa da waɗanda suke hana ka samun iso ga Ayyuka na Xbox, ta amfani da wasannin Xbox ko manhajojin Xbox marasa izini, ko ta amfani da manyan na’urorin hadwaya marasa izini tare da wani masarrafin Xbox.
- viii. Sofwaya na Cuta da Lahanta. Don kowace na’ura da za ta iya yi haɗi da Ayyuka na Xbox, muna iya bincika kai tsaye na’urarka don hadwaya da ba a ba wa izini ba ko sofwaya da take ƙarfafa cuci ko lahani wajen keta Dokar Ɗa’ar Ma'aikata ko waɗannan Sharuɗɗa, da kuma sauke sabuntawan sofwaya na manhajar Xbox ko canje-canjen tsari, da suka haɗa da waɗanda suke hana ka samun iso ga Ayyuka na Xbox, ko daga yin amfani da hadwaya ko sofwaya marar izini da take ƙarfafa cuci ko lahani.
- ix. Ƙarin Sharuɗɗa da Ƙa'idoji na Rajista. Rajistocin Ayyuka na Xbox suna gana wa ƙarin sharuɗɗa da ƙa'idoji da aka bayyana a cikin Sharuɗɗan da Ƙa'idojin Rajistocin Xbox | Xbox (https://www.xbox.com/legal/subscription-terms).
- x. Rajistocin Sabis na Xbox Mara Aiki. Ya yiwu Microsoft ta kashe cajin kuɗi mai maimatawa da kuma tsayar da caje-cajen masu maimatawa a cikin wasu takamaiman ƙasashe idan ba ka yin amfani da rajistarka ta Ayyuka na Xbox don wani tsawon lokaci ba. Microsoft zai samar maka da sanarwa kafin ya kashe cajin kuɗi mai maimatawa. Don ƙarin bayani, da ya haɗa da tsawon lokaci na rashin aiki, duba FAQ na rashin aiki na rajista | Tallafin Xbox (https://support.xbox.com/en-GB/help/subscriptions-billing/manage-subscriptions/xbox-subscription-inactivity-policy).
- xi. Ƙarin yarjejeniyoyin lasisi da kuma dokokin da'ar aiki na mai amfani. Wasu Sabis-sabis na Xbox na iya samun nasu sharuɗɗan amfani da kuma dokokin da'ar aiki.
Wurin Adana
- b. Wurin Adana. "Wurin Adana" yana nufin wani Sabis da yake ba ka damar yin burauzi, saukewa, saye, da kimantawa da kuma yin bitar manhajoji (kalmar “manhaja” ta haɗa da wasanni) da kuma sauran ƙunshiyar dijital. Waɗannan sharuɗɗa sun haɗa da amfani da wasu Wuraren Adana da Microsoft ko rassanta suka mallaka ko sarrafawa (da ya haɗa, amma bai taƙaita ga, Wurin Adana na Office, Wurin Adana na Microsoft a kan Windows da kuma Wurin Adana na Microsoft a kan Xbox ba). “Wurin Adana na Office” yana nufin wani Wurin Adana na samfurorin Office da kuma manhajoji na Office, Microsoft 365, SharePoint, Exchange, Access da kuma Project (sigogin 2013 ko gaba), ko duk sauran kayayyaki da aka sa wa alama Wurin Adana na Office. “Wurin Adana na Microsoft a kan Windows” yana nufin wani Wurin Adana, wanda Microsoft ko rassanta suka mallaka da kuma sarrafawa, don na’urorin Windows kamar su waya, kwamfuta, ƙaramar kwamfutar hannu, ko duk sauran kayayyaki da aka sa wa alama Wurin Adana na Microsoft ake samun iso gare su a kan na’urorin Windows kamar su waya, kwamfuta, ko ƙaramar kwamfutar hannu. “Microsoft Store a kan Xbox” yana nufin wani Wurin Adana, wanda Microsoft ko rassanta suka mallaka da kuma sarrafawa don konsololi na Xbox, ko duk sauran kayayyaki da aka sa wa alamar Microsoft Store kuma da aka samar da su a kan wani konsol na Xbox.
- i. Sharuɗɗan Lasisi. Za mu gano mawallafin kowace manhaja da take samuwa cikin Wurin Adana mabambanta. Sai dai idan an samar da wasu sharuɗɗan lasisi daban tare da manhajar, Sharuɗɗan Lasisin Daidaitacciyar Manhaja ("SALT") a ƙarshen waɗannan Sharuɗɗa wata yarjejeniya ce tsakaninka da kuma mawallafin manhajar wanda ya shirya sharuɗɗan lasisin da aka saka a kan wata manhaja da ka sauke ta hanyar duk wani Wurin adana da Microsoft ko rassanta suke sarrafawa (ban da Wurin Adana na Office). Don ganewa, waɗannan Sharuɗɗa sun shafi amfani, da kuma sabis-sabis da Sabis-sabis na Microsoft ya samar. Sashe na 5 na waɗannan Sharuɗɗa haka nan ya shafi Sabis-sabis da Manhajoji na Wasu da aka samu ta wata hanyar wani Wurin adana. Manhajoji da aka sauke ta hanyar Wurin Adana na Office ba sa ƙarƙashin kulawar SLT kuma suna da keɓɓun sharuɗɗan lasisi da aka sanya.
- ii. Sabuntawa. Microsoft za ta bincika da kuma sauke sabuntawa ta otomatik zuwa manhajojinka, koda idan ba ka shiga zuwa Wurin Adana mabambanta ba. Za ka iya sauya Wurin Adana ko saitunan sistem ɗinka idan ka fi son kada ka karɓi sabuntawar otomatik ga Manhajoji na Wurin Adana. Amma, ya yiwu a sabunta wasu manahajojin Wurin Adana Office da ake sauka cikakke ko wani ɓangare a kan layi a kowane lokaci ta wajen mai ƙira na manahajar kuma ya yiwu ba za a buƙata izininka don sabunta ba.
- iii. Ƙimance-Ƙimance da Bitoci. Idan ka kimanta ko ka yi bitar wata manhaja a cikin Wurin Adana, ƙila ka sami wani imel daga Microsoft da ya ƙunshi ƙunshiyar daga mawallafin manhajar ko Kayan Dijital. Kowane irin wannan imel yana zuwa daga Microsoft; ba ma raba adireshin imel ɗinka tare da mawallafan manahajoji ko Kayayyakin Dijital da ka samu ta hanyar Wurin Adana.
- iv. Gargaɗin Kariya. Don gujewa rauni, rashin jin daɗi, ko matsalar ido da yake yiwuwa, ya kamata ka ɗauki hutu lokaci-lokaci daga yin amfani da wasanni da sauran manahajoji, musamman idan kana jin wani ciwo ko kasala a sanadiyyar amfanin. Idan ka ɗanɗana rashin jin daɗi, ɗauki hutu. Rashin jin daɗi yana iya haɗa jiwa na tashin zuciya, ciwon motsi, hajijiya, yamutsi, ciwon kai, gajiya, matsalar ido, ko ƙeƙasattun idanu. Yin amfani da manahajoji yana iya ɗauka maka hankali da kuma tsare muhallanka. A kauce haɗarorin tuntuɓe, matakala, silin da ya yi ƙasa, abubuwan aras ko masu kima da suke iya lalace. Wani kason mutane ƙasan ƙila su iya fuskantar kamuwa a yayin kallon wasu hotuna kamar wuta mai walƙiya ko samfurorin da ƙila za su bayyana a cikin manhajojin. Ko da mutane waɗanda ba su da tarihin kamuwa ƙila su sami wani hali da ba a bincika ba da zai haddasa waɗannan kamuwa. Alamomi da suka haɗa da jiri, matsalar gani, kumburi, kakarewa ko motsa laɓɓa, ruɗewa da kuma rasa nutsuwa, ko farfaɗiya. Dakatar da amfani nan-da-nan ka kuma tuntuɓi likita idan ka fuskanci ɗaya daga cikin waɗannan alamomi, ko ka tuntuɓi likita kafin amfani da manhajar idan ka taɓa fuskantar alamomi da aka dangata su da kamuwa. Iyaye za su kula da amfani da ƴaƴansu suke yi da manhajojin don alamomi na kamuwa.
Siffofin Iyali na Microsoft
- c. Siffofin Iyali na Microsoft. Iyaye da yara suna iya yin amfani da fuskokin iyali na Microsoft, da suka haɗa Kariyar Iyali na Microsoft don gina aminci dogara da wata fahimtar juna kan waɗanne halaye, shafukan yanar gizo, manahajoji, wasanni, wurare na zahiri, da kuma kashe kuɗi da suka dace a cikin iyalinsu. Iyaye suna iya ƙirƙirar wani iyali ta zuwa https://account.microsoft.com/family (ko ta bin umurnu a kan na’urorin Windows ko na’urar Xbox ɗinsu) da kuma gayyaci yara ko sauran iyaye don shiga. Akwai fuskoki da dama da suke samuwa ga mambobin Iyali, saboda haka ka yi bitar bayanin da ka samar a hankali a lokacin da kake yarda ka ƙirƙiri ko shiga wani iyali da kuma a lokacin sayen Kayayyakin Dijital don samun iso na iyali. Ta ƙirƙira ko shiga wani iyali, ka nuna cewa za ka yi amfani da iyali ta bin manufarsa kuma ba za ka yi amfani da shi a cikin wata hanya marar izini da ta saɓawa doka don samun iso ga bayanan wani ba. Fuskokin Microsoft Family abubuwa da aka ware ga Sabis-sabis na Microsoft ne kuma ba a iya gusar da su zuwa wasu dandaloli ba. Alal misali, sanya saitunan takamammen Tsaro na Iyali na na'urar Xbox, Wasan Gajimare na Xbox, da manhajar Xbox akan PC ko na'urar tafi da gidanka, amma ba lallai a faɗaɗa zuwa ga wasannin Xbox Game Studios ba ko sabis da aka samu dama ko aka kunna akan wasu na'urori ko dandamali. Don tabbatar da kwarewar wasa mai tsaro don iyalinka, daure ka duba saitunan iyaye akan waɗannan na'urori da dandamali.
Aika saƙo na Rukuni
- d. Aika saƙo na Rukuni. Iri-irn ayyukan Microsoft suna bari ka aika saƙo zuwa ga wasu ta hanya murya ko SMS ("saƙonni"), da kuma/ko barin Microsoft da masu dangantaka da Microsoft yake sarrafa su aika maka ko ƙarin sauran masu amfani irin waɗannan saƙonni a madadinka. IDAN KA UMURCI MICROSOFT DA KUMA MASU DANGANTAKA DA MICROSOFT YAKE SARRAFA SU AIKA MAKA KO MA WASU IRIN WANNAN SAƘONNI, KANA NUNA KUMA KA TABBATAR MANA CEWA KAI DA KUMA KOWANE MUTUM DA KA UMURCE MU MU AIKA SAƘO YA YARDA YA KARƁI IRIN WAƊANNAN SAƘONNI DA KUMA SAURAN SAƘONNI RUBUTU NA HUKUMA MASU ALAƘA DAGA MICROSOFT DA KUMA MASU DANGANTAKA DA MICROSOFT YAKE SARRAFA. "Saƙon rubutu na hukuma" saƙonnin cinikaya na lokaci-lokaci ne daga wani sabis na Microsoft, da ya haɗa amma bai taƙaice a wani "saƙon maraba" ko umurnu a kan yadda ake tsai da karɓowa saƙonni. Kai ko mambobin rukuni wanda ba ya so ya karɓi irin waɗannan saƙonni ba kuma yana iya fita daga karɓowa ƙarin saƙonni daga Microsoft ko masu dangantaka da Microsoft yake sarrafa a kowane lokaci ta bin umurnun da aka samar da. Idan ba ka so ka karɓi irin waɗannan saƙonni ko hallara cikin rukunin ba kuma, ka yarda da cewa za ka fita ta hanyar umurnun da aka samar da ta wajen shiri ko aiki da ya shafa. Idan kana da dalili don amince cewa wani mamba na rukuni ba ya so ya karɓi iri waɗannan saƙonni ko hallara cikin rukunin ba kuma, ka yarda a cire su daga rukunin. Haka kuma ka nuna da kuma tabbatar mana cewa kai da kuma kowane mutum da ka umurce mu mu aika ma saƙo ya gane cewa kowane mamba na rukuni yake ɗauka nauyin kuɗin kowane saƙonni da aka iso ga ta wajen kamfanin sadarwa ɗinsa ko ɗinta, da ya haɗa kowane caje-cajen saƙonni na ƙasasshe waje da suke iya shafa a lokacin da ake watsar da su daga lambobin dogara da US.
Skype, Ƙungiyoyin Microsoft, da GroupMe
- e. Skype, Ƙungiyoyin Microsoft, da GroupMe.
- i. Sabis-sabis na Gaggawa. Akwai muhamman bambance-bambance tsakanin sabis-sabis na tarho na tafi-da-gidanka ko na waya na gargajiya da kuma Skype, Microsoft Teams, da GroupMe. Microsoft yana da taƙaitattun wajibai a ƙarƙashin dokoki, ƙa'idoji ko doka na gida ko na ƙasa don bayar da iso ga ayyuka na gaggawa, kamar kiran gaggawa na 911 ko 112 ("Ayyuka na Gaggawa") ta hanyar Skype, Microsoft Teams, da GroupMe. Kawai taƙaitattun sigogi na sofwaya na siffar Skype zuwa Waya na Skype suke iya tallafi kiraye-kiraye ga Ayyuka na Gaggawa a cikin wani taƙaitaccen adadin ƙasasshe, da kuma dangane da dandalin da aka yi amfani da shi. Za ka iya samu cikakkun bayanai game da samuwa da kuma yadda ake tsara wannan siffa a nan: https://www.skype.com/go/emergency. Idan an haɗa kiranka na gaggawa na Skype zuwa Waya, akwai buƙata ka samar da cikakkun bayanai ga ainihin wurinka don ƙarfafa ayyuka na gaggawa su ba ka amsa.
- ii. APIs ko Watsawa. Idan kana son amfani da sofwaya da samfurori na Skype dangane da abin da ya shafi watsawa, dole ne ka bi Sharuɗɗan Aiki na “Watsawar” a https://www.skype.com/go/legal.broadcast. Idan kana son yin amfani da wata farfajiyar shirin manhajar ("API") da Skype ta bayyana ko ta samar da ita, dole ne ka bi sharuɗɗan lasisi da aka sanya, waɗanda suke samuwa a www.skype.com/go/legal.
- iii. Amfani da Dokoki Bisa Adalci. Ƙila a sanya dokokin amfani bisa adalci ga amfanin da kake yi da sofwaya da samfurori na Skype. Daure a yi bitar waɗannan dokoki waɗanda aka shirya don kare daga zamba da cin mutunci kuma ƙila za su iya sa iyakoki a kan nau’i, tsawon lokaci ko yawan kiraye-kiraye ko saƙonni da ka sami damar yi. Waɗannan dokokin ba sa cikin waɗannan Sharuɗɗan ta ambato. Za ka iya samun waɗannan dokoki a https://www.skype.com/go/terms.fairusage/.
- iv. Keɓaɓɓe/Ba Na Amfanin kasuwanci Ba. Amfani da manhajar Skype da samfura na keɓaɓɓen amfanin ka da wanda ba na kasuwanci ba. An ba ka damar amfani da Skype a wurin aiki don sadarwar kasuwancinka na kanka.
- v. Lambar Skype/Skype Je Zuwa: Idan Microsoft ya samar maka da Lambar Skype ko lambar Skype Je Zuwa, ka amince cewa ba mallaki lambar ka ba ko kana da damar ajiye wannan lambar har abada. A wasu ƙasashe, za a iya sanya lamba yana samuwa gare ka ta abokin hulɗar Microsoft maimakon Microsoft, kuma kana iya buƙatar shiga cikin yarjejeniya daban tare da wannan abokin hulɗar. Don ƙarin cikakkun bayanai a kan Lambar Skype duba https://go.skype.com/home.skype-number.
- vi. Manajan Skype. An ƙirƙiri "Asusun Mai Gudanar da Manajan Skype" kuma ka gudanar, aiki a matsayin mai gudanarwa guda na rukunin Manajan Skype kuma ba a matsayin kasuwanci da ya wanzu ba. Ana iya haɗa ɗaiɗaikun asusunka na Skype da wani rukunin Manajan Skype ("Haɗaɗɗen Asusu"). Ƙila za ka iya naɗa ƙarin masu gudanarwa ga rukunin Manajan Skype ɗinka gana wa amincewarsu ga waɗannan Sharuɗɗa. Idan ka kasafta Lambobin Skype zuwa wani Haɗaɗɗen Asusun, kai ne da alhaki na bin duk wasu buƙatu da suka danganta da zama ko wuri na masu amfani da Haɗaɗɗen Asusun ɗinka. Idan ka zaɓa a cire haɗi wani Haɗaɗɗen Asusun daga wani rukunin Manajan Skype, ba za a ɗauko kowaɗane rajistoci, Kuɗin Skype ko Lambobin Skype da aka kasafta ba kuma Ƙunshiyarka ko kaya da suka dangantaka da asusun da aka cire haɗin ba za ka iya iso ga su kuma ba. Ka amince a sarrafa kowane keɓaɓɓen bayani na Asusun masu amfani da aka ɗa bisa da duka dokokin kare bayanai da suka shafa. Za a iya dakatar da Manajan Skype ɗinka idan mambobin rukuni suka kasa bin Ƙa'idar Aiki da ke cikin wannan MSA ɗin.
- vii. Cajin Kuɗi na Skype. Duka farashin samfurorin Skype da aka biya sun haɗa da haraji da aka saka, sai dai idan an bayyana akasin haka. Cajin da ake biya na kiran wayoyi da suke wajen rajistar ya haɗa da kuɗin haɗi (da ake caja sau ɗaya ga kowane kira) da kuma farshin minti kamar yadda aka bayyana a www.skype.com/go/allrates. Za a ɗebe cajin kiran ne daga ragowar Kuɗin Skype. Ƙila Microsoft ta canza kuɗin kiranta a kowane lokaci ta sanar da wannan canji a www.skype.com/go/allrates. Za a sanya sabon farashi ga kiranka na gaba bayan an wallafa sabon farashin. Daure a duba sababbin farasoshi kafin a yi kira. Za a saka cajin kira na lokuta kira na tsagi da kuma cajin kuɗi na tsagi a cikakken sashen kira na gaba. A wasu ƙasashe, abokan hulɗa ba Microsoft na gida ne yake samar da kayayyakin biyan kuɗi na Skype kuma za a sanya sharuɗɗan amfani na abokan hulɗar ga wannan hada-hadar. Duk da haka, ƙila kana da dama, a ƙarƙashin doka da ta shafi, ga wata mayar da kuɗi, idan aka tambaya, ko wata ragowar rajista da aka farkon biya a halin da ka sauya Lambar Skype ɗinka zuwa wani mai samarwa dabam.
- viii. Kuɗin Skype. Microsoft ba ya ba da garanti cewa za ka iya amfani da ragowar kuɗin Saka kuɗi na Skype don siyayyar duka samfuran Skype da aka biya, kamar yadda samfura da aka biya za su iya canzawa daga lokaci zuwa lokaci. Idan ba ka yi amfani da Kuɗin Skype ba a tsawon kwanaki 180, Microsoft za ta saka Kuɗin Skype ɗinka a kan matsayin rashin aiki. Za ka iya sake dawo da Kuɗin Skype ta bin hanyar sake dawowa a https://www.skype.com/go/store.reactivate.credit. Idan kana da zama a Japan kuma ka sayi Kuɗin Skype daga shafin yanar gizo na Skype, jumloli biyu da suka gabata ba su shafe ka ba, kuma Kuɗin Skype ɗinka zai ƙare cikin kwanaki 180 bayan ranar sayen. Da zarar kuɗinka ya ƙare, ba za ka sami damar sake kunna shi ko amfani da shi ba. Idan asusun Microsoft a rufe yake, akan kowane dalili, duk wani Saka kuɗi na Sype dake da alaƙa da asusun Microsoft ɗinka za su ɓace kuma ba za a iya dawowa da su ba. Ba lallai a iya tuea Saka kuɗi na Skype zuwa wasu ba.
- ix. Allon Buga Lambar Kira na Skype. Za ka iya amfani da Allon Buga Lambar Kira tare da biyan kuɗi mai aiki ko Saka kuɗi na Skype bayan ritayar kwamfutar kan tebur na Skype da manhajojin waya. Allon Buga Lambar Kira samfur na Skype ne da za ka iya samun dama cikin Ƙungiyoyin Microsoft ko akan intanet ɗin.
- x. Caje-cajen Saƙo na Ƙasasshen waje. GroupMe yana amfani da lambobin US don kowane rukuni da aka ƙirƙira. Kowane saƙon rubutu da aka aika ko karɓa daga wata lambar GroupMe zai lissafa a zaman wani saƙon rubutu na ƙasasshen waje da aka aika ko karɓa daga ƙasar Amurka. Dangane da wurinka, wataƙila Microsoft Teams ya yi amfani da wata lambar waya da ake iya ɗauka a zaman wani saƙon rubutu na ƙasasshen waje. Daure ka duba da mai samarwa ɗinka don kuɗin ƙasashen waje da suka danganta.
- xi. SMS na Microsoft Teams. Mai yiwuwa Microsoft Teams ya yi amfani da lambobi dogara da Ostareliya da aka samar da su ta wajen Belgacom International Carrier Services SA, da suke da ainihin wurin kasuwancinsu a Boulevard du Roi Albert II, 27 1030, Bruxelles Baljium ("BICS"), domin saƙonni zuwa ga masu karɓa da suke da lambobin Ostareliya. Microsoft da madangancinsu ba su danganta da BICS ba.
Bing da MSN
- f. Bing da MSN.
- i. Kayayyakin Bing da MSN. Maƙalolin, rubutu, hotuna, taswirori, bidiyoyi, fileyoyin bidiyo da kuma kayayyaki na wasu da suke samuwa a kan Bing da kuma MSN, da suka haɗa da Microsoft bots, manhajoji da kuma shirye-shirye, ba na amfanin kasuwanci ba ne, don amfaninka ne kawai. Sauran amfani, sun haɗa da saukewa, kwafi ko sake rarraba waɗannan kayayyaki, ko yin amfani da waɗannan kayayyaki ko samfurori don gina samfurorinka na kanka, ana ƙyale su ne kawai musamman zuwa iyakar da Microsoft ko masu mallakar haƙƙinsu ko dokar da ta shafa ta ƙyale. Microsoft ko sauran masu riƙe haƙƙoki su ke mallaka haƙƙoƙi ga kayan da ba a bayyana ko bayarwa daga Microsoft ba, ko a ƙarƙahshin sharuɗɗan lasisis, ko ta shafawa, ko akasi.
- ii. Tawirori na Bing. Ƙila ba za ka iya amfani da hoton idon Tsuntsu ba na Amurka, Kanada, Masiko, Ƙasar New Zealand, Ostareliya ko Japan don amfani na gwamnati ba tare da wararriyar amincewarmu a rubuce ba.
- iii. Wuraren Bing. Yayin da ka samar da Bayananka ko Taka Ƙunshiya ga Wuraren Bing, kana ba wa Microsoft lasisin a ko'ina duniya mara biyan kuɗin haƙƙi don yin amfani, sake sarrafa, adana, gyara, haɗawa, ciyar da, watsar da, nuna, da kuma raba Bayananka da kuma Taka Ƙunshiya (da suke haɗa da haƙƙin mallaka ƙirar kaya a cikin Bayananka da Taka Ƙunshiya) da kuma ƙaramin lasisi ga kowane ko duk haƙƙoƙi na gaba ga wasu dabam.
Cortana
- g. Cortana.
- i. Amfani na kai da ba na Kasuwanci ba. Cortana Sabis ne na keɓaɓɓen mataimaki na Microsoft. Siffofin, sabis-sabis da kuma ƙunshiya da Cortana take samarwa (gaba ɗaya suna nufin "Ayyukan Cortana") domin kawai amfanin kanka ne amma ba amfanin kasuwanci ba.
- ii. Aiki da kuma Ƙunshiya. Cortana tana samar da siffofi masu faɗi, wasu daga cikinsu keɓaɓɓu ne. Sabis-sabis ɗin Cortana ƙila ya ƙyale ka samun iso ga sabis-sabis, bayani ko aiki da sauran Sabis-sabis na Microsoft ko Manhajoji ko Sabis-sabis na Wasu suke samarwa. Keɓaɓɓen-sabis na Sharuɗɗa na sashe na 13 haka nan ya shafi amfani da Sabis-sabis na Microsoft da ake samu ta hanyar Sabis-sabis na Cortana. Cortana tana samar da bayani ga dalilai na shirinka kawai kuma kai za ka yanke shawara a yayin bita da kuma dogara da wannan bayani. Microsoft ba ta bayar da tabbaci dogaro, samuwa ko samun sakamako cikin lokaci da Cortana ke samarwa. Microsoft ba ta da alhaki idan wata siffar Cortana ta yi jinkiri ko hana ka karɓa, bita ko aika wata sadarwa ko sanarwa, ko samun wani sabis.
- iii. Manhajoji da Sabis-Sabis na Wasu. A zaman wani ɓangare na isar da Sabis-sabis na Cortana, Cortana za ta iya shawarta da kuma taimaka maka yin hulɗa da Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu (ƙwarewar wasu ko sabis-sabis da aka haɗa). Idan ka zaɓa, Cortana za ta iya musanya bayani tare da Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu, kamar lambar zip ɗinka da kuma tambayoyi da amsoshi da Manhaja ko Sabis-sabis na Wasu suka dawo da su, don taimaka maka sabun sabis-sabis da ka buƙata. Cortana za ta iya ƙyale ka yin sayayya ta hanyar Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu ta amfani da fifikon asusun da kuma saituna da ka ƙaddamar kai tsaye da waɗannan Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu. Za ka iya cire haɗin Sabis-sabis ɗin Cortana ɗinka daga Manhajoji da Sabis-sabis na wasu a kowane lokaci. Amfani da kake yi da Sabis-sabis na Cortana don haɗi da Manhajoji da Sabis-sabis na Wasu yana ƙarƙashin sashe na 5 na waɗannan Sharuɗɗa. Mawallafan Sabis-sabis da Manhajoji na Wasu za su iya canza ko daina ci gaba da aiki ko siffa ta Sabis-sabis da Manhajoji na Wasu ko haɗewa da Sabis-sabis na Cortana. Microsoft ba ta da alhaki ko nauyi na maƙerin da ya samar da sofwaya ko fimwaya ba.
- iv. Na’urori Masu Damar Cortana. Na’urori Masu Damar Cortana samfurori ne ko na’urori da suke ƙyale samun iso ga Sabis-sabis Cortana, ko samfurori ko na’urori da suke jituwa da Sabis-sabis na Cortana. Na’urori Masu Damar Cortana sun haɗa da na’urorin wasu ko samfurori da ba mallaki, ƙira ko samarwar Microsoft ba ne. Microsoft ba ta da alhaki na na’urori da samfurori na wasu.
- v. Sabuntawan Sofwaya. Ƙila mu bincika sigar sofwayar Sabis-sabis ɗin Cortana ɗinka kai tsaye da kuma sauke sabunta sofwayar ko canza saitin ko buƙatar duk maƙeran Cortana sun ƙyale na’urori don barin sofwayar Sabis-sabis na Cortana cikin sabunta.
Manhajoji da Sabis-sabis na Microsoft 365
- h. Manhajoji da Sabis-sabis na Microsoft 365.
- i. Sharuɗɗan Amfani. Microsoft 365 Family, Microsoft 365 Personal, Microsoft 365 Basic, Sway, OneNote.com da kuma sauran manhajar ko Sabis na Microsoft 365 ko Sabis masu alamar-Office domin amfani na keɓe, mara kasuwanci ne, sai dai kana da haƙƙoƙin amfani na kasuwanci a ƙarƙashin wata yarjejeniyar dabam tare da Microsoft. Ana gudanar da amfani da manhajoji kamar su Word, Excel, PowerPoint, Outlook, OneDrive, Acces, da kuma Publisher a cikin Microsoft 365 Family, Microsoft 365 Personal, da kuma sauran manhajar ko Sabis na rajista na Microsoft ta wajen ƙarin sharuɗɗan lasisi da ya kasance a https://aka.ms/useterms tare da waɗannan Sharuɗɗa.
- ii. Ƙarin Sharuɗɗan Outlook. Outlook yana haɗa da amfani da Taswirori na Bing. Kowace ƙunshiya da aka samar da ita ta Taswirorin Bing, da suka haɗa lambobin ƙasa, ana iya kawai amfani da su a cikin kayan ta wadda aka samar da ƙunshiyar. Ana gudanar da amfani da Taswirorin Bing ta Sharuɗɗan Mai Amfani na Ƙarshe na Taswirorin Bing da ke samuwa a go.microsoft.com/?linkid=9710837 da kuma Bayanin Tsare Sirri na Microsoft da ke samuwa a go.microsoft.com/fwlink/?LinkID=248686.
Kayayyakin Dijital
- i. Kayayyakin Dijital. Ta hanyar Microsoft Groove, Finafinai da TV na Microsoft, Wuirn adana, Ayyuka na Xbox da sauran ayyuka masu alaƙa da kuma na gaba, Microsoft yana iya ba ka damar samun, saurara, duba, kunna ko karanta (yadda ya kasance) kiɗa, hotuna, bidiyo, rubutu, littattafai, wasanni, ko sauran kayayyaki ("Kayayyakin Dijital") da ƙila za ka iya samu a tsarin dijital. Kayayyakin Dijital don amfani na mallakin keɓe, shaƙatawa mara kasuwanci ne kawai. Ka yarda ba za ka sake rarraba, watsar da, yi aiki ga jama'a ko nuna ga jama'a ko gusar da kowaɗane kwafe-kwafe na Kayayyakin Dijital ba. Ana iya mallaka Kayayyakin Dijital ta wajen Microsoft ko wasu. A dukan halaye, ka fahimta kuma ka yarda da cewa haƙƙoƙinka dangane da Kayayyakin Dijital sun taƙaice ta waɗannan Sharuɗɗa, dokar haƙƙin mallaka, da kuma Dokokin Amfani da suke samuwa a https://go.microsoft.com/fwlink/p/?LinkId=723143. Ka yarda cewa ba za ka yi ƙoƙarin gyaggyara kowaɗane Kayayyakin Dijital da aka samu ta hanyar kowane daga cikin Ayyukan don wani irin dalili ba, da ya haɗa don maƙasudin sakewa kama ko canzawa mallaki ko tushen Kayayyakin Dijital ɗin. Microosft ko masu mallaka Kayayyakin Dijital suna iya, daga lokaci zuwa lokaci, cire Kayayyakin Dijital daga Ayyukan ba tare da sanarwa ba.
Ma'ajiyar Microsoft
- j. Ma'ajiyar Microsoft.
- i. Kasafin Ma'ajiyar OneDrive. Idan kana da ƙarin ƙunshiya da aka ajiye a cikin asusun OneDrive ɗinka fiye da yadda aka samar maka a ƙarƙashin sharuɗɗan sabis na rajistarka ta kyauta ko ta biyan kuɗi don Ma'ajiyar Microsoft kuma ba ka ba da amsa ga sanarwa daga Microsoft don gyara asusunka ta cirewa rarar ƙunshiya ko matsarwa zuwa wani sabon tsarin rajista mai ƙarin wurin adana ba, mun riƙe haƙƙin rufewa asusunka da kuma share ko naƙasa iso ga zuwa Taka Ƙunshiyar a kan OneDrive. Karanta ƙari game da rabon ma'aiyar Microsoft a nan (https://prod.support.services.microsoft.com/office/how-does-microsoft-storage-work-2a261b34-421c-4a47-9901-74ef5bd0c426).
- ii. Aikin Sabis na OneDrive. Dangane da halaye kamar na'urarka, haɗin intanet da kuma ƙoƙarin Microsoft don kula da aikata da mutuncin aikinsa, kana iya lokaci-lokaci ɗanɗana jinkiri wajen yin lodi ko daidaitawa ƙunshiya a kan OneDrive.
- iii. Kasafin Ma'ajiyar Outlook.com. Idan ka wuce rabon ma'ajiyar akwatinka na saƙo na Outlook.com ko rabon ma'ajiyarka ta Microsoft da aka samar maka a ƙarƙashin wata rajista ta kyauta ko ta biyan kuɗi, ba za ka iya aika ko karɓi saƙonni ba har sai ka cire yawan ƙunshiyar ko matsa zuwa wata sabuwar rajista da ke da isasshiyar ma'ajiya. Idan ka gaza cire yawan ƙunshiyar ko samun isasshiyar ƙarin ma'ajiya bayan da ka karɓi sanarwa daga wajen Microsoft, muna mallaka haƙƙin goge ko kashe damar da kake da ita ga Taka Ƙunshiyar. Karanta ƙari game da rabon ma'aiyar Microsoft a nan (https://prod.support.services.microsoft.com/office/how-does-microsoft-storage-work-2a261b34-421c-4a47-9901-74ef5bd0c426).
Rama Kuɗi na Microsoft
- k. Rama Kuɗi na Microsoft. Shirin Rama Kuɗi na Microsoft ("Rama Kuɗi") na ba wa abokan ciniki na Microsoft damar samun rama kuɗi a lokacin da suke yin saye-saye tare da masu kiri da suka shiga shirin ta yin amfani da wasu samfurori da kuma sabis-sabis na Microsoft kamar Bing.com da Microsoft Edge. Idan aka yi rajista da Rama Kuɗi ko a aka aiwatar wani tayi na Rama Kuɗi, ka yarda kuma ka amince da Sharuɗɗa da Ƙa'idoji na Rama Kuɗi (https://www.microsoft.com/bing/rebates-terms). Wasu buƙatun cancanta, ƙayyadewa, da sauran iyakanci na iya sanya ga shigarwarka a cikin Rama Kuɗi; don ƙarin bayani, duba FAQ na Rama Kuɗi (https://www.bing.com/rebates/faq).
Microsoft Rewards
- l. Microsoft Rewards.
- i. Bayani na Gamagari. Microsoft Rewards ("Shirin Lada" ɗin) kyauta ne don a shiga, kuma yana ba ka damar samun makuna ("Makuna") don wasu ayyuka da kuma don amfani da kake yi da wasu samfurori da sabis-sabis na Microsoft. Idan kana da wani asusu na Microsoft kuma kana da zama a wani Yanki da ya cancancta (da aka bayyana a ƙasa), za a maka rajista ta atomatik a cikin Shirin Lada kuma za ka fara samun Makuna nan da nan. Za ka iya soke shigarwarka a cikin Shirin Lada ɗin a kowane lokaci ta hanyar bin umarnin da ke ƙasa.
- ii. Za ka iya fansa Makunanka ta ire-iren hanyoyi ("Zaɓuɓɓukan Fansa"), da suka haɗa da wasu samfurori da kuma sabis-sabis da aka jera a kan Shafin Fansa a https://aka.ms/redeemrewards ("Lada"). Domin a cancanta fanshi Makunanka don kowane Zaɓin Fansa, dole ne ka aiwatar da asusunka na Shirin Lada da farko ("Asusun Lada") a kan Dashbod na Lada a https://rewards.microsoft.com/ ko a kan wasu sauran shafuffukan yanar-gizo da kuma shafuffuka na Microsoft. Babu kuɗin da ake biya don aiwatar da Asusunka na Lada.
- iii. Ana sanya wasu ƙayyadewa da kuma iyakoki wajen samun, fansa, da kuma sauran amfani da Makuna a cikin Shirin Lada. Domin ƙarin bayani duba sashen Lada a https://support.microsoft.com ("Tambayoyi da aka Fiye Yi").
- iv. Buƙatu. Kana buƙatar wani asusu na Microsoft mai inganci kuma dole ne ka yi zama a ɗaya daga cikin wuraren ƙasa da aka jera a cikin FAQ ("Yankuna") don aiwatar da Asusunka na Lada da kuma son samu, fansa, ko ta wata hanya dabam amfani da Makuna. Za ka iya buɗe da kuma amfani da kawai Asusun Lada guda ɗaya, ko ma idan kana da ninkin adiresoshin imel. An iyakanci kowane gida su samun Asusun Lada guda shida. An samar da Shirin Lada ɗin ne kawai don amfani na keɓe da kuma mara kasuwanci. Yin amfani da hanyar sadarwa na keɓe mara ainihi (VPN) ko sauran fasaha ko sabis da ake iya yi amfani da su don ɓoye ko dusar da wurinka na ƙasa yakan jawo sokewar Asusunka na Lada da kuma gazawar samun Makunan da ka tara.
- v. Samun Makuna. Wataƙilka a gabatar maka da damar samun Makuna don wasu ayyuka masu cancanci ("Tayi"), kamar su Bincike-bincike, Samuwa, amfani da wasu samfurori da kuma sabis-sabis na Microsoft da sauran dama daga Microsoft. Dole ne ka samun wani Asusun Lada mai aiki don cin amfani da irin wannan Tayi. Bayan an kammala buƙatu don wasu Tayi, mai yiwuwa a buƙata ka yi diyyar Makuna a kan Dashbod na Lada kafin a smun Makunan kuma a ƙara su a Asusunka na Lada. Idan aka gaza yi diyyar Makunan a cikin lokacin da aka ƙayyade ta wajen Microsoft yakan iya saka a rasa Makunan. Tayi da suke Cancanta sukan iya bambanta ta Yanki kuma sukan iya samuwa kawai don wani lokaci ko gana wa wasu iyakoki. Dole ne ka bi duk sharuɗɗa da kuma ƙa'idoji na wani takamaiman Tayi don samun Makuna da ake bayar don wancan Tayi. Wataƙila a gabatar maka da Tayi kai tsaye a kan Dashbod na Lada ko a lokacin da kake yin amfani da wasu samfurori da sabis-sabis na Microsoft. Daga lokaci zuwa lokaci, Microsoft na iya yi maka tayi ko ba ka ƙarin Makuna a da ganin damarsu kuma tare da ko ban da sanarwa gabanni, da suka haɗa da abin da Microsoft ya ƙudurci a zaman Bincike na imani mai kyau da kuma sauran hulɗawa tare da sabis-sabis na Microsoft.
- vi. Domin dalilin Shirin Lada ɗin, "Nema" wani mataki ne na wani mai amfani guda da ke shigar da rubutu da hannu don ainihin dalilin samun sakamakon nema na Bing don dalilan bincike na mai amfani ɗin; wani "Nema" bai haɗa da tambayoyi da ba a yi niyyar ba ko ba a yi amfani a su don dalilan bincike na kai da ke da imani mai kyau ba, ko wata tambaya da aka shigar da ita ta wajen bot, makuro, ko wasu hanyoyi na atomatik ko na zamba ta wani iri ba. Domin dalilan Shirin Lada, wata “Samuwa” wata hanya ce ta sayen kayayyaki ko saukewa da kuma samun lasisi na ƙunshiyar dijital kai tsaye daga Microsoft, ko a kyauta ko kuwa ta biyan kuɗi. Ba a samar da Makuna don kowace Samuwa daga Microsoft, kuma wasu ƙayyadewa sukan iya shafa.
- vii. Ƙayyadewa da Iyakoki a kan Makuna. Ana bayar da Makuna ta wajen Microsoft ga Asusun Lada na Mutum kuma ba za a iya yi tiransifar zuwa ga wani mutum ko abu dabam ba. Duk da yake da wannan, Microsoft na iya daga lokaci-lokaci a cikin ra'ayinsa da ya mallka ba ka damar (i) raba Makunanka tare da gidanka (iyakoki sukan iya shafa), (ii) bayar da Makunanka don tallafa wata ƙungiya ta agaji da aka jera a kan Shafin Fansa, ko (iii) dangane da Yankinka da kuma gana wa sauran sharuɗɗan da ƙa'idoji, don fansar da duk da wasu daga cikin Makunanka don makuna a cikin wasu sauran shirye-shiryen lada ko biyayya, da suke haɗa da shirye-shirye da ake sarrafa ta wajen Microsoft ko wasu dabam da aka ba wa izini. Makuna suna nan kuma sun kasance a kowane lokaci kadara ta Microsoft, kuma ba su kunshi kadararka ba; ba su da dajarar kuɗi, kuma mai yiwuwa ba za ka samu kowane tsabar kuɗi ko kuɗi a musayan su ba. Ana samar maka da makuna sakayya ne ta hanyar garaɓasa kawai. Ba za ka iya sayan Makuna ba. Mai yiwuwa Microsoft ya iyakance yawan Makuna ko Lada da ake iya samu ko fansa ga kowane mutum, kowane gida, ko bisa wani tsarin tsawon lokaci (misali a rana) muddin ba ka rasa amfani wajen keta kyakkyawar aniya; daure ka duba FAQ ɗin don iyakokin da suke shafa a yanzu. Sai dai wani Tayi ko Zaɓin Fansa ya bayyana dalla-dalla ta wata hanya dabam, Makuna da aka samu a cikin Shirin ba su da inganci wajen, kuma wataƙila ba za iya yi amfani da su a haɗi tare da, sauran shirin da ake bayar daga wajen Microsoft ko wasu dabam. Makuna da ba a fansa ba dangane da Asusunka na Lada za su ƙare aiki idan ba ka samu ko fansar da Makuna ba a cikin Asusunka na Lada don watanni 12 a jere.
- viii. Musaya don kyauta. Zaɓuɓɓukan musaya don kyauta zai kasance yana samuwa gare ka akan Shafin Musaya don kyauata akan wasu shafukan intanet Microsoft da shafuka. Dole ne ka samu da kuma kana da dukkan Makuna a cikin Asusunka na Lada don wani Zaɓin Fansa kafin ka iya fansar da Makunanka don wancan Zaɓin Fansa. Mai yiwuwa za a samu iyakaccen yawan wani takamaiman Lada da ke samuwa, kuma za a bayar da waɗancan Lada bisa mai farkon zuwa, za a farkon bauta. Ƙila a buƙaci ka samar da ƙarin bayani kamar adireshin wasiƙarka da kuma wata lambar tarho (ƙari ga lambar VOIP ko kira kyauta), haka kuma ƙila a umarta ka shigar da lambar hana-zamba ko ka sa hannu a ƙarin takardun doka don fansa Makuna don wasu Zaɓuɓɓukan Fansa. Da zarar ka fansar da Makunanka, ba za ka iya soke ko koma Zaɓin Fansa ɗin ba don wani mayar da Makuna sai dai a halin samfurori masu aibu ko yadda aka buƙata ta hanyar doka da suke shafa. Idan ka zaɓa wani Zaɓin Fansa da babu shi kuma ko ba ya samuwa ba don wasu dalilai, mai yiwuwa mu maye gurbin wani Zaɓin Fansa na darajar da ta dace ko mayar da makunanka yadda muka gan dama.
- ix. Microsoft na iya sabunta ko tsayar da bayar da takamaiman Zaɓuɓɓukan Fansa a kowane lokaci don kowane dalili. Mai yiwuwa wasu Zaɓuɓɓukan Fansa suna da buƙatun shekara ko cancancin Yanki, ko sauran sharuɗɗa ko ƙa'idoji a yayin fansar da su ko amfani da su. Za a haɗa kowane ire-iren buƙatun ko ƙa'idoji a cikin tayin fansa mai muhimmanci. Kai ne da alhaki ga duk haraji na tarayya, jiha da kuma na gida da kuma sauran biyan kuɗi na karɓa da kuma amfani da Zaɓin Fansa ɗin. Za a turo Lada ta hanyar saƙon imel zuwa ga adireshin imel mai alaƙa da asusunka na Microsoft, domin a riƙe adireshinka na imel na kwanan nan. Ladan da ba a iya bayar da su ba za a sake bayar da su ba kuma haka nan za a rasa su. Ba za a iya sake sayar da Lada ba. Za ka iya fansa ba fiye da Makuna 550,000 a kowane shekara a cikin Shirin Lada.
- x. Sokewa Asusunka na Lada. Idan ba ka son shiga Shirin Lada ɗin ba kuma, bi umarnin a shafin fitarwa (https://rewards.microsoft.com/optout) don soke Asusunka na Lada. Idan ka soke Asusunka na Lada, za ka rasa nan da nan duk Makunan da ka samu kuma za ka rasa iyawarka ta samun sababbin Makuna a gaba. Domin a sake fara samun Makuna, dole ne ka buɗe wani sabon Asusun Lada (amma Microsoft ba zai sake sanya kowane Makuna da aka rasa a baya ba). Mai yiwuwa za a soke Asusunka na Lada (da kuma Makunan da aka rasa) idan ba ka shiga zuwa asusunka na Microsoft ba a cikin watannin 12 a jere.
- xi. Canje-canje ko Daina Shirin. Microsoft yana mallaka haƙƙoƙin canza, gyara, daina, ko soke Shirin Lada ko haka nan kowane ɓangaren a kowane lokaci, yadda suka ga dama, kuma ba sai da sanarwa a gabanni. Amma, idan an soke ko an daina Shirin Lada, za mu yi ƙoƙari masu hankali don sanar da kai ta hanyar imel da kuma a kan Dashbod na Lada da kuma don samar maka da aƙalla kwanaki 90 don fansa Makunan da ka samu, sai dai mun ƙudurci dole ne a zartar da irin wannan sokewa nan da nan don dalilan shari'a ko tsaro.
- xii. Sauran Sharuɗɗan. Microsoft yana mallaka haƙƙin soke Asusunka na Lada nan da nan, cire cancancinka daga shigarwa cikin Shirin Lada a gaba, rasa duk Makunanka da ka samu, da kuma soke ko dakatar da kowane Zaɓin Fansa da ka samu ta hanyar Shirin Lada idan Microsoft ya amince ka taɓa, zaga, ko yi zamba kowane kashi na Shirin Lada ɗin ko ka keta waɗannan sharuɗɗa. Bugu da ƙari Microsoft yana mallaka haƙƙin soke ko dakatar da kowane Zaɓin Fansa da ka samu ko ka yi ƙoƙarin samu ta hanyar Shirin Lada idan Microsoft yana ƙudurci ba ka cancanta samun wancan Zaɓin Fansa don dalilan shari'a (kamar su dokokin fita waje). Yayin da Microsoft yana yin kowane ƙoƙarin tabbatar da daidaito, kurakurai sukan iya auku lokaci-lokaci. Haka nan Microsoft yana mallaka haƙƙin don gyara irin waɗannan kurakurai a kowane lokaci, ko ma idan ya shafi Tayi na yanzu ko Makunan ko Ladan da kake jira, ka samu ko ka fansa. A halin kowane rashin daidaito ko bambanci tsakanin waɗannan sharuɗɗan Shirin Lada ko sauran bayanai da ake samu a cikin kowane kaya ko talla mai alaƙa, waɗannan sharuɗɗa za su rinjaya, gudanar, da kuma sarrafa.
Azure
- m. Azure. Amfani da kake yi da sabis na Azure yana ƙarƙashin kulawar sharuɗɗa da ƙa’idoji na wararriyar yarjejeniya wanda a ƙarƙashinta ka sami sabis-sabis ɗin, kamar yadda yake bayyana a shafin Bayanin Shari'a na Microsoft Azure a https://aka.ms/AA7z67v.
Microsoft Soundscape
- n. Microsoft Soundscape. Ka amince cewa (1) ba a zana, yi niyyar da, ko samar da Microsoft Soundscape a matsayin wata na'urar sha'anin lafiy ba, da kuma (2) ba a zana, yi niyyar da Microsoft Soundscape ta maye gurbin shawarar sha'anin lafiya mai gwani, binciken lafiya, jiyya, ko hukunci ba kuma bai kamata a yi amfani da shi don maye gurbin ko a matsayin wani abu da ya ɗauki shawara, bincike, jiyya, ko hukunci na sha'anin lafiya masu gwani ba.
Power Platform
- o. Power Platform. Amfani da kake yi da sabis na Power Platform yana ƙarƙashin kulawar sharuɗɗa da ƙa’idoji na wararriyar yarjejeniya wanda a ƙarƙashinta ka sami sabis-sabis ɗin, kamar yadda aka bayyana a shafin Bayanin Shari'a na Power Platform a Microsoft Power Platform (https://www.microsoft.com/en-us/power-platform/business-applications/legal).
Dynamics 365
- p. Dynamics 365. Ana gudanar da amfaninka da sabis na Dynamics 365 ta sharuɗɗa da ƙa'idoji ana wata yarjejeniya dabam a ƙarƙashin wanda za ka samun sabis-sabis ɗin, yadda aka bayyana a shafin Bayanin Shari'a na Dynamics 365 a Microsoft Dynamics 365 (https://www.microsoft.com/en-us/dynamics-365/business-applications/legal).
Ƙwarewar Copilot AI
- q. Ƙwarewar Copilot AI. Ana sarrafa amfani da kake samu daga Ƙwarewar Copilot AI (sai dai Copilot da ke da kariyar bayanai na kasuwanci) ta hanyar sharuɗɗan da ƙa'idoji a ƙarƙashin da ka samu waɗannan sabis-sabis yadda aka bayyana a Copilot - Sharuɗɗan Amfani (bing.com) (https://www.bing.com/new/termsofuse#content-policy) tare da waɗannan Sharuɗɗa. Idan kai wani mai amfani da Microsoft Copilot da ke da kariyar bayanai na kasuwanci, daure ka ziyarci wannan shafi don yin bitar sharuɗɗan amfani da suke shafe ka, tare da waɗannan Sharuɗɗa: https://aka.ms/BCETermsOfUse.
Sabis na AI
- r. Sabis-sabis na AI. "Sabis na AI" sabis ne ko siffofi daga ciki da ke amfani da fasahohin Basirar Wucin gadi (AI), ciki har da kowane Sabis na AI masu ƙirƙira.
- i. Babu Kwararrun Shawara. Ba a zana, yi niyyar ko a yi amfani da sabis-sabis na AI a matsayin madai don ƙwararriyar shawarar ba.
- ii. Aikin Injiniya na Juyin Kaya. Mai yiwuwa ba za ka iya yi amfani da sabis-sabis na AI don gano wasu kayayyakin haɗi da suke da muhimmanci ga samfurori, tsare-tsaren lissafin abu, da kuma tsari. Alal misali, mai yiwuwa ba za ka iya yi ƙoƙarin ƙudurci da kuma cire nauyukan samfurori ba ko tsame kowaɗane kashe-kashe na sabis-sabis na AI daga na'urarka ba.
- iii. Tsame Bayanai. Sai dai an bayar da izinin da zahiri, wataƙila ba za ka iya yin amfani da hanyoyin tsame bayanai daga yanar-gizo ta hanyar bot, tsame bayanai da ga yanar-gizo, ko tsame bayanan yanar-gizo don tsame bayanai daga sabis-sabis na AI.
- iv. Iyakoki a kan amfani da bayanai daga Sabis-sabis na AI. Kana iya amfani da sabis na AI, ko bayanai daga sabis na AI ɗin, don ƙirƙira, horo, ko inganta (kai tsaye ko ba kai tsaye ba) kowane fasaha na AI.
- v. Amfani da Ƙunshiyarka. A matsayin ɓangare na samar da sabis-sabis na AI, Microsoft zai sarrafa da kuma ajiye shigawarka ga sabis ɗin duk da fitarwar daga sabis ɗin, don dalilan ƙura ido don da kuma hana amfani ko fitarwa na cin zali ko mai cutarwa na sabis ɗin.
- vi. Mallakin Ƙunshiyarka. Microsoft ba ya ɗauka nauyin mallakin kowace ƙunshiyar da ka samar da ita, aika, shigar da, ko miƙa zuwa ga, ko karɓa daga sabis-sabis na AI (da suke haɗa da martani da shawarwari). Akwai buƙata yi naka ƙudurci dangane da haƙƙoƙin kariyar ƙerar wani da kake da shi wajen ƙunshiya ta waje da kuma amfaninsu, yi la'akari da, tsakanin wasu abubuwa, tsarin amfani a da kuma dokoki na yanki na musamman. Kana bayar da izini da kuma wakilta cewa ka mallaka ko ta waya hanya kai ne mai sarrafa duk haƙƙoƙin ƙunshiyarka yadda aka bayyana a cikin waɗannan Sharuɗɗa da suke haɗa, ban da iyakanci, duk haƙƙoƙin da ake buƙata domin ka samar da, aika, ɗora, shigar da, ko miƙa ƙunshiyar.
- vii. Bayanan ƙunshiya. Lokacin da ka yi amfani da sabis na AI ɗin don samar da ƙunshin bayani, Microsoft zai iya ajiye bayani game da ƙunshin bayani da ke da alaƙa da wannan bayanin da ƙunshin bayani tare da takardun ƙunshin bayani. Ba lallai ka iya amfani da sabis na AI ba ko ƙirƙirar ƙunshin bayani tare da niyyar cirewa, canzawa, toshewa, ko ɓoye takardun ƙunshin bayani ko wasu hanyoyin asali, alamu, ko siginoni ko kuma yi amfani da sabis na AI don samar da ƙunshin bayani don niyyar ɓatar da wasu game da ko an samar da ƙunshin bayani ta amfani da sabis na AI.
- viii. Diyya na wasu dabam. Kai kaɗai ne kake da alhakin bayar da amsa ga diyya na kowane wani dabam dangane da Amfanin da kake yi da sabis-sabis na AI da suka dace da dokokin da suke sanya (da suke haɗa, amma ba su taƙaita da, keta haƙƙin mallaka ko sauran diyya dangane da fitarwa da ƙunshiya a lokacin Amfanin da kake yi da sabis-sabis na AI).
- ix. Iyakokin Amfani. Bayan haka bin "Ƙa'idar Aiki" da ke sama, ka amince cewa ba za ka yi amfani da sabis na AI ba, ciki har waɗanda ke yanke shawara, ko ɗaukan mataki, da kansako tare da matakai daban-daban na shiga tsakani na mutum:
- 1. Don yin shawara ko ɗaukan mataki ba tare da daidaitaccen kulawa na ɗan adam wanda zai iya samun tasiri sakamako akan kowane matsatin doka na mutum, matsayi na kuɗi, damarmakin rayuwa, damarmakin samun aiki, ko hakkin ɗan adam, ko zai iya haifar da cutarwa jiki ko hankali ga mutum ko rukunin mutane;
- 2. Don yaudara ko yaudara da niyyar boye gaskiya (misali. tallacen karya), ko amfani da dabarun sirri na fahimta (misali, na gani, ji, ko wasu siginoni da suka wuce iyakar fahimtar mutum) da nufin sarrafa ko sauya halin mutum a yanayi mai cutarwa;
- 3. Don amfani da kowane raunin mutum saboda shekarunsa, nakasa, ko lamarin zamantakewa ko tattalin arziki na musamman, da manufa, ko tasiri, na sauya halin mutumin ko mutum da ke cikin wannan rukunin a yanayi da ke haifar da ko zai iya haifar da muhimmin cuta ga wannan mutumin ko wani mutum;
- 4. Don makin zamantakewa ko hasashen bayanai wanda zai haifar da nuna wariya, rashin adalci, son kai, rashin goyon baya, ko hanyoyin cutarwa na wasu mutane ko rukuni na mutane;
- 5. Na kimanta haɗarin aikata laifi na mutum bisa ga bayanai kawai na mutum nahalitta ko akan kimanta dabi'un halayen su da yanayin halayen mutum. Haramcin ba zai yi aiki ga sabis na AI da aka yi amfani da shi wajen tallafin kimantawar ɗan adam na jiɓintawar mutum cikin aikin laifi, wanda ya riga ya ta'allaka da manufa da gaskiya da za a iya tabbatarwa da aka haɗa kai tsaye ga aikin laifi;
- 6. Dangane da bayanan hanyoyin tantance mai waya ɗinsu, don rarraba mutane ko a rage hasashen launin fatar su, ra'ayin siyasa, membobin hulɗar kungiyar kwadago, ra'ayoyin addini ko falsafa, ko rayuwar jima'i ko yanayin jima'i, sai dai banda lakabi ko tace tattara bayanan hanyoyin tantance mai waya da aka samu ta doka, kamar hotuna, dangane da bayanan hanyoyin tantance mai waya ko rarraba bayanan tantance mai waya a yankin hukumar tsaro;
- 7. Don ƙirƙira ko faɗaɗa kundin bayanai na ganewar fuska ta cire bayanai ba tare da takammman dalili ba na hotunan fuska daga intanet ko bidiyon CCTV;
- 8. Don kowane fasahar ganewar fuska na ainihin lokaci akan kyamarorin waya da aka yi amfani da su ta kowane hukumar tsaro a duniya baki ɗaya don yunƙurin gane mutum a yanayin rashin sarrafawa, muhallin "cikin daji", wanda ya haɗa da (ba tare da iyaka ba) jami'an tsaro suna zagaye ta amfani da kyamarorin da aka sanya a jiki ko dashboard ta amfani da fasahar gane fuska don yunƙurin gane mutum da ke cikin kundin bayani ko masu zargi ko kafin su zama 'yan kurkuku; ko
- 9. Don yunƙurin fahimtar yanayin shauƙin mutane daga jikin su, hankali, ko halayyan halaye (misali, yanayin fuska, motsin fuska, ko tsarin furuci), har da hasashen yanayi kamar fushi, ƙyama, farin ciki, baƙin ciki, mamakin tsoro, ko wasu kalmomi da aka fiya amfani da su don kwatanta yanayin shauƙin mutum.
Sabis na Sadarwa
- s. Sabis na Sadarwa. Sabis da ke ba da damar sadarwa tsakanin mutane, har da amma ba a iyakance ga Skype ba, Ƙungiyoyi, Outlook, da GroupMe, ana mulkar su ta ƙarin sharuɗɗan amfani da ke a https://aka.ms/useterms tare da waɗannan Sharuɗɗan.
Tarkace
14. Sauran abubuwa. Wannan sashe, da kuma sassa na 1, 9 (ga kuɗi wanda ya shiga kafin ƙarewar waɗannan Sharuɗɗa), 10, 11, 12, 15, 17 da kuma waɗanda sharuɗɗansu aka sanya bayan waɗannan Sharuɗɗa sun ƙare, duk wata ƙarewa ko soke waɗannan Sharuɗɗa ba ta shafar su. Har iyakanci da dokar da take shafa take yarda da, ya yiwu mu sanya waɗannan Sharuɗɗa, yi wa wajibcinmu ƙaramar kwangila a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa, ko yi wa hakkinmu ƙaramin lasisi na waɗannan Sharuɗɗa, gaba ɗaya ko wani ɓangare, a kowane lokaci ba tare da sanar maka ba. Ƙila ba za mu saka waɗannan Sharuɗɗa ko tura su zuwa wasu hakkoki don amfani da Sabis-sabis ɗin ba. Wannan ce ɗaukacin yarjejeniya tsakaninka da Microosft don amfani da Sabis-sabis ɗin. Wannan ya soke duk wata yarjejeniya ta baya tsakaninka da Microsoft da suka shafi amfani da Sabis-sabis ɗin da kake yi. Wajen shiga waɗannan Sharuɗɗa, ba ka dogara kan duk wani jawali, wakilci, garanti, fahimta, aiwatarwa, alƙawari ko tabbbaci fiye da waɗanda aka bayyana a cikin waɗannan Sharuɗɗa ba. An sanya duk sassa na waɗannan Sharuɗɗa zuwa iyakar da dokar da ta shafa ta ƙyale. Idan kotu ko wani alƙali ya ce ba za mu tilasta wani sashe na waɗannan Sharuɗɗa kamar yadda aka rubuta ba, ƙila mu iya musanya waɗannan sharuɗɗa tare da wasu sharuɗɗa masu kama zuwa iyakar tilastawa a ƙarƙashin dakar da ta shafa, amma ba za a sauya ragowar waɗannan Sharuɗɗa ba. Waɗannan Sharuɗɗa ne dominka da kuma alfanunmu. Waɗannan Sharuɗɗa ba alfanun sauran mutane ba ne, sai ga magada da kuma waɗannan Microosft ta sa. Kanun sashe don ddubawa ne kawai amma ba su da sakamako na shari’a.
15. Dole ne a Miƙa Ƙorafe-Ƙorafe Cikin Shekara Ɗaya. Duk wani ƙorafi da ya shafi waɗannan Sharuɗɗa dole ne a miƙa shi a cikin kotu (ko alƙali idan an sanya sashe na 10.d) cikin shekara guda daga ranar da za a fara miƙa ƙorafin, sai dai idan dokar ƙasarka ta buƙaci lokaci mai tsawo don miƙa ƙorafe-ƙorafe. Idan ba a miƙa cikin wannan lokaci ba, za a hana shi dindindin.
16. Dokokin Fitarwa. Dole ne ka bi duk dokokin gida da na waje na fitar kayayyaki ƙasashen waje da suka shafi manhajar da kuma/ko Sabis-sabis, wanda ya haɗa amma ba da iyakancewa ba da ƙasashe, masu amfani, da kuma nau’in amfani. Domin ƙarin bayani kan taƙaitawa na wurare da kuma fitar da kaya, ziyarci https://www.microsoft.com/exporting.
17. Keɓe Hakkoki da kuma Martani. Sai dai inda aka bayyana a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa, amma Microsoft ba ta baka wani lasisi ko duk wasu sauran hakkoki ko wasu iri a ƙarƙashin kowace lambar ƙira, yadda-ake, hakkin mallaka, sirrin kasuwanci, alamomin kasuwanci ko sauran hakkoki na ilimi mallakin Microsoft ko wanda take sarrafawa ko duk wani abu mai alaƙa, da ya haɗa amma ban da iyakancewa ga duk wani suna, alamar kasuwanci, tambari ko madadinsu. Idan ka ba wa Microsoft wata dabara, ƙuduri, shawara, ko wani martani, da ya haɗa, amma ban da iyakancewa ga dabaru na sababbin samfurori, kimiyya, talla, sunayen samfuri, martanin samfuri da kuma haɓaka samfuri ("Martani"), ka ba wa Microsoft, ba tare da wani biyan kuɗi ba, kuɗin shiga ko tilastawa gare ka ba, hakki na yi, samarwa, ayyukan kwaikwayon ƙirƙira, amfani, rabawa da kuma kasuwancin Martaninka ta kowace hanya da kuma kowane dalili. Ba za ka bayar da Martani da ya shafi wani lasisi da yake buƙatar Microsoft ta bayar da lasisin manhajarsa, fasaha ko daftarori ga wasu saboda Microsoft ta haɗa Martaninka a cikinsu.
SANARWA
Sanarwa da hanyoyin yin diyya kan keta haƙƙin mallakar ƙirar mutum. Microsoft tana mutunta haƙƙokin mallakar ƙirar mutum na wasu. Idan kana son aika wata sanarwar ketar haƙƙoƙin mallakar ƙirar mutum, da suke haɗa da diyyar ketar haƙƙin mallaka, daure ka yi amfani da hanyoyinmu na miƙawa Sanarwar keta (https://www.microsoft.com/en-us/legal/intellectualproperty/infringement) waɗanne hanyoyi suke kunshi waɗannan Sharuɗɗa. KAWAI BINCIKE DA SUKE DA MUHIMMANCI GA WANNAN HANYA NE ZA SU SAMU WATA AMSA.
Microsoft yana yin amfani da hanyoyi da aka bayyana a cikin Take na 17, Tsarin Doka na Amurka, Sashe na 512, da kuma inda ake sanya, Babi na III na Ƙa'idoji (EU) 2022/2065 don bayar da amsa ga sanarwar keta haƙƙoƙin mallaka ƙirar mutum. A lokuta da suka dace, haka kuma mai yiwuwa Microsoft ta hana ko ƙare asusu na masu amfani da ayyukan Microsoft waɗanda ƙila suka sake maimaita keta doka. Bugu da ƙari, a halayen da suke dace, wataƙila Microsoft ya dakatar da sarrafawa sanarwa ta wajen ɗaiɗaikun mutane ko ƙungiyoyin da suke sau da yawa miƙa sanarwa mara hujja. Wani ƙarin bayani ga hanyoyin da suke sanya don wani Sabis da aka bayar, da suke haɗa da sake dubawa mai yiwuwa na shawarwarin da Microsoft suke ɗauka a matsayin ɓangare na waɗannan hanyoyi, ana iya samun su a Sanarwar keta (https://www.microsoft.com/legal/intellectualproperty/infringement).
Sanarwa da kuma hanyoyi dangane da damuwa kan haƙƙin mallaka ƙirar mutum a cikin talla. Daure a yi bitar namu Jagororin Haƙƙin Mallaka Ƙirar Mutum (https://go.microsoft.com/fwlink/?LinkId=243207) dangane da damuwa da haƙƙin mallaka ƙirar mutum a kan tsarinmu na sadarwa na talla.
Sanarwar haƙƙin mallaka da alamar kasuwanci. An mallaka haƙƙoƙin Sabis-sabis ɗin © Microsoft Corporation da kuma/ko masu samarwa nasa, One Microsoft Way, Redmond, WA 98052, U.S.A. An mallaka duk haƙƙoƙi. Sharuɗɗan sun haɗa da Jagororin Microsoft na Alamar Kasuwanci da Alamar Samfuri (https://www.microsoft.com/en-us/legal/intellectualproperty/trademarks) (yadda ake gyara lokaci-lokaci). Microsoft da kuma sunaye, tambarori, da duk alamomin samfurorin Microsoft, sofwaya, da kuma sabis-sabis ta yiwu alamomin kasuwanci wanda ba a yi wa rajista ba ko alamomin kasuwanci na taron kamfanoni na Microsoft da aka yi wa rajista a Ƙasar Amurka da kuma/ko sauran ƙasashe ne. Wannan da ya tafe wani jeri na alamomin kasuwanci na Microsoft wanda ba dukkansu ne nan ba https://cdn-dynmedia-1.microsoft.com/is/content/microsoftcorp/microsoft/mscle/documents/presentations/TrademarksListFY25Q3.pdf. Ainihin sunayen kamfanonin da kuma samfurori za su iya kasance alamomin kasuwanci na waɗanda suka mallaka su ne. Duk haƙƙoki da ba a bayar da su dalla-dalla a cikin waɗannan Sharuɗɗa ba an mallaka su. Wasu sofwaya da aka yi amfani da su a cikin wasu sabobin shafin yanar-gizo na Microsoft suna dogara ne a wani ɓangare aiki na Rukuni JPEG mai zama da kansu. Haƙƙin mallaka © 1991-1996 Thomas G. Lane. An mallaka duk haƙƙoƙi. Sofwayar "gnuplot" da aka yi amfani da ita a wasu sabobin yanar gizo na Microsoft suna da haƙƙin mallaki © 1986‑1993 Thomas Williams, Colin Kelley ne. An mallaka duk haƙƙoƙi.
Sanarwa kan lafiya. Microsoft ba ya bayar da shawara kan lafiya ko wasu shawarwarin kula da lafiya, binciken lafiya ko samun magani. Nemi shawarar likita ko wani ƙwararren mai kula da lafiya da duk wasu tambayoyi dangane da lafiya, abinci, kuzari ko shiri mai ƙara lafiya. Kada a taɓa yin sakaci ko jinkiri da ƙwararriyar shawara kan lafiya wajen nemanta saboda bayanin da ka sami iso gare shi ko ta hanyar Ayyukan.
Ambaton hannayen jari da kuma bayanan fihirisa (da ya haɗa da darajojin fihirisa). Bayanin Sha'anin Kuɗi da aka samar da shi ta Ayyukan don amfaninka na keɓe, mara kasuwanci ne kawai. Ƙila ba za ka iya amfani da wasu daga cikin bayanan sha'anin kuɗi ko makunan mai bayar da lasisi na wasu ba da suka shafi samarwa, ƙirƙiri, ɗaukar nauyi, kasuwanci, tallar ko garaɓasa na wasu na'urorin sha’anin kuɗi ko samfurorin zuba jari (misali, fihirisoci, sakamako, tsararrun samfurori, kuɗin zuba jari, kuɗin musayar kuɗi, wuraren zuba jari, da sauransu, inda farashi, riba da kuma /ko ƙarfin aikin na'urar ko samfurorin zuba jarin sun dogara kan, dangane da, ko an yi niyyar bin sawun kowane bayanan sha'anin kuɗi) ba tare da wata keɓaɓɓiyar rubutacciyar yarjejeniya tare da mai bayar da lasisi na wasu ɗin ba.
Sanarwar sha’anin kuɗi. Microsoft ba dillali ba ne/dila ko wani mai bayar da shawara kan hannun jari da aka yi wa rajista a ƙarƙashin dokokin kadarori na tarayyar ta Amurka ko sauran dokoki kan kadarori na wasu ɓangarori ba kuma ba ta ba wa ɗaiɗaikun mutane shawara kan zuba hannun jari, saye, ko sayar da kadarori ko sauran samfuroin sha’anin kuɗi ko ayyuka. Ba wani abu a cikin Sabis-sabis ɗin da ya kasance wani tayi ko jan hankali kan sayen ko sayar da wata kadara. Microsoft ko masu samar da ambaton hannun jari ko bayanan fihirisa ba su yaba ko shawarta wani keɓaɓɓun samfurori ko sabis-sabis na sha'anin kuɗi. Ba wani abu a cikin Sabis-sabis ɗin da aka yi niyyar ya zama ƙwararriyar shawara, da ya haɗa ba tare da iyakancewa ba, zuba jari ko shawara kan haraji.
Sanarwa game da Ƙa'idojin Bidiyo na H.264/AVC da kuma VC-1. Ƙila sofwayar ta haɗa da fasahar kodek ta H.264/AVC da kuma/ko VC-1 da bayar da lasisin ta wajen MPEG LA, L.L.C. Wannan fasara wani tsari ne don danƙara bayanai da bayanin bidiyo. MPEG LA, L.L.C. yana buƙatar wannan sanarwa:
AN SAMAR DA WANNAN SAMFURI NE A ƘARƘASHIN LASISI H.264/AVC, DA KUMA VC-1 SHAIDAR LASISIN KAYA DON KEƁAƁƁEN AMFANI DA KUMA AMFANI DA BA NA KASUWANCI BA ZUWA (A) ENCODE VIDEO BISA DACEWA DA INGANCI ("VIDEO STANDARDS") DA KUMA/KO (B) DECODE H.264/AVC, MPEG-4 VISUAL, DA KUMA VC-1 VIDEO WANDA AKA JUYA GA MAI KEƁAƁƁEN AMFANI KO AMFANI WANDA BA NA KASUWANCI BA DA KUMA/KO AKA SAMU DAGA LASISIN MAI SAMAR DA BIDIYO DON SAMAR DA WANNAN BIDIYO. BA LASISI DA AKA BAYAR KO ZA A SANYA DON WANI AMFANI DABAN. ƘILA ZA A IYA SAMUN ƘARIN BAYANI DAGA MPEG LA, L.L.C. DUBA SHAFIN YANAR-GIZO NA MPEG LA (https://www.mpegla.com).
Domin dalilan bayani kawai, wannan sanarwa bai iyakance ko hana amfani da sofwayar ba da aka samar da su a ƙarƙashin waɗannan Sharuɗɗa don amfanin kasuwanci na yau da kullum da suke kasance keɓaɓɓe ga wancan kasuwar wanda bai haɗa da (i) sake rabawa sofwayar ga wasu, ko (ii) ƙirar da kayan da suke da ƘA'IDOJIN BIDIYO da suke dace da fasahohi na rabawa ga wasu.
Sanarwa game da Ƙa'idar Bidiyo H.265/HEVC. Sofwayar tana iya haɗa da fasahar ɓoye bayanai na H.265/HEVC. Access Advance LLC yana buƙatar wannan sanarwa:
IDAN AKA HAƊA, ANA KULA DA FASAHAR H.265/HEVC A CIKIN WANNAN SOFWAYA TA WAJEN DIYYA ƊAYA KO FIYE DA HAKA NA HAƘƘIN ƘIRA na HEVC DA AKA JERA A: PATENTLIST.ACCESSADVANCE.COM. DANGANE DA YADDA KA SAMU SOFWAYAN, ZA A IYA BAYAR DA LASISI NA WANNAN SAMFURIN A ƘARƘASHIN TSARIN INGANTACCEN HAƘƘIN ƘIRA.
Idan aka girka wannan sofwaya a kan wata na'urar Microsoft, za a iya samu ƙarin bayanin lasisi a: aka.ms/HEVCVirtualPatentMarking.
DAIDAITATTUN SHARUƊƊAN LASISIN MANHAJA
DAIDAITATTUN SHARUƊƊAN LASISIN MANHAJA
MICROSOFT STORE. MICROSOFT STORE A KAN WINDOWS, DA KUMA MICROSOFT STORE A KAN XBOX
Waɗannan sharuɗɗan lasisi wata yarjejeniya ce tsakaninka da kuma mawallafin manhajar. Da fatan za a karanta su. Sun shafi manhajojin sofwaya da ka sauke daga Wurin Adana na Microsoft, Wurin Adana na Microsoft a kan Windows ko Wurin Adana na Microsoft a kan Xbos (wanda kowanne ake nuni da shi a cikin waɗannan sharuɗɗan lasisi a zaman "Wurin Adana"), da ya haɗa da duk wani sabuntawa ko ƙari ga wannan manhaja, sai dai idan manhajar ta zo da keɓaɓɓun sharuɗɗa, inda a wannan hali ake sanya waɗannan sharuɗɗa.
TA SAUKE KO AMFANI DA MANHAJAR, KO ƘOƘARIN YIN ƊAYA DAGA WAƊANNAN, KA AMINCE DA WAƊANNAN SHARUƊƊAN. IDAN BA KA AMINCE DA SU BA, BA KA DA WANI HAKKI KUMA DOLE NE BA ZA KA SAUKE KO AMFANI DA MANHAJAR BA.
Mawallafin manhajar yana nufin wanda yake baka manhajar lasisin, kamar yadda aka gano a Wurin Adana.
Idan ka bi waɗannan sharuɗɗan lasisi, kana hakkokin da suke ƙasa.
- 1. HAKKOKIN SA WA DA KUMA AMFANI; LALACEWA Za ka iya saka da kuma amfani da manhajar a kan na’urorin Windows ko konsololin Xbox kamar yadda aka bayyana a cikin Dokokin Amfani (https://go.microsoft.com/fwlink/p/?LinkId=723143) na Microsoft. Microsoft yana ƙayyade haƙƙin gyara Dokokin Amfani (https://go.microsoft.com/fwlink/p/?LinkId=723143) na Microsoft a kowane lokaci.
- 2. AYYUKA DA SUKA SHAFI INTANET.
- a. Amincewa da ayyuka da suka shafi Intanet ko haɗi ta hanyar iska. Idan manhajar tana haɗi da sistem na kwamfuta ta hanyar Intanet, wanda ƙila zai iya haɗawa ta hanyar sadarwar iska, ta amfani da manhajar yana aiki kamar yadda ka amince don watsa daidaitaccen bayanin na’ura (da ya haɗa amma ban da iyakancewa da bayani game da na’urarka, sistem da kuma softwayar manhajar, da kuma sauran kayan haɗi) ga sabis da suka shafi Intanet ko haɗin ta hanyar iska. Idan an gabatar da sauran sharuɗɗa da suka shafi amfani da sabis-sabis da ka sami iso gare su ta hanyar amfani da manhajar, haka nan an sanya waɗannan sharuɗɗa.
- b. Rashin Amfani da Ayyuka Masu Aiki-da-Intanet Yadda ya Dace. Ƙila ba za ka yi amfani da sabis da ya shafi Intanet ba ta kowace hanya da za ta cutar da shi ko katse amfanin wani ko cibiyar sadarwar marar wayar. Ƙila ba za ka iya amfani da sabis ɗin ba wajen ƙoƙarin samun iso ga wani sabis, bayanai, asusu, ko hanyar sadarwa ta kowace hanya ba.
- 3. FAƊIN LASISI. Aikace-aikacen yana da lasisi, ba a sayar ba. Wannan yarjejeniya kawai tana ba ka wasu hakkoki ne na amfani da aikace-aikacen. Idan Microsoft ta hana dama ta amfani da aikace-aikacen a kan na´urarka bisa yarjejeniya tare da Microsoft, duk wani lasisi da ya shafa zai ƙare. Mawallafin manhajar ke riƙe da duk iko. Sai dai idan dokar da ta shafa ta ba ka ƙarin hakkoki duk da wannan iyakancewa, ƙila ka iya amfani da manhaja kawai kamar yadda aka ƙyale a bayyane a cikin wannan yarjejeniya. A wajen aikata haka, dole ne ka bi duk wasu iyakoki na na´ura a cikin manhaja da kawai yake ƙyale ka ka yi amfani da shi cikin wasu hanyoyi. Ƙila ba za ka iya:
- a. Aiki a kusa da duk inda aka yi wa taƙaitawar sana’a a cikin manhajar.
- b. Juya kimiyya, sake haɗa manhajar, banda kawai yadda doka ta tanada a rubuce, duk da wannan iyakancewa.
- c. Samar da kwafin manhajar sama da yadda aka ƙayyade a cikin wannan yarjejeniya ko da dokar da ta shafa ta ƙyale, duk da wannan iyakancewa.
- d. Wallafa ko kuma samar da kwafin manhajar ga wasu mutane don yin kwafi.
- e. Haya, ba da haya, ko aron manhajar.
- f. Tura manhaja ko wannan yarjejeniya zuwa ga wasu.
- 4. ADANA DAFTARI. Idan an samar da manhajar tare da daftari, ƙila za ka iya kwafi da kuma amfani da daftarin don dalilai na amfaninka.
- 5. TAƘAITAWAR KIMIYYA DA KUMA FITARWA. Manhajar ƙila ta zama a ƙarƙashin Amurka ko kulawar kmiyyar ƙasar waje ta Amurka ko dokokin fitarwa. Dole ne ka bi duk dokoki da ƙa’idoji na gida da na waje da suka shafi kimiyya da aka yi amfani da ita ko manhajar take goyon baya. Waɗannan dokoki sun haɗa da taƙaitawa a kan wuraren kaiwa, masu amfani da kuma ƙarshen amfani. Domin ƙarin bayani kan samfurorin Microsoft masu alama, je ka shafin yanar-gizo a fitar waje na Microsoft (https://go.microsoft.com/fwlink/?linkid=868967).
- 6. AYYUKAN GOYON BAYA. Tuntuɓi mawallafin manhajar don ƙayyade ayyukan goyon baya da suke akwai. Microsoft, maƙerin hadwaya ɗinka da kuma mai samar maka da sadarwa ta hanyar isa (sai dai idan ɗayansu shi ne mawallafin manhajar) ba su da hakki na samar da goyon baya kan sabis-sabis na manhajar.
- 7. ƊAUKACIN YARJEJENIYA. Wannan yarjejeniya, kowace dokar tsare sirri da take shafa, kowaɗane ƙarin sharuɗɗa da suka bi manahajar, da kuma sharuɗɗan don ƙari da sabuntawan cikakkiyar yarjejeniyar lasisi ce tsakanin kai da mawallafin manahajar don manahajar.
- 8. DOKA DA AKA SA.
- a. Amurka da Canada Idan ka sami manhajar ne a Amurka ko Canada, dokokin jihar ko gundumar da kake zaune (ko, idan wani kasuwanci ne, inda cibiyar kasuwancinka take) ke kula da fashin-baƙi na wannan yarjejeniya da kuma ya shafin duk wani ƙorafe-ƙorafe na keta ta, da kuma duk sauran ƙorafe-ƙorafe (da suka haɗa da kariyar mai amfani, gasa bisa rashin adalci da kuma koke-koke kan lahani) koda kuwa wace irin babbar doka ce ta saɓanin.
- b. Wajen Amurka da kuma Canada. Idan ka sami manhajar ne a wata ƙasa, dokokin wannan ƙasa za a sanya.
- 9. SAKAMAKON SHARI’A. Wannan yarjejeniya ta bayyana wasu hakkoki ne na doka. Ƙila kana da sauran hakkoki a ƙarƙashin dokokin jiharka ko ƙasarka. Wannan yarjejeniya ba ta sauya hakkokinka a ƙarƙashin dokokin jiharka ko ƙasarka idan dokokin jiharka ko ƙasarka ba su ba da damar aikata haka ba.
- 10. KASHEDIN GARANTI. Gana wa dokar da aka sanya, an samar da lasisin manhaja “kamar yadda yake”, “tare da duk lahanoni” kamar “yadda yake samuwa”. Duk haɗari na amfani da shi ya rataya a wuyanka. Mawallafin mahajar, a madadin kansa, Microsoft (idan Microsoft ba shi ne mawallafin manhajar ba), masu samar da sadarwa ta hanyar iska waɗanda aka samar da manhajar ta hanyar sadarwarsu, da kuma kowane rassanmu, masu sayarwa, jami’a da kuma sararwa (“Waɗanda abin ya Shafa”), ba su bayar da wata yarjejeniya, garanti ko sharuɗɗa da suka shafi manhajar ba. Ɗaukacin haɗari ga ingancin, tsaro, jin daɗi, da ƙarfin aiki na manahajar yana a hannunka. Idan an tabbatar da buƙatar ba daidai ba ce, kai ke da alhakin biyan duk kuɗin da ya shafi sabis ko gyara. Ƙila kana da wasu ƙarin hakkoki na mai amfani da kaya a ƙarƙashin dokokin ƙasarka da wannnan yarjejeniya ba za ta iya canzawa ba. Har iyakanci da dokoki na gida ɗinka suke yarda da, Kulallen Wasu sun ware kowane warantoci ko halaya da suke shafa, da suka haɗa waɗannan na kasuwanci, dacewa don wani takamaiman maƙasudi, taro, jin daɗi da kuma rashin keta doka.
- 11. IYAKA A KAN DA KUMA WARIYA NA MAGANCEWA DA KUMA LALACEWA. Zuwa ga iyakar da doka ba ta haramta ba, idan kana da wata hujja ta rashin ɗaukar asara, za ka iya dawo da kuɗi daga mawallafin manhajar kawai kai tsaye har zuwa adadn kuɗin da ka biya na manhajar ko $1.00, duk wanda ya fi yawa. Gana wa dokar da aka sanya, ba za ka iya, kuma ba za ka fasa kowane haƙƙi na, neman dawo da kowaɗane sauran ɓarnoni, da suka haɗa, riba da aka rasa, ɓarnoni na musamman, mara kai tsaye ko wanda ya auku daga mawallafin manhajar. Idan dokoki na gida sun kafa wani tabbaci, garanti ko ƙa'idoji ko ma waɗannan sharuɗɗa ba su gana wa dokar da aka sanya ba, an iyakance tsawon lokacinsa zuwa kwanaki-90 daga lokacin da ka zazzage manhajar.
Wannan iyakancewa ta shafi:
- Duk wani abu da ya shafi manhajar ko ayyukan da aka samar ta hanyar manhajar; da kuma
- Koke-koke na keta dokar kwangila, keta dokar garanti, tabbaci ko sharaɗi; bashi mai tsanani, sakaci, ko wani laifi; keta doka ko ƙa’ida; azurtawa bisa rashin adalci; ko a ƙarƙashin duk wani irin dalili, duk zuwa iyakar da dokar da aka sanya ta ƙyale.
Haka nan ya shafi idan:
- Abin da ake bayarwa ba ya biyan diyyar gaba ɗaya asarark; ko
- Mawallafin manhajar ya sani ko yakamata ya san yiwuwar lalacewar.
Sabis-Sabis da ya Haɗe
Samfurorin da suke tafe, manhajiji da kuma sabis-sabis suna ƙarƙashin kulawar Yarjejeniyar Sabis na Microsoft, amma ƙila bza su samu a cikin kasuwarka ba.
- Abinci da Abin Sha na Bing
- Account.microsoft.com
- Asusun Microsoft
- Binciken Microsoft cikin Bing
- Bing Image and News (iOS)
- Bing Search APIs/SDKs
- Bing Translator
- Bing Webmaster
- Bing.com
- Bingplaces.com
- Bugawa ta MSN
- Clipchamp
- Cortana skills by Microsoft
- Cortana
- Default Homepage and New Tab Page on Microsoft Edge
- Dev Center App
- Dictate
- education.minecraft.net
- Face Swap
- Feedback Intake Tool for Azure Maps (aka “Azure Maps Feedback”)
- Finafinai da TV na Microsoft
- Forms.microsoft.com
- forzamotorsport.net
- Galarin Hoto na Windows
- Groove Music Pass
- Groove
- GroupMe
- Hasashen Yanayi na Bing
- Haɗin Microsoft 365 na zaɓi
- Hoton Bango na Microsoft
- Image Creator from Microsoft Designer
- Iyali na Microsoft
- Kulle Allo na Gaba
- Kuɗi na Bing
- Labarai na Bing
- Lafiya da Kuzari na Bing
- Lafiya ta Microsoft
- LineBack
- Link to Windows
- Mai warware Ilimin Lissafi ta Microsoft
- Maitaimakon Goyon baya da Samuwa Microsoft ga Office 365
- Manajan Skype
- Manhajar Lafiyar Na’ura
- Manhajar Nema ta Bing
- Manhajar Taswirori
- Manhajar Tsara SMS
- Manhajoji da sabis-sabis da suka shafi Gama-Garin Microsoft 365
- Manhajoji da sabis-sabis da suka shafi Iyali na Microsoft 365
- Manhajoji da sabis-sabis da suka shafi Microsoft 365 na Mutum
- Manhajoji da sabis-sabis da suka shafi rajistar konzuma na Microsoft 365
- Manhajoji na Bing
- Ma’adanar Office
- Microsoft 365 Business Standard, Microsoft 365 Business Basic, Microsoft 365 Apps, Microsoft 365 app, Microsoft 365 Copilot, Microsoft 365 Copilot app, and Microsoft 365 Copilot Chat*
- *Until a commercial domain is established for use of these services, at which time separate Microsoft commercial terms will govern instead.
- Microsoft 365 Consumer
- Microsoft 365 Family
- Microsoft 365 na intanet
- Microsoft 365 Personal
- Microsoft Academic
- Microsoft Add-Ins for Skype
- Microsoft Bots
- Microsoft Copilot
- Microsoft Defender domin mutum ɗaya
- Microsoft Educator Community
- Microsoft Launcher
- Microsoft Loop
- Microsoft Pay
- Microsoft Pix
- Microsoft Reading Coach
- Microsoft Research Interactive Science
- Microsoft Research Open Data
- Microsoft Rewards
- Microsoft Soundscape
- Microsoft Sway
- Microsoft Teams
- Microsoft Translator
- Minecraft Realms Plus and Minecraft Realms
- Mixer
- MSN (wanda aka sani da Microsoft Start a baya)
- MSN Explorer
- MSN Lambawan
- MSN.com
- Nema mai Dabara
- OneDrive.com
- OneDrive
- OneNote.com
- Outlook.com
- Paint 3D
- Phone Link
- Presentation Translator
- Rangwamen Bing
- rise4fun
- Seeing AI
- Send
- Shafin Bing
- Skype in the Classroom
- Skype.com
- Skype
- Snip Insights
- Spreadsheet Keyboard
- Sway.com
- Tafiya ta Bing
- Tallafin Microsoft (Mabuƙaci)
- Tari
- Tarin Microsoft
- Taswirori na Bing
- to-do.microsoft.com
- Translator for Microsoft Edge
- Translator Live
- Tsarin Microsoft 365 na kyauta
- Universal Human Relevance System (UHRS)
- UrWeather
- ux.microsoft.com
- Video Breakdown
- Visio Online
- Wasanni na Bing
- Wasannin Minecraft
- Wasannin, manhajojin da kuma shafukan yanar gizon Windows da Microsoft ta wallafa
- Wasannin, manhajojin da kuma shafukan yanar gizon Xbox Game Studios
- Web Translator
- whiteboard.office.com
- Windows Live Mail
- Windows Live Writer
- Windows Movie Maker
- Wurin Adana Windows
- Wurin adana
- Xbox Game Pass
- Xbox Live Gold
- Xbox Live
- Xbox Music
- Xbox Store
- Ƙamusu na Bing